Sashe 245
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya kasance jumma,ace ranan hakan yasa nayi kwaliya na dan gyara fuskana duk da ba inda zan fita don tun zuwana ban fita ko ina ba. Duba ga zancen daddy a gareni hakan yass na kara kama kaina ko marmarin fita daga gidan banyi dama ba gwanar fita irin haka baceni. Wasu material da ummah ta saya min duk da nace da ita kayana suna nan banyi amfani dasu bama a lokacin saidai hakan bai hanata ta saya min ba. Suna dauko na saka ance yaba kyauta tukwici kayan sun karbi jikina sosai zaune nake muna shan ferfesu kwatsan muryan salima ya daki kunnena. Wani irin faduwan gaba ya ziyarci zuciyana lokaci guda a daidai lokacin data tsaya kofan dakin tana kara kwada muna sallama akaro na barkatai ana kuma amsawa tare da fadin tashigo mana. Anty salima don har lokacin ina saya sunansu a yadda na saba kiransu dashi da farko tashigo ta sauke idonta a kaina inda nake zaune kasa saman carpet tare da bin plate din dake gabana da kallo wanda yake shake da koda zallah da saudatu ta gyara muna. A,a kune a tafe salima tace eeh tare muke gaba daya ai harsu yaya da mama jin hakan yasa naso tashi a inda nake zaunen . Saidai na makara da hakan don sun riga da sun fara shigowa falon ko da sallamansu anayi masu sannu da zuwa tare da dan kauce kaucen abubuwan dake gaban mu duk daba muni a cikinsa. Saare da tayi zuwan dole tana ta faman mede muna fuska tana wani dube dube a falon suka zauna kafin ta mayar da hankalinta a kaina. Kallo daya nayi mata na fahinci ranta a bace yake wai ashe tun shigowansu kaduna ta soma fadin amma mama yakamata mu leko su mami muga lafiyansu. Shine ya yazid ya bata amsa da fadin ke saratu nan makirace watau kin kulla gulma duk wanda kikayi a waya bai isheki ba sai kinyi na face to face a gabanta toba zamuje ba din din ba shi ya kawomu ba . Saratu ai zaki iya sauka ki karasa idan kin gama saiki samemu mami kuma idan suna son mu ganta ai sunsan hanyar gidan mu ko ? Yatace mami amma bakin jinin dake zuciyana na uwarta ya sa a yanzu har ina mantawa da ita a yanzu daga inda mama take zaune ta sake wani sallati tana fadin subbahanallahi kanka daya kuwa Jafar kake fadan haka ga yarka. Yarkace fa koma me uwarta tayi ma karka manta yarkace ai dinshi nace ina mantawa dasu a yanzu ya sake fadan hakan. Ita kuma mama sai cewa tayi lalai kanka ba daya bane Jafar na yarda akwai abindake damun kwakwalwanka a yanzu to sai ita,,,, Haba dai dubu don yaron nan ya fadi haka ai kinsan bacin rai yakaishi ga fadin hakan ku bar wanan zancen tunda ransa har yanzu a bace yake game da yarinyar nan Nusaiba. Ai don jan magana munafukar nan ta dauko zamcen Nusaiba din don irin haka tunda tasan abinda ya kawomu garin nan . Tasan ba wurin Nusaiba muka zo ba munzo bikon yar mutunci da sanin ya kamatane wacce tasan metakeyi ba wace son abin duniya ya dama ba Yazid ke fadan hakan. Wanan abinda yazid din ya fada shine yasa ta shigo gidan tana fushi duk gaisawan da saudi ke masu fuskanta a daure yake ita. Kafin komai har saudi din ta cika masu gaba da abincin karyawan mu da akayi hakan ba karamin daukaka saudi din ta ja min ba duk da sunsan ba gidan ubbana bane nan din amma ko hakan yayi min dadi har cikin raina. Mazan suna waje basu shigo ba daddy ya fito suka gaisa dashi shi yayi masu jagora zuwa cikin gidan nasu inda suka samesu a falo suna karyawa nan yazid ya hau masu sheri da sunshigo sun buge da cin abinci. Saudatu ce ta shigo take fada min yaya Jafar dashi akazo yana nan yana baza ido yaga ta inda zan fito a gidan ai sai ya matsa na fada ina tsuki. Uwata ba aiwa miji tsuki haka don shiryawa zakiyi da abinki adaiyi hakkuri din bawan Allah nan yana kaunarki matuka ki duba yadda akazo dashi a daddafe haka daganinsa har yanzu yana jin jikinsa. Amma ya taso saboda ke zuwa nan don Allah ki sassauta mashi kinji kada kice ba zaki bishi a yanzu ki koma dakinki hakana kinji ? Daidai lokacin ummah ta shigo ta samu tana fadan haka sai cewa ummah tayi gara dai ki fada mata donni banga laifin wanan mutum ba. Kada fushin daba nasa ba fushin yan uwasa ya debe maki ladanki ga banza saboda kawai suga kun samu barka dashi suke fata. Saudi ta kara fadin shiyasa nake bata shawara ta koma idan an shirya idan anji abinda ya kawosu sai kiyi hakkuri don Allah ? Muryan Abba daya dawone yake fadin ina ummah yasa ta fito falon aka zauna naji falon yayi shiru iya ta soma magana tana fadin to Alh . Kamar yadda nayima alkawarin dawowa gashi Allah ya dawo damu cikin ikonsa tare da iyalina da kowa don muzo muyi bikon yar wajenka da fatan an huce zuwa yanzu ? Don Allah ayi hakkuri wanda yace zomu zauna kamar yace zomu sabane sai an hada da hakkuri zama ke dadi in sha Allah abinda ya faru da farko ba za a sake maimaitashi ba in sha Allahu. To hjy naji aimu ba fushi mukayi ba kun sani illa iyaka so muke a tsawata akan abubuwan cin fuska da izigilanci da akewa yaran nan yayi yawa. Ina son ku gane bayin yaran nan bane gaba dayansu kaddaransuce hakan aure a gida daya hakama yaran ku maza suma hakan tasu kaddarance tazo a hakan. A zatona yau duk wanda yaso naka haka yagama dakai a rayuwa ba sauran zargi ko wani hasashe ga wanan bawa ko don alherinshi gareka zaka daga mai kafa ka kawar da kai ga duk wani abu tunda yaso naka tsakani da Allah. Ayi hakkuri don Allah a zauna da juna a cikin mutunci sai aji dadin juna a gama da duniya lafiya ga zuwairatu nan a gidan nan ba haihuwa tayi damu ba amma ta kama kan diyan nan ta hade min kamar itace ta haifo abinta. Tsohuwa meyafi wanan farin ciki a wajena yau na samu macen data san darajata data yayana tasan zafinsu tankar itace ta haifesu yanzu haka saisu shigo gidan nan suyi shawara da ita ba tare dana sani ba wanan ai kwanciyan hankalina ko bana raye a duniyan nan haka yan uwana kaf dinsu kowa na zuwa gidan nan yanzu ta dalilin wanan macen da Allah ya ban. Don haka ni a ganina wanan abin farin cikine yau a gareku don duniya ta sheda yarinyar nan bata bar mijinta a wullakace ba daidai lokacin da yake bukatan soyayyan na tare dashi. Duk wanan bayanjn da Daddy yakeyi saratu sai wani harare harare takeyi tana yatsunan fuska tana basarwa tana nuna maganan zucin da takeyi a fili. Ba daddy din ba duk wanda ke falon ya kalketa yasan abinda take nufi da hakan mai karatu ba saratu bafa har mama dake zaune irin shigen wanan yanayin take itama a lokacin. Yazid ne ya karba da fadin Alh munsan kokarin Rahama a gidan mu duba ga yan kwanakin nan da bata gidan bashi da yake mijinta take jinya ba kowan mu a yanzu ya fahinci ranan ta a tare damu. Kwaraima don wallahi ba sai an fadi ba mutum ko yaya yake ai rana gareshi ba a sani kuma sai ranan daya bar wajen za a gane hakan. Balle yar nan data zama tauraruwar gidanmu a yanzu ta share ko ina tas ba kyashi ba hassada kafin gari ya waye tayiwa mijinta komai saidai a zo a sameshi a gyarensa duk wake hakan ita ? Yanzu fa Alh yaron nan sai yabaka tsusayi kamar ka zubar mashi da hawaye don wani abin yana so ba,,,,,,,,,,, Humm,ummm ya fito daga bakjn Saratu hakan yasa yazid fadin tayi karya ko ta juyo tana fadin me nace yanzu don Allah kuma ? Sai in karyaki a nan ta godewa Allah taga nata rayuwan auren ki saurara naki ke kuma saukin abin dai auren sai bawa yayi matukar yana raye . Zaku fara halin naku ko me kaji ta fada yanzu da kake kokarin mata baki har kana fadin ,,,,,, A,a dakata hjy don Allah dama yarki ce matsalan yarinyar nan kaf dinku kun sanda hakan a wajen nan to gashi a gaban mu ta nuna maganar banza akeyi a yanzu. Ina ganin abin nan kawai a hakkura hjy don yarinyar nan ta nuna muna bata da tarbiya da zataji sulhun da akeyi a wajen nan balle a koma a zauna lafiya. Wallahi bata isa ba Alh ita dinme harta isa ta hana min matana zama a gidana saboda ita abu dayane yanzu a gaban kowa tunda tace haka zan mata iyaka da matana dukka don ba ita kadai bace kanwata ai ? Ina da yan uwan dake kaunan zumuci dani sai yayi kamar ya sarke don maganan da yakeyi a cikin bacin rai hakan yasa da sauri dan uwansa mikewa zuwa gareshi tare da goran ruwa a hannunsa. Ya bashi suka hau lalashinsa akan yai shiru don Allah yazid sai fadin yake wallahi kikai sanadin yaya kowaya tsaya maki sai kasheki Saratu. Kin gani dai mama tazo ta nunawa mutane rashin tarbiyanta a nan yanzu haka kuma tana kallon yadda dan uwan mu ke wahala amma wai yarinyar nan tana neman bata muna tafiyan mu don tana yar iska kawai. Kananan maganganu ta soma yi daddy sai murmushinsa yakeyi irin nasu na manya yana kada kafanshi irin yasan za a rina ? Saida iya ta samu sukai shiru ta hau fada yake fadin dakata tsohuwa wanan abu ai mai saukine yanzu kai malam Jafar kaje kayi hakkuri don muna son yar mu gaskiya. Rahamatullah ba zata koma gidan ku ba da wanan halin da kuka nuna muna a gabanmu which means koda ta koma dai halin yana nan bai caza zani ba. Yar mu tana fama da laulayin ciki don likitoci sun bata hutu komai batayi a yanzu sunje asibiti da uwarta