← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 283 OF 306

Sashe 283

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zaba wai ita wayewa oho dai su suka sani ta fada cikin bacin rai. Allah akbar kishin ke nan fa mata kishiya idan ba ta daina ganin numfashin kishiya ba ko taji an fasa ihu shine kawai zata numfasa amma wani ciwo ko wani kakanakayi bai hana kishi ga wasu. Asibitin kuma habu ya fara kira yake cewa dashi muna asibiti da Rahama idan akwai kudi a wajenka don Allah turo min an rubuta min magani. Yana hamma don barci yakeyi yace kudi gaskiya ba wasu kudi a hannuna sosai yanzu amma bari in duba yace ba matsala. Shiru yayi bayan sun gama wayan ranshi a bace ya kira abokinsa na nan dake juya mai kudin Salima yace dubu dari biyu yake so don Allah ina asibiti da matana aiki za ayi mata yanzu. Subbahanallahi aiki kuma gani nan zuwa amma ai sha,anin asibiti dari biyu baiyi gaskiya bari dai in karaso yanzun nan zan watsa ruwa in sameka kuna wani asibitin ne a ciki ? Ya fada mai yace gashi tafe har yazo aka shiga aikin bayan ya kawo mai dari hudu duk wani zirga zirgan asibitin akayi dashi saida aka fito mai da jariri ya tambaya akace za a fito dani yanzu yayi godiya ga Allah. Mama da Salimace suka tafi gida da yaron don ai mashi wanka suka bar iya da inna data biyo mu daga baya ita da Nafisa. Duk abinda yakeyi hankalinsa yana ga dan uwansa yana mamaki furucin yaya habu din don mamaki shi kwarai yake a zuciyarshi. Yana aiyana lalai kudi sune rufin asirin bawa yau shine dan uwansa na jini yayiwa hakan gara yazid ya san baida kudin amma ya turo mashi da abinda ke akwai a lokacin. Haka yayi ta sintiri da yunwa a cikinsa sai karfe biyu ya koma gida don ya watsa ruwa ya samu abinda yaci lokacin abokin nasa shima zai tafi yace dashi zaka jini insha Allahu sulaiman nagode kwarai da taimakonka. Haba dai dole muyi maka ai J waye silan zaman mu hakan a yau i bamuyi ma ai Allah zai tambaye mu ni wallahi ba wancan kudin bane kyauta na baka wa yan nan din. Abinda bai tsamata ba hakan ya sama don koda ya shigo gidan da saiba ya fara cin karo tana shayi a wajen haraban gidan har ya aje mota ya fito ko kallo bai isheta ba. Saida ya shiga ciki ga wari ga komai ya fara kwalawa Asmau kira da ita yana fadin wanan warin fa tun safe nake jinshi a part din nan ? Asmau ta fito da danta a hannu tana fadin kadawo ashe yaya mai jikin kuma yace da sauki ashe an sauka Allah raya ya amsa da amin yana fadin. Wanan warin fa na meye do Allah yaya zaku zauna cikin warin nan kuna ji zai iya illanraku amma kun kasa duba kome ke wari haka don Allah ya fada yana bin falon da kallo. A,a warin ruwan waken da Saiba tayi alale dashi jiyane na fada mata yana wari ta dauke taki to munafuka kina fada mashine don ya dakeni kome ? Hauka nayi da har na fara duka waike Nusaiba wace irin macece da baki son zaman lafiyane komai naki nacin mutuncine ke ? Yanzu ina shigowa asibiti na fito amma kika bini da kallon wullakanci din kina yar rainin wayau ko ke gaki issasa ki shiga ki dauke ruwan nan yanzun nan kafin na fito. Ina ruwana da ka fito asibiti tunda ban aike ba asibiti wanan ruwanka kai ya shafa bani ba name zaka kuma dafa min wai nayima mugun kallo ? Ai nasan ruwana tunda bai shafeki ba niko daya shafa ai kinga naje har kuma kin gune da hakan ni yanzu na gane ki sarai kanki kawai kika sani ke saukin abin kowa dai na ciwo aiko ? Wata sabuwa za a dora min laifin da banji ba bangani ba akai kaje kaji da wace ta jaka zuwa asibiti ta kwanta don samun waje bani ba ? Ai kinji nace niya shafa kuma naje ba sai kinyi hakan zaki nuna min ranki a bace yake ba ai dani taje ta kwanta kuma naje na tsaya din anyi mata aiki ina shike nan koda kudinki nakai ta asibitin ? Meye nawa malam mu dai da aka raina idan munyi magana ace damu babu kudi gashi yanzu anyi kudin kai mata asibiti ai tunda tana yar gwal. Au bakin cikinki ke nan ashe na samu kudin dana kaita asibiti akai mata aiki to kije ki kwanta kema asibitin sai in kashe maki kudin ko ? Kai kai kai wai haniyar meye kukeyi hakane kai da kake da mara lafiya kazo nan kana wanan hayaniya haka kuma kuna saida hali ? Yarinyar nan mama yar rainin wayauce ya juya yana fadawa mama din yace har da asibiti mutum ya dawo ba zata barshi ya huta ba nina gaji wallahi tunda bata da ranan gyara halinta ? To ka gaji mana sai me keko kikan fara halinki ke nan wallahi tunda kinsan hankalinshi na a kwance yake ba baki kyaleshi koma meye ? Mama kodaya fita gidan nan bai fada muna matarshi tana asibiti ba ko zai kaita asibiti don ina tsoronsu yanzu sai ince mashi yaya jikinta ko an haihu ? Kallon mama din yayi cikin mamaki yaji abinda zata fada sai yaji tace towa ya fadawa ga abinda ke nan muma saida yaga za ayi aikin aiya kiramu tunda bamu da amfani a zancen ? Ina dai fadama kayi hankali da mace balle irin shu,umar yarinyar nan data iya kisisina iri iri tun bata kai nan ba. Mama kin goyi bayanta ke nan fa zancenki ke nufi ba zancen goyon baya a nan tsoranka akeji daba za a fada maka gaskiya ba tunda an nayar daku shanun tatsa ko yaushe kuke nan cikin wahalan mata ? Yarta ta kwanta tace bata iya daukan ciki balle haihuwa yanzu gashi itama ta tsiri hakan farawa da iyawa saika koma kaita kashe jiki ana tatsanka kaiga mata asibiti. Ballema ita bata haifo a sa,a ba tunda taszo da kissan ba kudin ta gaji da kwanci ta taso don kanta idan taga ba abinda sukewa din ta makara wajen wanan kissan. Kai ya girgiza ya juya zuwa dakinsa ya rufo ya barsu tsaye cirko cirko a wajen sai nusaibance ta kawar da shirun take fadin wallahi Asmau muna fukace ta karshe wai mutum bai fada muna komai ba take mashi wani kashe murya yanzu . Wanka yayi ya koma asibitin Nafisa ya kira yake fada mata taje can gidanmu ta shiryo abinci a kawowasu mama nan ya bata kudin mota ta tafi. Koda ya shiga dakin ya samu na farfado ina ina kwance mama tana gefe da jaririn a hannunta tare da sauran yan family house dinsu da sukazo ya shigo suna gaisawa dashi suke mashi barka da arzikin fitan kai lafiya. Ya amsa kafin ya aje masu ledan daya riko dan abinda zasuci a lokacin ya nufi wajen gadon yana min yaya jiki na lumshe ido cikin gajiya tare da amsawa da kyat nace da sauki. Ya juya gurin mama yana tambaya yace wai kuwa matar habu tazo mama mama din tace yanzu na kare zancenta a raina da ban ganta ba nima. Waya ya dauko yana bugawa habu din wayan ta kusa katsewa ya dauka yana dauka yake fadin sorry J wallahi kudin ne basu samu ba kajini shiru. Yace nerve mind nace ka fadawa Matarka cewa muna asibiti anyiwa kanwarta CS an cire da dazun ? Wai dama aiki za ayiwa Rahama din na zata kunje ganin likitane kawai fa ya katseshi da fadin don Allah fada mata anyi aikin an cire da tun dazun muna nan Royal da ita ya kashe wayan . Ya juyo gareni nake fadi a hankali dama ka kyaleta ai yace No a dai fada mata din kada ayi laifi donshi bai fada ba wai baisan aiki za ai maki ba. Shigowa likita yasa sauran fita aka bar mama dashi a dakin likitan na fita mama ta soma fadin matanka fa da dubu koda yake ga iya ai da salima sunzo ba zance basu sani ba. Sun sani mama ya fada a cikin wani irin yanayi na bacin rai kafin ya juya zancen da fadin yaron yanzu mai za a bashi ga dai ruwan zamzam nan na sayo da dabino a leda. Nagani salima zata bashi likita ya shigo barci ma yakeyi tun dazun dai yayi dan kuka kuma aka lalasheshi yayi barci. Likitan yace ya gaji da yawa hutu yake so ai an auna arzikine aka sameshi raye yarinyar nan tana da taurin kai mama tana nakuda tun cikin dare amma bata kirani ta sheda min ba ? Murmushi mama tayi tana fadin bafulatancefa Malam aiko inba ta zama bafulatanan zamani ba baka taba jin ta bude baki tacema ga matsalan ta wanan halinsune alkunya da kawaici shi mutane suke dauka rashin wayewa nan ko alkunyace irin tasu ta fulani da akasani. To mama kana cikin wanan cindition din baka kikirana kunya hardani zata hada mama haba mama tayi murmushi tana fadin daga ita har matan habu ai basu yarda akidojinsu na fulani ba. Mama ni yau ai ina a cikin mamaki sosai wallahi ashe idan baka dashi ba kowa kake a wajen ko yan uwanka ba mama ni habu zauwa haka. Ban gama mamaki ba kuma naje gida na samu wanda yafi wanan abin mamaki ace maman mu har da asibiti take adawa akai wai da gangan Rahama tazo ta kwanta akai mata aiki. Don kawai a kashe mata kudi da ganganfa mama ta katseshi da fadi yace wallahi mama ita kuma shashashan nan mai bakin kishi ta dora nata sai Asmau ce tayi min Allah sauwaka kuma sukaga laifinta. Ita dubu har abin yakai haka gareta to Allah ya sauwaka don abin nata sai addua iya fa ta fara ban labari dazun ashe ta fada maka hakan kaima Allah ya sauwaka toh. Mama ni habu zai hanawa kudi sai wani banza can na waje bare aboki dana taimakawa taimakon da baikai nasa danayi mashi ba shine zai dauko kudi ya ban masu yawa inyi lalurata dashi. Amma ko habu bai kyauta ba barshi insha Allahu ko
Chapter 283 · 0% Book details