Sashe 193
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
tuni din ? Ai kaji me nace yau shekara kusan biyu ke nan da rasuwanta ai amma yarta na ciki itace ta gajeta ga aikin yanzu aifa shike nan kuma kai habu namu ya samemu kuma a yanzu iya ta kara fada a rude mama kan hawayene suka soma zubo mata lokaci guda takai tsugunne a waje daya cikin tashin hankali. Dayan mutumin ke fadin ku karasa ciki koma meye yarta kudidi tana nan zata saurareku ai don ganin yadda fuskokinsu ya nuna damuwa da tashin hankali lokaci guda jin mutuwan tsohuwan da sukayi. Yaro aka tura yayi masu iso da matar da aka kira da kudidi din ta dan jima bata fito ba don tana ganawa da wasu bakin a lokacin . Yayin datayi masu ison su shigo kawune ya fara shiga dakin da take karban bakinta sai iya sai mama dubu habune yayi karshen shiga dakin da sallama a bakinsa. Neman inda zai zauna yayi ya kai tsugune don ita wace suka zo wurinta din tana neman wani abu a lokacin don haka ta basu baya ba zasuce ga fuskanta ba . Lokaci guda gabanshi ya fadi yayin da yai arba da wanan matar mai maciji a kwalla na shekarun baya ba zai taba mantawa da fuskan wanan matar ba. Ba annuri a fuskan nata gata saye cikin bakaken tufafi irin na mutanen dauri tun daga sama har kasa sune a jikinta. Yau Allah yayi kun samu zuwa ke nan abinda ya fito daga bakinta ke nan lokacin data juyo garesu shiru dan dakin yayi na lokaci guda. Ta mika hannu ta dauko wani dan kwarya ta girke a tsakiyarsu tana fadin tabaci ke nan tunda na ganku nan kai habu aina fadama dole saika nememu dama tun abu baikai haka ba har kun bari komai yakai ga lalacewa. Sunan habu data kirane ya basu mamaki gaba dayansu har habu din da har lokacin kallon mamaki yake binta dashi . Kawune yayi kokarin soma magana cikin wani murya ta dakatar dashi da fadin kai mana shiru don Allah kome ya faru laifinkane . Da yar uwarka kazo nan neman sa,a kayi dace an karbama anyi a cikin sa,a amma ka bata komai da hannunka saboda son kai irin na yan adam daka sawa kanka a rayuwanka. Kaki yar uwarka kabi ra,ayin matarka duk da gargadin da mahaifiyana tayi maka a wancan lokacin akan yar uwarka da kake son cin amananta. Amma ka yarda ka,biyewa matarka kuka cutawa yar uwarka duk irin biyayyan da take maka kaida matarka amma kukai amfani da biyayyanta kuka cuta mata ba tare da sanin taba. Naso na taimaka tun abin nan bai kai haka ba amma shu,umar matarka ta hana hakan a lokacin don bata bar yar uwarka a banza ba ita da zurianta. Kai kanka kasani kasan irin yadda take duke kan wa yan nan mutane duk akan abin duniya kuke hakan duk da kusan cewa karshen hakan ba zai maku dadi ba nan gaba. Yanzu ba wanan ba kun zone akan dan uwaka dake fama da jikinsa ko habu ? Saita kada kai tana bata fuska kafin tace shi an riga da an sameshi saidai ba yadda akaso samun nasa ba. Don ansone ayi mashi karaf daya wanan karon saidai hakan bai samu ba saboda wani dalili kai haba kasani na fadama wanan yarinyar da ka aura tana da wani siri a tare da ita. Hakama ita wace ke tare da dan uwar naka naga kamar yar uwar matarkace ita tana da natukar kokari sosai don Allah ya kyauta zamata tare dashi matuka da komai ya jagule akansa wanan karon don Abin nasa yayi masa yawa gida ajefeshi haka wajen neman halak dinsa a jefasa, ga makiya yan hassada suyi masa yawa, haka kuma a gidan matansa basu barshi ba. Ta sake girgiza kai tana duban wanan faifai din gabanta data rike tana fadin yanzu ba lokacin wani bincie bane dole bakin rafi zamu a fara bada sadaka . Saidai idan karyan nan yaki tafiya ya tsaya a waje daya haka na nufin sadakar bai karbu ba ke nan saidai mu zurwa sarautan Allah ido gaskiya. Amma da zaran an saka wanan kwaryan ya tafi yabi ruwa insha Allahu wanan sadakan ya karbu ke nan don haka sadakan zai kasamce biyune a yanzu. Da wanda zamuyi don dan uwanka dake fama da lalura a yanzu sai kuma naku kaida sauran yan uwanka da a yanzu ba aikai gareku ba. Don haka dole muyi gagawan yin riga kafin akanku kamar yadda al,adan abin yake murya iyace ya katse matar da take fadin. Aah, Ikon Allah inda ranka kasha kallo dauda nan kuma ka kawo yar uwarka da zurian ta don son kai irin naku dauda ? Tsohuwa kiyi halkuri ayi wanan hadayan kafin komai ya kai ga jagulewa a yanzu daga baya mayi duk wanan bayanin daku a tsanake. Ta juya gun mama dubu tana fadin kece zaki saka komai a cikin kwaryan nan zaki saka da niyar fansan rayukan yayanki daga mutanen ruwa masu bada sa,a da yarda,,,,,,, Kallon juna sukayi tsakani mama da iya har habu sai matar tace shi yasan komai don shi ya dauki alkawarin hakan garemu tun farko. Dole mama ta mike ama fada mata duk wani abinda zatayi suka dauki kwaryan dake da abubuwa a cikinsa hardasu masa kosai alawa ayaba sukari da turmin zani zuwa bakin rafi . Tun bayan isarsune wajen dole mama dubu din ta taka zuwa ciki ruwan tana bin matar da kwaryan farko wanda zata fara sadakan dashi akan jafar din . Gaba dayansu gabasu na faduwa wajen son ayi abin cikin sa,a ba tare da an samu matsala ba matar ta karbi kwaryan ta fara jera kirari tana daga kwaryan sama tana saukewa . Suna tsaye suna kallon ikon Allah a gefenta can ta mikowa mama dubu tace tayi niyar ga sadaka ta kawo masu idan sune sanadin rike danta jafar tana rokon da su sakeshi ta biya sadakan da suke binta akanshi . Saidai yadda ta aje kwarya a saman ruwan ko alaman motsi baiyi ba hakan yasa gabansu ya fara faduwa cikin tashi hankali. Wanda hakan ke nufin cewa da alama jafar din yana da wuya wanan abin ya barshi hakan na nufin dai sai abinda ya fito daga Allah gareshi kuma. Anyi anyi kirari kwarya yaki matsawa daga inda aka ajeshi hakan yasa aka miko mata na sauran yaran nata wanda shima yake da nasa kalan tarkacen abin mamaki a na dorawa a saman ruwan kwaryan ya soma tafiya yana bin kabin ruwa da sauri. Gani hakan yasa habu dake tsaye gefe daya bakinsa dauke da addu,oinsa ya tako daga inda yake zuwa wajen kwarya farko da aka aje don jafar din ya cira shi ya daga yana fadin ka tafi kaima kamar dan uwanka ya dora saman ruwa suka bishi da kallon mamaki. Suna jin tausayin irin halin dayake ciki da har baisan abinda yakeyi ba a lokacin ciki yardan Allah sai kwaryan ya fara dan juyawa sannu a hankali saman ruwa ya soma tafiya shima .