← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 201 OF 306

Sashe 201

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasamcewar manya a wurin hakan yasa na rakube gefe daya kokai ban dago na kalleta ba mama ke fada da ita sosai hakan yakai ga tace da iya . Lamarin yarinyar nan dole in kasance a gidan nan tare dasu don abin nata ba hankali sam a cikinsa . Ga yaron nan kwance amma yarinyar nan bata saduda ba sai banzan haukan kishi da take kokarin nunawa mutane ina ita din dai matarshice ko ? Ko har da hakan baki yarda dashi ba na taba ganin wanan rashin hankali wanan ba kishi bane haukane ai har yaushe mijiki yana kwance haka sharkaf a hannun Allah kika samu bakin kishi ? Koda yake bata da laifi laifin Dubuce dake kama mata duk abinda tayi yarinyar ko yar gidan uban waye aini bata kai min hakan ba na rasa meke damun Dubu akan wanan yar ? Irin haka ai dole ta dauka kowa baida daraja a nan tayaya zan zauna matan dana tana wanan iskancin a gabana ban dauki mataki ba ? Har idan an barki dashi din uwar me zaki tsinana masa a nan din banda fitinan da kika saba don kinga Dubu tana kama maki kafan iskanci. Mama ba sai kin tanka mata ba ai ku barta muga abinda zatayi din a nan Rahama zata zauna har zuwa lokacin da Allah zai bashi lafiya to ai shike nan mama ta kara fada. Da farko banyi niyar zuwa dakin da kayana suke ba don wata zuciya dake dibaba akan na koma gidana kawai in zauna yafi min sauki da zama nan tare dasu din da zanyi. Sai kuma nayi tunanen idan nayi hakan ban kyautawa yaya habu dasu mama din ba wanan yasa naja bakina nayi shiru saida aka rage a falon na shiga dakin komai a gyare yake tsab a dakin. Sai yar jakata dake saman gado aje na dauka na bude wardrobe na saka a ciki na shiga bandakin nayi akwala na fito sallah nafila nayi na roki Allah ubangiji ya tsare ya kareni daga duk wani fitina daka iya tasowa a gidan. Muryan mama dake kirana a falon yasa na fito take fadin zoki gyara muna wajen kwanciya ita wanan mai sababin da a haka zata barmu mu kwana a zaune ke nan ? Na gyara masu shimfida don a kasa sukace zasu kwana ni kuma na zauna a saman dogon kujeran da aka bari a falon don zama don an kwashe sauran kujerun falon ankai ta bayan ginan . Asmau ce ta fara shigowa da yaran ta ta zauna an dan jima kuma saiga saiba din ba wanda yayi magana don kowa ya gane manufarsu a nan zamu kwana dukkan mu dasu ke nan abindai ba tsari gaskiya. Ni dama ace rabawa akayi akan duk ranan da girki ya dawo kaina sai inzo nayi aikin da zanyi in koma amma ba ace in dawo nan din in zauna haka a tsakaninsu ba. Na dan jima a zaune na mike zuwa dakin bancewa kowa komai ba na kwanta don duk a gajiye nake addua nayi na lumshe idona ina tunanen duniya. A hakan barci ya daukeni ban sani ba barci ko sosai nayi don ban falka ba sai tsakiyan dare sosai da fitsari ya tayar dani dana kewaya na dauro alwala na fito. Ina sallah nake jin muryansu a falon sama sama hakan baisa na fito ba don ina son kama kaina don gudun zargin kishi . Har yakai ina jin muryoyin nasu sosai hakan yasa na daure nafito don na fahinci akwai matsala a lokacin shina sama yanata kwara amai daga kwancen da yaken wani irin bakin amai kamar an wanke bayan tukunya ga yawan yunkurin da yakeyi din sai ya baki tausayi don da gani cikin wahala yake zuboshi. Daki kamashi ya dago mama ta fada saita juyo ta dan dubi mama din tana fadin ni yaya zanyi in kamashi haka mama ? Ke yar nan amma baki da kunya dazun nan kike fada akan wata tazo ta taimaka yanzu kuma kice ke baki san ya zaki kamashi ba ? Duk yadda zaki kama ai kin sani tunda wace ke iyawan kin yakinceta da zuwa kusa dashi din yanzu ki dagoshi kada ya sarke don Allah ? Tayi kamar zata dagoshi din sai kuma ta fasa ta juyo gun mama din tana fadin sai wani ya taimaka min hakan yasa mama tashi ta kamashi a hannunta ya karasa aman saida ya gama ta wanke mashi bakinsa. Washegari kuma dai haka mama tasata gaba akab tayi mai wankan magani din a wahalce ta karasa kwana biyun ta sai gashi wai ta kwanta bata da lafiya tunkan lokacin ta ya kare Asmau ta karbeta din . Dole mama tasa na kama don Asmau ko wahalan goyo ya isheta haka dai ake rayuwan a jigirce don kowa mama bata bari ba a cikin mu wanan zaman sai gashi an daina zuwa kwanan da aka fara saidai wace zata karbeshi itace zata shigo koshi na dolene nikan da rana bani wuni dasu ina wajen exam dina . Wani lokaci kona fito da wuri zan wuce can gidana in huta sai yamma zan dawo sun wahala lokacin don mama zaune suke suna bada command kuma dole ayi din . A hakan na gama exam din na a wahalce abin farun ciki amma yazo min da rashin walwala don ba wani farin cikin da nayi da hakan asalima nasan dai faduwa zanyi ga jerabawan nan don banyi karatu ba . Dole na mayar da hankali gun jinyar yaya don yadda ko ganina yayi na gitta ya kafawa wurin ido ke nan bai kawarwa sai idan ya daina ganina . Don a yanzu yana gani saidai ba magana ba kuma wani motsi jikinsa a sake yake kamar jikin ya mutu nakan kebe in samu wuri inyi kuka mai isata in fito. Tun dai ranan da Saare da Saiba sukai min habaici a cikin magana da Saiba ke fadin kwadayin wasu baiyi rana ba don an kare a wahala. A dama ai ance kuda wajen kwadayi yake mutuwa wanan kudan da alama kan a kwadayin za a mutu don an fada ruwa tsundum . Kudaje dai don ba kuda bane kawai mai kwadayi akwai sauro mai dafi yasha jinin na tare dashi acan ake makeshi wajen kwadayinsa . Wanda bai ko fara allon sa ba balle ya biya shikewa mai sauka shagube ai gara da wanda ya sauke yafi wanda bai gwada saukan ba. Ai Gara da kudan ya san dadin kwadayi don dai ya lasa din koda pdll Qwya mutu, don ba duka kuda bane suke mutuwa a wajen kwadayi. Balle shi wanda ko masunsuni bashi da yaje zagin mai kamshi,daji bai ga ma cin wuta balle aiwa kututure barka da arziki. Me kike nufi da hakan amsan zancen ku na baki indai kwadayi ya shigo dani gidan dan uwanki ai gara dani na lasa keko dako gidan da zaki baki sani ba fa ? Kina nufin bata aure ke nan kome duk yadda kikace inma haka kuka dauka don ba wace zatace cas bance da ita kule ba a cikin ku. Salatin da Anty barakha ta saka yasa mu kallon kofa ta karaso tana fadin wanan wani irin rashin hankalone mijin ku na kwance haka a wani hali kuke haka a gabanshi don Allah ? Anty yarinyar nan yar rainin wayauce daga muna magana da ta sako muna baki a zancen mu tana son fadawa mutane maganan banza don tana ganin yanzu daidai take da kowa a gidan nan ? Haba dai kamar ya daidai take da kowa dama ai daidai taken da kowa tunda itama aure take kamar kowa a cikin gidan za ace ba zatayi magana ba kuma idan ya shafeta ? To shike nan dama kuke nuna mata hakan shiyasa take kokarin dagawa mutane kai bar ganin a kwanaki kin shanmace mu kina ganin kamar kinci galabane a kan mu lokacin ? Ko zaku gwadane a yanzu ko zaku rama duk macen datace zata sakani gaba a gidan nan mu zuba da ita ban shiga tsabgan kowa a cikin ku ba balle mace tace zata fada min magana na kyaleta ? Abinda kowan ku ke takama dashi shine miji nima ina takama dashi a yanzu don haka kikai min ba daidai ba sai dai muji zafin a tare dake wallahi. Ramaah ki kyale zancen nan ku duba bawan Allah nan a kwance a tsamanin ku baya jin abinda kukeyi ne don baya iya fadane kawai amma yanzu yaya yana fahintar komai da akeyi gabansa. Anty Salima idan kwadayi yasa na auri yaya itama kwadayinne yasa ta auri mijin kawarta ai don ta fini zalama tunda ita tanace saida ta aureshi . Dani dake waye makwadaicin a yanzu ciwo kuma Allah ne ya dora mashi shi kuma zai yaye mashi aduk lokacin da yaga daman hakan gareshi ita kuma Saare rashin sanin zafin dan uwanta yasa har take furta hakan gareni a yanzu. Idan fitsari banzane kaza tayi mana aiko ida nufi bajintane ga mai rabo aurena da dan uwanki nufin Allah ne a garemu mu biyun duka inma cutane ni kuka cuta da mugun nufinku a kaina daya koma min hakan a yanzu. Don haka ni ban raina kyauta da baiwan da Allah yai min na matsayin mata ga yaya ba duk da halin da yake ciki a yanzu kuwa. Lafiyanshi najawa ba abin duniyan dayake tsone maku ido ba don ban taba saka abin duniya a raina ba aure nayi da yaya na tsakani da Allah ba don komai ba iyauyena sun amince dashi a gareni a matsayin miji nima na amince da hakan don bansan baiwan da Allah yai min na dalilin hakan ba ? Ku dake ganin kwadayi ya kawoni na aureshi yau gashi ya fada jinya a halin rai kwakwai ku hakan yaiwa dadi har kuka fada baki sake don ba Allah a zuciyarku. Haba don Allah ina wanan zance ya fito haka kuma lafiyan ku kalau kuwa muna da mutum haka a gaban mu har kuka samu wajen fitina haka don Allah ? Asmauce take fadan hakan a cikin zafin rai na juya gateta a zafafe ina fadin anty Asmau matukar Nusaiba bata rike girmanta a kaina ba nima ba zan taba girmamata a
Chapter 201 · 0% Book details