← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 306

Sashe 174

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

. Sai ranan na fahinci waye mama da kyat suka samu na fito daga part din cikin masifa don banson na bar gidan su mayar da abin akan yar uwata dake fama da kanta aiki daba kan ranan sungashi wajena don ban raga masu ba. Asmau tazo har inda nake tana fadin kizo ki bar gidan nan don Allah don in baki tafi ba fadan nan ba karewa zaiyi ba wallahi. Na budawa idona yaji nace ba inda zan tafi saina tashi so nake tazo ta murjeni kamar filawan datace an fada mata shiru shiru tsorone dama niba maria bace da take kyalesu duk wanda yai min zan mashi nima ban kaunar a zauna lafiya din. Kawune ya soma zuwa cikin wanda mama ta kira tun a get ya soma fadin asshaaa subahanallahi garin yaya haka ya faru kuma ke dubu ? To kadai gani ace yarinyar nan ta biyosu da masifa har gida irin haka don ta rainawa mutane wayau komai ? A,a mama inda ita ta biyosu ai part din mu zata nufa ko amma a wajen yar uwarta fa ta sameta saida nace kada Saiba ta fito don Rahama taba yaran nan abu shine wani abu don Allah ai,,,,,,, Kaji munafunci ko zaki juya zancen yanzu Saiba datace taje ta shirya tafito da wani bakin dogon wando da t,shirt ajikinta take fada ta nufoni kawu yana mata tsawa. A lokacin kuma motan su yaya ibrahim ya tsaya suka shigo gidan ankira mazajen mu an fada masu abinda ke faru shine yace yan uwansa din suzo gidan. Tare dasu na koma gida inda suka jawa kowa kunne kan duk wanda ya kara tayar da zancen wallahi su zasu dauki mataki mumuna akan mutum. Jin hakan yasa na yarda na bisu badon naso barin yar uwata ba da naga suna da niyar illanta muna ita haka kuma mijinta dake kusa ya kamo hanya zuwa zaria hankali a tashe kar wani abu ya samu matarshi din. Gaba dayan su na barsu da tabona a jikinsu zakice ko wani abu na samu nayi masu illa haka dashi duko hannunane yayi masu wanan aikin haka ? Ana gwadawa bafulatani hanyar keta muda in muje daji muke gwada karfin mu da juna don gudun ta taso a garemu . Kodana koma gida daki nashiga bance da iya komai ba jin hannuna yana son takura min da tsami yasa na gasa jikina da ruwan dumi na shafa rob na sauya tufafina wajajen karfe biyar na fito falon. A lokacin kuma kawu ya shigo gidan shida mama sukayi sallama sai lokacin iya kejin abinda ya faru a bakinsu don irin fadan da mama din take min akan me zan hada har saratu don tana rabamu ? Dakata Dubu ban fa fahinciki ba shin da saratu akai fadan nan koda yar nan Nusaiba don zancenki yana nuna da mutum biyu akai fadan nan haka ? Iya dasu biyun nefa duka tayi fada haka daga maganar fatan baki zaki dinga kai masu duka kamar kina jirace dasu dama ? Kaiya iyan ta fada ta kara fadin nace kaiya dubu ina hankalinki ya shigane wai har hakan yakai ga faruwa ? Ba yau ba kinsan halin yaran nan haka suke wanan dabi,an takaiwa yar uwarta duka daga magana kadan sai duka ita saratu ya akayi ta shiga zancen shine ban gane ba ? Wai rabasu takeyi shine kawai ta,,,, dakata muji daga bakinta ai tana da hujjan yin hakan tunda ba hauka tayi ba ko ? Jin abinda iya ta fada yasa na soma magana banji nauyi ko tsoron idon mama ba don zuciyana daya bushe a lokacin komai zai faru ya faru shike nan nace. Ina school Maria ta kirani tana fada min zancen rashin lafiyanta shine na kira yaya nace zanje na ganta dana isa ina jin yunwa na dauki youghout ina sha nan dai na fada masu komai tas har dukan da saratu din takai min. Kaiya iyan ta fada a hasale ta kara da kin min daidai gobe ta koma in halintane tunda bata da mutunci ita a fakaice ta shigarwa masoyiyarta fadan ko saita hadu da fulani sukai mata maigaba daya. Ta dauka ta hada fada zataci bulus ko tunda ta zata irin sakarancan ne da suka saba tauyewa su zalunceta tayi ta kuka ana dariya gobe su kara in halinsune iyan ta fada. Amma iya wanan abu yayi yawa ta yaya zata bisu har gida tayi masu wanan aikin kamar an turota tayi masu hakan sai iya ta dubi mama tace kila nice na turata tayi masu hakan ko ? Bakiji kunyar wanko kafa zuwa gidan nan kina wanan maganan ba dubu aure fa ba bauta bane dubu duk abinda ya faru dama an shirya a tozarta yarinyar nan ne sai Allahnta yafi nasu ya dorata kansu duka shine kuma yanzu don an daki yarki data saya aka sayar mata kikazo fadan haka ? To ki bari mijinta ya dawo dubu sai kisa a ranan ya saketa ina shike nan tunda kina da power hakan a hannun ki idan bashi ba wanan abin kunyan ina na taba jin haka ? Fada ya hadata da abokiyar zamarta yarki ta shiga ta saya an mata dukan tsiya yanzu kinji haushin hakan tunda ba ita bace aka samu sa,anta akaiwa hakan ? Iya na yarda yaran nan da goyon bayanki suke haka tana ganin tafi kowa a yanzu don an nuna mata fifiko akan abokan zamanta har take ganin zata iya dukan saratu a gabana ko ? Yau muna ga rasulu shine zancen mamakin iya idan abu ya daure mata kai shi kuma ta furta a lokacin cikin mamakin mama dubu din dake gabanta. Tace yanzu ai gata nan idan kinzo sakintane saiki bata takardanta kowa ya huta ina zance ya kare tunda baki iya tsayawa can ki tsawata yarki datayi abin kunya ba haka ? Iya ai abin bakai can ba don dai kawai abinda ya faru kar a koma hakan ne yasa mukazo mu tsawata mata don gaba kada a ,,,,😑😑 kai dakata don Allah ta fadawa kawu daya soma magana. Tace bakinku daya kowa ya sani kunji zafi ba itace akaiwa duka ba don baku da kunya kuka kwaso jiki zuwa nan kuciwa yar mutane mutunci ko ? To Dubu kin kai ga yadda kike so ai yau gari ya dauka ga abinda yarki dake kuka taru kukaiwa matan danki har da kishiyarta abin kunya kamar yar nan zakuyiwa taron dangi haka dubu ? Ganin yadda iya bata basu daman magana ba yasa mama ta soma fadin iya kinsan dole in tsawatawa saratu ai duk abinda ya faru itace ta jawoshi. Don anba yaran nan abu zataje ta fadawa uwarta ita kuma don bata da hankali takwashi jiki zuwa fada duk nayi masu fadan hakan amma yadda yarinyar nan tayine bata kyauta ba tunda muna wajen muna tsawata mata ai. Daga gefe na bude baki nace mama kuyi hakkuri don Allah amma ni banje gidan nan da fada ba itace tazo ta sameni ta soma zagina ganin tana da niyar kai min duka nima nakai mata. Amma da nazo yakamata ki dubi tsufana ki ji me nake fada aiko ayi hakkuri nayi kuskure hakan ko gobe ta kawo maki kada ki kyalesu tunda da niya sukai hakan iya ta fada. Keko iya inji kawu ni tayi min daidai yau don Allah ya nuna masu mugun abinsu a fili gobe su kara in halinsune gida kuma ba zata fasa shiga ba tunda gidan mijintane kuma yar uwarta na gidan zaune dole ta shiga. Ai don haka muka taso iya amma kin hana ayi magana kamar kina zugatane fa iya irin abinda kike fada yanzu ? Dauda so kake su daketa taki ramawa kome don ban fahince kaba har yanzu yarinyar nan kowa yasan halinta magana ba magana ba duka ne zata kaiwa mutum . Ba haka tayiwa Salima ba wani lokaci kan dan maganan fatan baki kuma yarinyar nan tasani suka dai samu suka tafi don magariba daya kawo jiki lokacin. Tunda na shiga daki ban fito ba don gaskiya jikina yayi tsami abinda na dade banyi ba biba tashigo ta sameni take tambayana ta kawo min abincine nace tea zansha. Zata fita nace ta miko min wayata a jaka ta dauko min miscal din dana gani a lokacin bana lafiya ba duk kuma nasan akan abinda ya faru dinne ake kirana din. Nasa kiran kusan goma sha hudu gana yaya habu har ukku sai na Nafisa da anty salma na anty Salman na fara dauka . Tana dagawa take fadin ke Ramaah meya kaiki hada jiki da kishiya ashe bana fada maki hakan tsiya yake kawowa ba ga mutum ko ga miji ? Idan ban dauki mataki ba dukana zatayi anty tace taci bulus aida kikayi kadan sai ki bari amma duka haka kamar wace taci tauri Rahama ? Maria tace min taji tsoronki dazun ta dauka ko kina da iskane tace fuskansu da jikinsu kin masu illa sosai a wajen fadan ? Na kwashe yadda abin ya faru na fada mata sai naji tace kin min daidai wallahi ya kirani hankali tashe yake fada min shi a zatonshima wai ciki gareki kikaje kina fada haka ? Tsuki naja jin abinda ta fada tace Allah yace with dis condition naki zakije kina fada a illantashi idan wani abu ya samu cikin jikinki fa ? Kyashi anty ni banda komai a jikina na fada muka kuma koma zancen su din inda tace wani lokacin irin haka idan ba haka ya faru ba dama ba a samun natsuwa ai. Yanzu tunda ta gwada hada jikin taga baci zata koma wani sallonne kuma in bi a hankali don zata fara makirci tunda taga uwar mijin tana kama mata. Ita kuma yar iskan nan sai taji a jikinta ai nace na dauka ai sakina zaiyi idan ya dawo tunda haka uwarshi ke so na daki yarta a gabanta ke kin min daidai wallahi. Maria tace ai mijinta ya dawo ya zo ya karanta masu hauka iya son ransa yace wallahi duk wani abu ya samu matarshi sai yayi karasu kuma yace zai bar masu gidan ya koma gidansa ya gaji da jidali kullum. Ashe ya dawo a gurinta nake ji tace ai ya dawo kuwa yayi
Chapter 174 · 0% Book details