← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 306

Sashe 15

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Abubakar ya kawar gefe daya alaman baima saureshi ba alokacin nufar part din yayi ya fara dukan kofan cikin hasala nocking ukku yayi masu kyau cikin hasala hakan yasa Asmau ta daure ta fito tana fadin ana zuwa kafin ta tsaya tana tambayan waye ? Ke bude min kofa nine jin muryanshi yasa ta bude kofan da sauri gami dayi masa sannu da zuwa dan kallon second ya jefa mata ya gane daga barci ta shi a lokacin ke nan har sun shiga barci. Ciki ya shiga yana fadin wanan kidan haka fa kamar gidan yan kwaya batayi magana ba don haushin da taji da dan cikinta an hanata shakat yazo kuma zai tsareta da tambaya ? Wurin fridge ta nufa ta dauko mai goran ruwa ta nufoshi dashi bai tsaya karba ba kai tsaye dakin Nusaiba ya nufa ya tsaya daga kofa yana daga labule. Kwance ya hangota tayi rub da ciki tana barci sai kanta gwigwiyye da hula ya zame suman kai yayi wani tsatsaye tsirma,tsirma dashi yaja tsuki cikin takaici. Takawa yayi zuwa wajen da kidan ke tashi yakai hannu ya kashe kidan duk da hakan bata motsa ba hakan yasa ya kai mata mugun maka a tsakiyan bayanta ta tashi firgice tana fadin wani dan ,,,,,,,, Ganinsa yasa ta soma kame kame tana fadin umm,umm sweet J dama kana hanya ashe shine baka sanar muna ba ? Fuska a murtuke yake fadin wanan kidan na meye haka ke wata irin yarinyace Nusaiba baki ganin kina daukan alhakin sauran jama,an gida ? Ke shadaniyar inace wai kina yar musulmai da daren nan zaki kwanta min da kida haka a cikin gida kamar gidan disco don rashin tauhidi a zuciyarki ? Aiko kira,a kika saka ba zaki kure volume dinsa haka ba don gudun shiga hakkin wani saidai ki kunna iyake. Daga hakan ya juya ya fita inda ya hango Asmau a tsaye inda ya barta da ruwa tana jiran fitowarsa daga dakin abokiyar zaman nata. Karba yayi kafin yayi niyar zama saman kujeran dake tab da kayan wankin Asmau data nado waje kwanan su sunkai biyar a wajen bata kwashe ba tana kuma kallon kayan a wajen. Tsuki yayi ya fasa zama yana maijin wani irin zafi a zuciyar shi ya nufi hanyar fita part din saidai yana fitane yaga alaman part din duk an kashe wuta ke nan masu part din sun kwanta haka ke nufi hakan yasa ya juya zuwa wajen motarshi daya bari bude bai dauko komai ba sai rufe ko ina da yayi har gidan ya duba yana da tabbacin Abubakar ya rufe ko ina a lokacin yasa ya koma part dinshi kai tsaye wurin iyalinshi. Kallon takaici ya tsaya yana karewa falon dake hargitse zakice ba mata biyune ke rayuwa a part din ba babu inda baida miskila don da gani falon nan bai samu shara ba na tsawon kwanaki . Dama sai ya sanar dasu ranan zuwanshi maigirki takan garje tayi dan kwaskwarima gyaran sama sama don sunsan sam baya son kazanta yanzune da ya iso zai soma fada balle wanan zuwan dayayi masu na bazata babu sanarwa. Don haka babu zancen gyara a wajensu koda ya shigo rasa mai zaiyi a falon yayi ita Asmau itace ta mike zuwa part dinta ta shiga gyara gado tana kawar da kayan data tula a ko ina dakin. Don ta dara Saiba kazanta gaskiya ita dai saiba tana da garjewa ta gyara jikinta da inda zata kwanta amma wanki da sauran aikin gida sune aiki a wajenta. Baicewa Saiba komai data hakkince saman gujera tana jiran taji me zaice dasu ko kuma taga inda zai shiga ya kwana duk da tasan in zancen gaskiya za abi wurin Asmauce zai shiga ya kwana tunda itace tayi girki a ranan sukaci. Dama ance mai mata fiye da daya kullum a cikin lissafi yake don gudun fadawa ga halaka saidai wanda baida tsoron Allah zai iya dulmuye gaskiya yayi son ransa. Donshine Jafar kai tsaye don yabi lissafi tun a hanya ya gano dakin da zai sauka kai tsaye ya nufi bangaren uwargida Asmau wace ya samu tana shimfida zanin gado don shi. Sam Saiba bata ji dadin hakan ba yana shiga ganin ko dan zama baiyi sunyi yaya hanya ba bai bata lokaci ko kadan ba sai taji ba dadi sam a ranta ta mike a cikin fushi zuwa dakin ta. Yana shiga ya tsaya a kofa ya harde kafan shi a waje daya yana bin Asmau din da take aikin gyaran gadon a gurguje da kallo a cikin mamaki. Ta jawo room freshener ta fesa ko ina har zuwa bayi kafin ta juyo gareshi tana dan sakin murmushi tace dashi bissimillah . Ajiyan zuciya ya sauke kafin ya motsa a yadda yake ya tako yana balle aninaiyar rigansa cikin daure fuska tunawa tayi da tabar towels din da yake amfani dashi a wajenta waje hakan yasa da sauri ta nufi falon da bakowa sai hasken wuta da aka a kunni ta nemo tawul din ta kashe ta dawo daki tsaye ta sameshi a bakin bayin tawul din ta mika mashi bai karba sai sunan ta daya kira. Da Asmau ta yaya zanyi amfani da bayin nan don Allah komai a kazance ke wata irice saboda Allah ace mace ba tsabta ko kadan kedai baki kaunar ki tsaya ki gyara koda muhalinkine saboda Allah ? Ai bansan zaka dawo ba shiyasa ban gyara ba ta fada a sanyayye kallon takaici yai mata kafin yace au sai zan dawo ke nan zaki gyara ashe ? Bata daiyi magana ba don tasan jafar yana da bala,in hakkuri da halayensu don da wanine yadda yake dan gayun nan dashi daya anji kansu a kullum amma haka yake shanye takaicin su a zuciyarshi. Abubakar a bangareshi haushi da takaicin yayan nasa ya juya zuwa dakinsa dashi ya rufo duban lokaci yayi a jikon wayasa shadaya bai rufe ba a lokacin haka kawai yaji yana son kiran layin Yanda ya gwada ya gani ko zai shiga. Saidai ya tsaya yana wasi wasin kasan zuciyashi ya kirane ko yabari da safe baijin zai iya hakan yasa ya danna kiran Allah da ikonsa kuwa yaji layin ya shiga kai tsaye ta soma kira. Har ya debe rai da daukanta sai gashi ta daga ta dauka da sallama muryanshi taji yana fadin baki barci ba ke nan ko kuma nina tayar dake daga barcin yanzu. Sautin murmushinta yaji tana fadin amincin Allah ya tabba bata a gareka kun sauka lafiya ko kuna hanya ban zata akwai layinka cikin waya ba ai sai yanzu daka kirani. Ke nan baki duba wayan taki ba ko gaskiya ban duba ba kasan mun wuni aikin gyaran kaya yau da kula da dabbobin baffa da suka wahala a wajen tatsansu da mukai tayi a yan kwanakin nan. Au ashe dabban kayi wahala itama sai yaji tayi murmushi tace halan ba rayuwace da ita ba yadda mu yan adam muke wahala ai itama rai gareta don haka sai mun kula dasu sosai don ba karamin alheri suka kawo muna ba a rayuwa. Sanadin kayan da kuka saye muna na samu baffan mu yau har girki yasa mukayi akaci aka koshi a gidan ko sallah albarka a yau din nan. Yadda take maganan yasa bai katseta ba don yana fahintar wasu abu daga cikin zancen datake ta zubawa din a lokacin duk shi bamai yawan son surutu bane amma sai ya biye mata. Ya fahinci rayuwan yaran a can yana cikin wahala a hannun yan uwan mahaifinsu da zaman su ya koma hannunsu. Suna a cikin matsi da tsangwama babu freedon sam a tare dasu kamar sauran yara karatunsu da sukayi ya tashi a banza yanzu wace takai matakin karatun Nurse a yanzu ta koma tana tatsan nono a rugga saboda rashin gata. Da wanan tunanen ya kwana a ransa har gari ya waye duk da ya dan samu runtsawa kadan saboda gajiyan dake jikinshi a lokacin na bin dogon hanyan da sukayi tafiyan zuwa da dawowa haka. Don shine bai fito ba da safe da wuri saboda bayan sun dawo daga sallah ya koma ya kwanta barci sai zuwa shadaya saura ya mike ya shiga bandaki ya watsa ruwa tare da brush din bakinsa ya fito. Washe gari mama Dubu tana kitchen tana hada masu breakfast sai jin sallaman Jafar din tayi a kofan kitchen din amsawa tayi tana mashi kallon mamaki da yaushe ya dawo. Ya fahinci kallon da uwar ke masa yasa yace na dawo tun jiya da dare ai mama kun kwanta a lokacin Abubakar na samu ya bude min gida na shigo. Malam meyasa baku tsoron tafiyan darene wai don haka take kiransa da malam Jafar kamar yadda uwaye da dama sanadin marigayi malam jafar suna kyautata zaton diyansu su samu irin albarkansa suke kiran yayansu da malam jafar. Ai ba da dare sosai na shigo ba mama wajajen shigowa kaduna dare yayi min na shigo nan wurin sha daya saura na darene ai. Allah ya kyauta nan ya fara gaida ita cikin ladabi kafin muryan iya ya ratso tana fadin wai Jafar ne da safen nan haka ? A nan ya kwana Iya mama ta fada ahawaraki shine baka tayar dani na karbi jakkar tsaraban taka ba ka mikawa marasa hankalin matanka ? Iya ko allura ban shiga dashi ba gida sai makullin motata kawai ko yanzu kina iya karban jakkar kafinsu ya fada yana nufar iya din itama juyawa tayi zuwa wajen kujerun falon ta zauna shima haka ya zauna yana fadin. Habu bai shigo bane ko har ya fitane zuwa wajen aiki mama ta karaso tana fadin anya yau zai shiga kaduna kuwa yadda suka kwaso gajiyan nan suma. Gama tsaraban da yayo muna nan ko kwancewa ban samuyi ba har yanzu Iyace tace badai abinda zai lalace a ciki ko ? To ina na sani iya ai kinga baiko tsaya muna bayani ba yafita da sunan zaije ya dawo har yanzu bai shigo ba kuma karna taba ya kasance ba nasa bane duka naga abinda yawa hakane ? Ba zai shigo dasu nan ba ai idan ba nasa bane kinsan halin Habu ai mama Jafar ya fada shi nake nema ya kamin mu fito da kayan danazo dasu ashe ba
Chapter 15 · 0% Book details