Sashe 89
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
iskan mata kawai na bata amsa da mungama yau ai. Shine suka tareki da bacin rai ga gajiyan exam a tare dake goben nan zan turo a daukeki har gida ki shiri ba maria waya muyi magana . Hakan yasa na mike zuwa falo bata nan na duba dakinta nan ma bata nan sai na leka waje naji hayaniya yana tashi a wajen. Nacewa Salma ina zuwa na kashe wayan nabi bayan ta daidai da zan shiga naga mama ta sakota gaba tana fadin tayi hakkuri suma sun fadane don batanci amma ai fadan ya koma masu ciki yanzu don matakin da jafar din ya dauka. Ranan kan sunsan sun taba mata yar uwa don tayi masu abinda basu taba zato ba ta zagesu tas dama ance kunne ya girmi kaka ina jin muryan saiba daga cikin part dinsu tana fadin idan ta isa tasa a yau din nan a dauki mataki a kansu din idan habun ya dawo. Ranan dai da bacin rai kusan kowa a gidan ya kwana da safe nake fada mata Abuja nayi wurin anty salma inyi hutuna a can din. Bata koce mijin ta aibai gari ba yadda ta saba tauyeni shi kuma idan ya dawo yake hanawa sai cewa tayi hakan ma yafi. Sai can nace kuma kada in tafi na barku daga ke sai Abba ku kadai a cikinsu tace ki tafi ba abinda zasuyi min ki daga ki basu waje kawai zaifi sauki har a kwana biyu. Karfe daya da yan mintuna muna hanya ban tsaya sallama da kowa na gidan ba sai Nafisa data shigo taga ina shiri nake fadawa Abuja zan tafi ranan. Sai ga mama ta shigo tana tambaya yanzu maria kan wanan zancen da akayi ya wuce zaki tura yar nan Abuja tayi murmushi tana fadin badon shi bane mama dama tana da niyar zuwa tayi masu hutu a can. Yanzu haka driver da zai dauketa yana hanya tafe takai zaune tana fadin koda zata tafi ba dai yau ba kan zancen nan dai ya kawo wanan tafiyan shi Habu ya sanda zancen tafiyan natane yau ? Zan kirashi a waya mama dama yasan zata tafi ai ummah ma tace ta tafi din tace to shike nan Allah ya sauwaka ina daki ina jinsu sai mamakin hali irin na mama na sanyi hali nakeyi. Barma dawowan su din nan abin nata kamar ya sukurkuce ne gabadaya kardai abinda suke fada kan suna shige shige gaskiyane hakan ? Koma dai meye sun samu waje da yawa ni dai har tagama ta fita ban leko ba kuma ba a jima ba driver da anty salma ta sheda muna ya taso tun bakwai na safe ya iso daukana din sai da aka gama saka kaya a mota anty maria ta matsa min nashiga na sallami su mama na fito muka dauki hanya. Karfe hudu da wani abu muna Abuja don mun tsaya kaduna mun karbi sako na kuma shiga nayiwa ummah sallama na tafi. Tunda aka shiga min da kayana nashiga nayi sallah ban fito ba ina daki don har lokacin ina jin zuciyana a cunkushe abinci ma nan anty salma tasa aka biyoni dashi ta fita ta barni da yaranta zuwa asibiti duba wata kawarta. Wa jajen karfe biyar maria ta bugo take tambayana mun sauka lafiya na amsa da lafiya yaya na barsu kuma tace lafiya kalau ga Abbati yana kewana. Nace a bashi waya yana jin muryana yasa kuka nake lalashin shi a waya ina mashi waka nan uwar ta karbi waya tana fadin ai habu ya kira yana fada wai meyasa na tafi ban bari ya dawo ba. A raina nace tunda ubana yake ba amma a fili cewa nayi da ita dana bari ya dawo ba zai yarda in zo ba yanzu ko gani hankalina kwance saidai kewan su don ba karamin shakuwane tsakanin muba da ita. Shigowan anty salma dakin yasa mu dakatar da maganan ta karbi wayan suka danyi sharfi akan zancen na wani dan lokaci. Bayan sun gama take fadin wallahi sunyi arziki ba a gari daya muke ba da sunga tsiya don sai nayi karansu wallahi. A bakin iya yake jin tafiyana Abuja din daya shigo take fadin ina kashiga yau Jafaru yake fadin ina can kofan gidan mu iya da abokaina . Nikan nace da kana gida ba zaka bari yarinyar nan ta tafi ba ban zaton zasu barta ta dawo gidan nan kuma don wanan sherin na matanka Jafaru. Wace yarinya iya ? Yarinyar nan me take da suna Nafisa dake zaune take fadin wai Ramaah take nufi fa sunan ma ta kasa fada kullum sai an tuna mata sunan . Ina taje Nafisa tace Abuja dazun aka aiko da mota aka dauketa daga can yanzu kan ai ta tsufa Abuja ita kan saiga salima ta fito daga dakinsu tace . Nifa banga laifinsu ba gara data gusa ta basu waje wanan zargin ya kare hakana haba don Allah wanan iskancin har ina don Allah ku dauki kishin yar uwarta ku yabawa yarinya bataci ba bata sha ba don Allah dai. Humm, kawai yace ya mike tsaye yana fadin iya zan fita me zan sayo maki yau iya ? Jafar kaji saukin fitane irin haka naga dare ya soma yi a yanzu kardai don shedanun matan nan naka zaka tsiri fitan yamma haka ? Bai bata amsa ba ya fice daga gidan motarshi ya nufa ya shiga ya zauna maigadi ya bude mashi lokacin ya ciro waya yana neman number waya. Nidai ina waje tare da anty salma ya kira harya katse ban dauka ba lokacin dana dawo kuma ban koma takan wayan ba nayi sallolina na kwanta. Washegari tunda safe ya fito a cikin shirinsa ya nufi wajen su mama ya samu suna azzakar din safiya ya gaidasu yana fadin zai danje kaduna kila ya isa har katsina saidai yadda hali yayi sunganshi . Haka ya bar zaria zuwa Abuja don shi kadai yasan yadda ya kwana cikin bacin rai ya kulla wanan ya kwance ko iyalinsa sai a bakin kannesa suke jin baya garin. Sam bai manta da gidan anty salma ba direct ya dira gidan ya dan jima a kofa yana kiran waya ba a dauka ba yasa ya fito yayi sallama. Daga cikin masu aikin gidan wani ya shigo yana fadin wai anawa Anty Rahama sallama daga zaria bakuwar data zo jiya.