Sashe 149
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
mata aiki koda yana gari zata iya maimaita kaya guda a kwanaki acewanta wai wankin ne yake mata wuya yasa bata saka kaya lokaci lokaci. Sai salima tace ni banga gara ba a dukkansu duk halinsu daya shiyasa sukai abota a school lokacin don kazantarsu iri dayane wallahi. Nayi dan murmushi ina juyowa gareshi nace a cikin muryata dake kara rikitashi love you too yaya J. Naji ya kara kameni yana fadin really ? Uhumm na iya fada don sallon daya saukowa jikina a lokacin haka muka samu raya daren dashi duk da nasan hakkin wata ya dauko ya kawo min amma sanin halinsa nasan yana da dalilinsa nayin hakan a lokacin. Washegari daga school naje gyaran jiki don nasan dole koda yamma ko washegari zanje gidan don haka dole in gyara jikina yadda zan fuskancesu don ba zan yarda inje masu a yakuce ba su samu abin kushewa a jikina duk da kishiya komai haduwan ki saita hango muni a jikin ko cikin shigarki. Kishiya bata taba hango abinda miji ya gani ya auro ki saidai akasin hakan agareki da zata rike a kamin yakarki wajen miji. Ni kaina nasan gyaran yayi ba laifi a shagon yazo ya daukeni zuwa gida sai sambatu yake duk da da farko na hango damuwa a fuskanshi amma muna hada ido dashi duk bacin ran dayayi dakon ya gushe a fuskansa din lokaci guda. Ina zama yake fadin nawa kika biya matan nan Rahama ? Saida na kalloshi nace dubu biyar suke karba sai naga ya bude mota yana fadin ina zuwa ya fita kai tsaye shagon ya shiga na bishi da kallon mamaki ko me zai masu kuma ? Sai gashi tare da matar tana gyara lafayanta zuwa kai tana gyara rufe jikinta tazo gabana tana dariya tace amarya oga ya kara muna kudin gyara fa. Kinga sako yakai ke nan shine na fito inyi godiya a gabanki don gobe ki dawo mu kara cancara mashi ke dakyau fiye da hakan ya shigo motan yana murmushi tare da gyada kai. Har da musayan lamba mukayi da ita a gabanshi yaja mota ya tafi sai wani kallo yake jefo min can yake fadin gaskiya matar nan ta iya gyara sosai Rahama kinga yadda kika kara fitowa fresh dake don Allah meye sirin da suke maku ne anan wai ? Kin ganki kuwa kin koma min yar filonki sak dake haka har yafi irin ganin dana fara maki Allah a ranan dana fara ganin ki haka kawai naji gabana ya fadi duk da a lulube jikin ki yake da wanan katon hijab din da kike sakawa lokacin ? Amma saida naji gabana ya fadi sak ke din na dade ina nema a rayuwata saidai a lokacin wallahi ban kawo komai game dake ba a raina tunda naga kamar Habu yai muna shinge a tsakanin mu ba yadda zai kasance in sameki ? Sannan kisan me wallahi duk lokacin da zan ganki sai dabi,un ki sun burgeni a lokacin don haka nidai kawai kina burgeni duk lokacin dana ganki amma saboda Habu mijin yarkice bantaba kawo komai a tsakanin mu ba dake irin haka ? Ashe ke dinma rabotace kedin daice mafalkin rayuwata Rahama sak yanayin ki da komai naki kalan dana dade ina mafalkine Rahama macen dana mallaka ta kasance a hakan cikin tsabta da sanin darajan kowa na tare dani ta kasance mai biyayya da dokokina Rahama . Sai gashi Allah ubangiji ya kawo min ke a saukake ba tare da wani shan wahalan komai ba Allah ya duba min kuncin da nake kwana dashi nake wuni dashi yaban ke a cikin ruwan sanyi. Wai ace mace don ta haihu ai irin gyaran nan da miji zai shigo yaji dadi amma ina babu shi Rahama yau saida nayiwa Asmau kaca kaca a gaban mutane. Wanan ai sai a zageni wallahi sai ace kaina kawai nake gyara na barsu a wullakance haka idan kai magana kuma ace mutum ya faye fitana. Zasu gyara ka barsu kawai ka daina fadan dan nan da kake masu a gaban mutane don Allah yayi tsuki kawai ya maida hankalinshi ga tukin da yakeyi din saida muka shiga get din gidan nake tambayanshi ? Yaushe zaka kaini inyi barkane yaya kada ace banje ba ko ina bakin ciki da haihuwan yasa ban damu ba ? Saida ya parker mota naji yace gobe baku fita gobe sai ki shirya in kaiku ku wuni can keda habiba ko daga can idan kun gama zaku dawo in biya daku gidan mu ku gaidasu mama can din. Naji dadin hakan yasa nace har gidan yaya Ai sai muje da anty Rukkaiya yace duk a goben Allah ya kaimu lafiya idan da lokaci sai mu biya ai ku gaishesu. Wanan yarinyar ma ai taso taje taga mahaifiyar ta don ban tsamani ai ta tafi tunda tazo gidan nan ko ? Gaskiya bataje ba tunda tace min ta zata ba haka halina yake ba da tazo da niyar komawa gidane sai taga ashe ba haka abin yake ba ? Aina sani ya fada yana bude mota ya fitar da kafansa daya waje yana fadin koda naje daukanta ai da kuka tafito bata so zuwa nan din ba. Sai gata ta fito daga cikin gidan da dan murnanta tana dariyan ganin dawowan mu tana gaidashi ya amsa yana fadin Habiba dagani dai ba zancen komawa gida yanzu ko anty ta karbewa yaya ke ke nan ? Tayi murmushi tana boye fuskanta nace tazo ta dauki kaya a bayan mota lokacin ta juya da sauri zuwa wajen bayab motan ya bude ta kwaso kayan da nake gani kamar na baby ne yaso lokacin. Saida tayi gaba yake fadin abokina ya aiko minsu daga kaduna yau saidana biya na karbo naje daukoki ai nace dama bai wahal da kansa ba tunda ba amfani zasuyi dashi ba sai dai a jibgesu don basu gyara kansu ba balle yaransu. Ni dai nace rabon sune don haka abar zancen nan ai saida naje dakina na rage kayan jikina na fito na hada mashi abincin da muka girka don rana wanda har lokacin yana da zafinsa saboda kyau warmers din nake amfanin dasu. Banyi wani girkin dare ba fruit salad da nama shi muka sha muka hada da naman muka kwanta ni dai ido na kawo na saka kawai ban kara magana ba tunda na fahinci bai son maganan a lokaci amna dole nasan akwai masa dayasa hakan . Washegari ko tunda safe mukayi aiyukan mu don fitan da nasan zamuyi din yana daki yana barcinsa shigowan kawu gidan yasa naje tmna tayar dashi daga kwana. Hakan baisa mun zauna ba shirin mu mukaci gaba dayayi bayan na gabatarwa kawu da komai na koma kitchen don mu rage aiki tunda nasan sai yamma lis zamu dawo gidan kila ranan . Daga kitchen din na ke dan fahintar abindake faruwa zuwan kawo kan matsalansa da Nusaibane don naji yana fadin ai na fada mata saita gane kureta kawu. Ta dauka da wasa nakeyi ko wanan karon ba zanji ta kowa ba tunda ni ba mai tausayina akan matsaloni dasu sai zance ya tashi ace nayi hakkuri don haka in zata zauna ta zauna tunda zaman mama takeyi ni ba zan koreta amma ba ruwana da ita kowa ya sani. Banyi wani abin asha ba don na tare a nan gidan Asmau ce ta haihu don haka ina da inda zanje in huta a yanzu babu takura a gareni kuma kun gani. Kawu din ya tausa murya yana fadin abinda nake son ka gane tunda har mahaifiyar ka ta nuna hakan bai mata ba kayi hakkuri kai Jafar ka shirya da matar ka kada ka shafawa wanan din laifin daba itace ta sakaka yin hakan ba. Sai naji yace kawu ina yarinyar nan dai nine ke auren ta ba wani ba kuma zamana takeyi a gidan nan don haka ina rokon kowan ku daya saka min ido da ita don Allah ? Nidai har kawu ya tafi banji sunyi maslaha akan zancen ba tsakaninsu saidana gama na fito kitchen din nasawa Biba kira daga dakina. Ta shigo ta sameni kayan dana dinka mata don gudun kada a girshemu haka na fitar mata da kala daya komai set da gyalensa da takalma har yan kunne na mika mata ina fadin taje tayi maza ta shirya nasan yanzu yaya zai fito mu tafi. Ta karba da murnanta tana min godiya murmushi kawai nayi ta juya zuwa dakinta don ta shirya din .