Sashe 299
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
yana son saratu amma ba yadda ya iya da fati matarshi ta farko don macece ita mai tsananin kishi da dokoki matukar bata amince da mace ba, bata taba zama gidan. Don ta shiga gallaza maki ke nan sai kinbar gidan don kanki kuma iyayyen miji suna matukar son ta don ta iya kissan sace zuciya. Ajiyan zuciya ya sauke ya dawo cikin gidan hankalinsa tashe yana bada baya yaji matan sun kwashe da dariyan shakiyanci gareshi baidai juyo ba ya shige dakin daya fito. Wayanshi ya dauka ya kira layinta ana cewa layin a kashe yake haka ya wuni kira ko wani lokaci amsa dayane shine kashe layin nata yake. Ya kira layin yaya J shima ance mai baya samu nan hankalinshi ya kara tashi kada yar mutane ta bata a hannushi ya daiji idan ta isa gida hankalinshi ya kwanta. Bashi ya samu wayan nata yashiga ba sai wajajen goma na dare kuma taki dagawa ya tura mata text tana ina ta bashi amsa da gidansu zaria sai lokaci hankalishi ya dan kwanta. Ina kwance a falo muna hira da mama Aminu ya shigo cin abincin dare don duk fitanshi bai wuce karfe takwas a waje ya dawo gida. Shikewa mama hira da cewa ashe mummy saratu tazo ne dazun na ganta da naje gidan su kauwa anty salima sako wai yau din nan tazo . Na dago kai nace Saratu fa kace tazo yace wallahi na ganta har mun gaisa ita kuma matan uncle ance jiya tabar gidan bayan taciwa mama da uncle mutunci ba irin zsgin da batayi masu ba. Kai Aminu mamafa taciwa mutunci kace to ba zata iya bane don ance taciwa dubu mutunci aiba abin mamaki bane tunda bata samu yadda tayi tsamani ba yanzu. Dama shirin aiba na Allah da Annabi bane akeyi na munafuncine dama yanzu kuma Allah ya nuna masu abinsu sai haka zai biyo baya rabu da abinda ba a farashi da gaskiya ba dama a haka ake karewa. Mama dubuce ke dogon sharfin da yasa duk muka tsaya muna saurarenta shi Aminu ya dora da fadin wai har cewa tayi mama ta tanka a dakin nan tashigo ta murjeta. Kai fa yace iya ke ban labari kinsan iya ta tsani wanan matar donshi tace azo a sakawa kofansu makulli kada ta dawo tace zata zauna nan yake bamu labarin taje gidan da suka koma maigadi ya hanata shiga don an fada mashi ya kulle gida yace ba zata shiga ba tayi cin mutunci ta dawo gida kuma ta dora wani don mama tace tayi hakkuri ta hau zagin nama din har kowa bata ragawa jiyan ba. Shine yau tunda safe ta tafi tana fadin ga gidan nan tabar masu abinda mama da danta sukai mata sai sungani a rabon su kuma wallahi sai ta hanasu zaman lafiya a rayuwansu. Bata isa ba maman tudu ta fada tace yarinyar nan bata da mutunci ko kadan aniyartane ya koma masu daga ita har dubu din data marawa karya baya. Dama ta dawo gidan nan da niyar fitar da Rahama dakinta sai Allah ya nuna masu yana bayanta duk abinda sukeyi bai taba samunta ba kuma baisa ta saduda ba ga hakan rabu da wanda Allah ya tsarkake zuciyarsa kaji. Wai koda ake cewa na fadawa yarinyar nan ta tashi tsaye tayi hankali da ita sam ban taba fada mata ba balle hankalinta ya tashi hakan yasa nayi murmushi ina fadin. Mama nifa bafilatan asalice bani sheri ga kowa in kaimin ya bika haka nima idan nayi ba zai barni ba donshine mu fulani bamu damu da yiwa mutum mugunta ba muke kuma cikin daji zaune da dabbobi lafiya. Kai Anty kikace fulani basu mugunta karshe ke nan Aminu ya fada yana dariya Aminu bamu mugunta saidai ramuwan gaiya a cikin fushi. Bafulatani duk ka cuceshi da safe shi kuma zuwa yamma sai ya dauki fansa ko shekara nawa akayi sai mun rama abu ga mutum don bamu mantuwa. Saida ya tashi mama ke fadin akwai dai ba banza yarinyar nan saratu tazo gida ba dole akwai dai don in zatazo ai tare da mijinta ko wani nasa ya kamata ace tazo zuwan farko. Amma haka kimkam ace Saratu tazo dole akwai dai ba bamza ba gaskiya koma meye ai zamuji bari dai mijinku ya dawo zamuji ko meye don duba ba zata fada ba yanzu. Allah ya sauwaka nace na dora da fadin ni nazata tazo ganin gidane tace wani ganin gida har yaushe tabar garin nan da za ace tazo boyewa sukeyi amma auren ba dadi tunda aka kaita. Can dana je gida nake ji wai ashe yazid yasa an kulle kawunsu gidan yari ko kudinsa ko fursuna yanzu jafaru ake jira ya dawo aji. Kuma ance shi yazid din ya koma abuja abinshi ya zauna bayan yasa an kulleshi amma ai kinga dubu bata fada muna ba sam bata son asan komai kan diyanta. Shi kuma mijin ku bayayi saida yan uwansa yanzu shi yayanku shike kokarin a sako kawunku din amma suki sunce sai wanda ya kawoshi kara yazo nasan kudi ya basu don suyi mai haka din. Yayan ku yace Yazid ya fada mai kudinsa yaci yaki fitowa dashi idan yaji matsi zai fito mashi da abinsa so yake a bada hakkuri a manta zancen ya cinye kudin daga baya shiko bai yarda da hakan sai ya bashi kudinsa koda zai sayar da gidansune. Kaj amma yazid bai kyauta ba kawu zaisa a kulle ai yaci ragowa a wajensu ko don mahaifiyarsu dan uwan haihuwantane fa ? Baki san yazid ba ko yazid baida kunya haka ya tashi da rashin mutunci tun yana karami zuwa karatun nan da Alh ya turashi waje shinema saukinsa yanzu . Nashiga daki ina mamakin wanan rayuwam na mutanen gidan mu na yau daban na gobe daban kullum a cikin rikici suke zancen kudin nasan dashi na dau boyewa mamane kamar ban sani ba ashe abin har yakaisu ga haka. Ni yanzu a kwanakin nan ba abinda nakeyi sai tuno da yan uwana da muka bari a rugga cikin wahala musane ya taba zuwa maria ta haushi da fada lokacin don me yazo ace mun taru mun cika masu gida . Haka tashi gaba muna kuka ta sallameshi washegari ya koma gida tun lokacin bai kara dawowa zaria ba banjin koda mama tayi aure kaduna sunzo kin san mu fulani da rikon tsiya a zuciyar mu. Saida naba matan hardo sako da sukazo sunan Amir akai masu tare da wasika a ciki nace su kirani har zuwa lokacin banji kiransu ba ni duk yadda yaya jafar yake da yan uwansa ina son yadda suke rayuwansu a waje daya din nan amma mu tamu kaddarance mu taso ba tare da yan uwan mu ba. Dan uwa fa rufin asirine yau da dayansu zaizo ba zan taba korashi ba zan rike abinane duk abinda mama zatace saidai tayi matukar ba mai gidanne ya koreshi ba. Amma ita tsoro da zurfin ciki yasa tayi masu abinda ba zasu taba mantawa da ita ba a lokacin saida mukai karamin gaba da ita na gaji na sake zancen yanzu ko ina son ganin su sosai a raina. Ina dadin muna cikin daula su suna cikin wahala ba tare da mun taimakawa rayuwansu ba sun fito fili tunda tare mahaifin mu ya barmu dasu.