Sashe 36
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai mama Dubu ta bada lokacinta tana kula da yayata haka kuma taja min kunne nasa ido kan yar uwata sosai ga duk abinda zataci ko zatayi a gidan. Hakan kuma nake wanan kokarin duk da a lokacin akwai sauran kurciya sosai a kaina amma ban fita saina tabbatar da nayi komai daya dace a gidan. Dana dawo kuma zan shiga in mata abinci da gyaran waje saidai indan mijinta yana gari dan yanzu bai faye dogon tafiya ba sosai. Koya tafi baifi yai yan kwanaki ba ya dawo saboda laluran matashi a yanzu duk da abin baikai daga hankalin da kowa zai fahinci akwai matsala ba gareta. Bayan kamar wasu yan satutuka ya Jafar daya je kasan waje kamar yadda nakeji a bakin matanshi da yan uwansa ya dawo kasan. Ranan Anty Saiba ta sauke jin kanta ta samemu a part din Iya zaune muna kallo take fadin Sare zuwa nayi don Allah muje wajen mu ku tayamu aiki. Anty Sare na mata ba,a da cewa lalaima ba dole ba maigida zai dawo ana mashi soye suka dan taba ba,a zata tafi har ta juya sai kuma ta tsaya tana fadin . Ramaah har kefa zamuje don aikin yayi muna yawa sosai gashi rana yayi komai bamu hada ba yasa nake son don Allah kuzo ku tayamu. Mama dubu ta kalli inda nake zaune tana fadin Ramaah ai bata da matsala ga dai mashiririta nan su da kika fara gaiyata ba komai zasuyi ba banda surutu. Saida naje wajen antyna na gyara don mijinta yana iya fadowa ko wani lokaci gidan yasa koda yaushe cikin tsabtace mata wajenta nake zakice ba wani mahalukin dake rayuwa a part din don yadda yake kal ko dayaushe. Nayi mamakin yadda na samu wajen nasu don na kwana biyu banshiga ba saboda exam din da mukeyi banda lokacin laka part dinsu a yanzu . Haka kuma iya ta hana wanan aikin da Asmau ke fakewa tana sakani a baya yanzu iya tayi mata gatse da hakan yasa na samu ta shafa min lafiya. Don wai ashe shigan cikine da ita lokacin yasa take narkewa haka bata iya yiwa kanta komai a rayuwanta nayi mamakin yadda mata biyu zasu kasa gyaran wanan katafaren ginan nasu . Su biyu sai yan yaran su amma part din har wani bashi yakeyi da tsamin dauda tunda daminane a lokacin aka shiga. Kitchen na samesu tsaye suna shawaran abinda zasuyi din ga dai kaya abincin nan amma da yawa sun lalace saboda rashin amfani dasu da ba ayi sun lalace. Wanan bashin kuma wai daga fridge dinsune wari ke fita haka da ace nice zan kwashe kayan nan kaf in kyautar dashine in wanke fridge din insaka kamshi ko wani yaro ba zanso yaji wanan warin da fridge din nan keyi ba balle babba. Saidai kashh duk sherin da Sare ke zuba masu kwando kwando bai sa sun duba maike wanan warin haka su fitar dashi ba karshe falo muka koma muka kara aikin ko a nan ma warin bai barmu mun zauna da dadin rai ba. A dakin Nusaiba maigidan zai sauka shine dalilin wanan shirin da mukeyi din inda Asmau take dakinta tana shakar barcinta hankali kwance saida muka dawo falone hayaniyar mu ya tayat da ita ta kuma dan jima bata leko falon ba a lokacin. Saida ta bushi iskanta ta fito sabe da yarta a kafada da dan cikinta daya tasa kadan tana fadin duk aiki ake sha hakane ? Banza kowa yayi da ita ta samu waje ta zaune don sun fahinci kishine ya hanata fitowa a yadda na kula su anty Sare sunfi kula Saiba bisa ga Asmau wata kila don kyautantane data dara Asmau din dashi ko kuma wani abu can dai na tunanensu. Dukko da cin mutunci irin na Saiba da nuna ita watace kuma matan wani saidai zasuyi fadan kiga sun dawo sun shirya kuma dasu nidai wanan abin yana daure min kai dasu sosai wallahi. Munyi cake dunut milk pop wanda a karshe aikin ya dawo nawa suka koma tayani don da ban wajen shirme zasu tabka da hasara don basu iya kwabin bama balle . Wasa wasa saida muka kai yamma don suyan kajin da muka tsaya yi wanda yayi ja gwanin sha,awa dashi sai bayan magariba muka samu kan mu da aikin muka kammala . Ni dai ina mamaki rashin ganin sun gyara falon gidan tsab da sauran part din gidan kosu Sare banji suna masu tunin hakan ba a lokacin a kasan raina nake mamakin hakan sosai a lokacin. Wanka na shiga antyna tana falo zaune tana azzakar Saiban ta shigo part dinta tana fadin ina Ramaah ga dan abin da mukayi na debo mata. Tana wanka Anty maria ta fada ta aje saman table suka danyi gaisuwa sama sama da yar uwar tawa da sai bin wajenta takeyi da kallon mamaki don ko kai waye shiyan yar uwata dole ya baka sha,awa kome tsab yake ga kamshi. Ita Saiba zance baifi sau nawa ba duk dan zaman mu gidan data shigo part din sai wanan dalilin daya kawota yanzu din. Kodana fito wanka ta fice antyna ke nuna min nake fadin kici donni ya hau min kai tun a wajen suyan da mukayi din na koma nayi sallah. Saida na fito take fadin ina ganin Habu yana hanya Ramaah kallon ta nayi ina fadin ya bugo ke nan tayi dan luuuu da ido tana fadin haka dai naji a jikina kawai kamar shima zai zo dai yau. Hira muke jefi jefi da ita wanda hiran zaman mu na Abujane wanan abin da mukayi ya tuna muna idan wani zai dawo gidan yadda akan wuni ana gyaran waje da aiyuka saidai su banga hakan garesu ba ko kadan. Karan wagale get din gidan da akayi ya katse muna hiran mu wanda mazan gidan ne suka iso lokacin ashe zancen antyna gaskiyane ya Habu shine yaje ya dauko dan uwansa da yai wajen wata uku bai kasan . Ta window part din anty na muka leka mukaga tare suke ashe dukka su ukku har da wasu mutum biyu a lokacin. Ya Abubakar ya jima bai shigo part dinsa ba don sun tsaya a na sauke kayan yayan nasu zuwa part dinshi na tsaya jiransa mu gaisa sai gashi ya shigo mukai mai sannu da zuwa. Shi mutum ne wanda baida sakewa da kowa haka yake dunkunkun dashi ni ina mamaki ma yadda suka hadu da yar uwar tawa haka. In har kinji muryan yaya Habu yana tare da iya ne ko mahaifiyarsu saiko idan ransa ya baci zai tsaya yayi fada akan abin ko kuma ya barka a cikin zullumin abin. Bayan na gaidashine na shige na dauko abinda zan dauko nafice na koma wajensu iya a zaune na samesu ga kayan tsaraban da aka shigo dashi part din tsofin a gefe daya an tara. Ban zauna falo hira ba saboda gajiyan dake jikina na shige dakin kwanan mu nan ma ba kwanciya nayi ba saida na dan tsabatace dakin har ban dakin kafin na kwanta. Can cikin barci nake jin maganan su Saare dake fadin dama nasan wanan abin sai yaya yayi fada wallahi idan ya iso ya samu waje haka. Warin ne yayi yawa Salima ta fada tana hawowa saman gadon da muke kwana tare da ita tace na bude fridge din aina duba naman kaine yake wanan wari haka. Makin su zubar amma wai sun aje basu fitar dashi ba duk part din ya dume da warinsa ga kuma kazantan dake falon koshi ai takaicine. Banfa sa sunda yau zai shigo garin nan ba Saare ta fada nan nasa masu baki nace kuma gashi munyi aiki ba a gyara falon ba saukin abin ita Saiba ta dan gyaro wajenta dazun din don kodana shiga na samu tana gyaran dakinta ai. To ai a banza Ramaah duk fa cikinsu babu mai tsabta a raina nace kamu na zagin koko ke nan kuma ai halin kuka dauka na fada kasan zuciyana. Sai gashi Salima na bata amsa da fadin abinda iya ke fada muna ke nan kullum wallahi nima dai zagewa zanyi da koyon irin na Ramaah ina dan aiyuka a gidan nan don in saba. Tabe baki Saare tayi tana fadin ko ita dake hakan ai halittance hakan bawai yin kanta bane muryan ya J ya dakatar damu don tabbas a falon iya yake wanan tsawan. Tsit mukayi a dakin muna saurarenshi yana fada ina zan iya kwana cikin wanan kazantar haka iya sai doyi da bashi wajen keyi a nan dakin yusuf zan kwana yau. Muryan mama naji tana mashi fada akan ya koma ya kwana wajen matanshi ai dole su gyara tunda ya nuna masu bacin ransa a fili. Can dai muka daina jin muryanshi a haka barci ya daukeni sai washe gari na falka don akwai gajiya sosai a jikina na mulkan fulawan da mukayi jiyan. Hakan bai hanani fitowa nayi aiyukan dana saba yi ba anan suka dawo suka sameni part din iya suka nufo gaba dayansu shida ya Abubakar din. Wanan ya hanani komawa part din na nufi wajen yar uwata bayan mun gaisa na karbi aikin da takeyi din nacigaba ita kuma ta koma dakin kwanansu tana gyara. Har inda na gama bai shigo ba dakina na koma nayi wanka na gyara jikina lokacin naji muryan shi ya shigo yana fadin . Bansan ya matan can suke son mayar da kansu ba gidan nan miji ya dawo tun jiya yake bala,i dasu akan kazanta ki shiga ki saka hijab dinki kije wajen iya zamu zauna a nan. Ma,ana dai a fahintana zasu dan yi magana da dan uwan nasa nan part din antyna ke nan hakan yasa nayi sauri karasa shirina a gurguje na fito daga dakin kusan lokaci daya muka fito a dakin da ita. Muna gaisawa dashi take fadin naje kitchen na fito mashi da kayan karyawa ita kuma naga ta koma dakinta na dauko muka aje muka fito tare da ita daga part din. A wajen muka samesu shida kawu suna magana muka gaidasu tayi mai sannu da dawowa muka shiga ciki wajen su mama din dake falo suna duba tsaraba. Shi tsaraba ga iyali wani abune mai daraja dana sanshi tun ina kankanuwa a