← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 306

Sashe 126

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Saida ya gaisa dasu iya tagama sakamai albarka ya juya wajen mama yana tambaya suna dai lafiya ko ?
Ido ta zuba mai tana hango annuri da annashuwa a tare da dan nata da hakan ke nuna yana cikin walwala sosai a lokacin saidai har yanzu tana jin zafinsa a ranta wanda ba zatace ga dalili ba.
Ita dai abinda tafi dauka shine yayi aure bada izininta ba ya nuna bata da tacewa gareshi ya isa yanzu bai bukatan shawaranta a yanzu.
Inkin debe wanan ba zatace ga abinda da dan nata yayi mata ba da zata fada don Jafar shine na daya a kaf iyalinta dake mata biyayya.
Zata iya fassara wanan abin da jin zafin abinda yaiwa matanshi na cin fuska don zata kira wanan auren da sunan cin fuska a wajensu yayi aure ba tare da sanin kowa a cikinsu ba inbada kawu da yaiwa dole ya daukeshi zuwa neman aure kamar yadda kawu ya fada mata.
Jin tambayan da yake mata yasa ta nisa daga dogon tunanen da takeyi nasa a lokacin tace lafiya lau muke Jafar ya wajen ita Rahama din naji Habu na fadin bata jin dadi kuma ?
Da sauki tasha magani kafin in fito ta samu sauki don taki yarda muje asibiti ai dama Rahama bata son ko magani balle zancen asibiti Salima ke fada.
Ai naga alama ta daiji sauki da ranan nan don saida naga taci abinci nafito na barta zaune a falo tana gaishekuma.
Iyace ta kara fadin amaryace mai batun hankali injin dai kazo min da tawa sauran kazan amarcin naku ya mike tsaye yana dariya yake fadin iya ke aiba saura za a baki ba taki dakwalwan za a kawo maki dai kema.
Daga part din iya nasa part din ya nufa inda ya samesu a kitchen tsaye suna sa,insa a tsakaninsu kan kayan da aka shigo dashi din.
Daga kofa ya tsaya rike da hannun yar wajen saiba yana fadin wai ya hakane kuma ku dai baku zama bakuyi fitina a tsakanin ku ba ?
Wai cewa nayi a dauko wanan naman daya saura sai a soya kada a hada da wanan shine wai ban isa ba a hada waje daya duka Asmau ta fada.
Don me zakice haka ba ita bace babba ita tasan yadda za a adana kayan ke meye naki a ciki tunda tace haka za ayi jafar ya fada.
Au Allah ko ashe an fara babba a gidan nan yanzu to maji magani ashe ta fada tana mashi wani irin kallo na yatsune.
Kedai baki zama a waje ba ai fitina ba saiba ni bansan abinda yasa kike wanan rayuwa haka ba juyawa tayi ta bashi baya tana juye abincin data gama dafawa a plate ya bita da kallo kafin ya koma fadin.
Wait naga kin juye abincin duka sufa ba zasuci bane tace ka tambayeta mana ai dazun ta dafa itama taci da yaran ?
Asmau yaushe kuka fara girki daban dabab a gidan nan gashi nan a cooler na zuba mata kuma ta gani ta dafa wani ai.
Abincin da yayi sanyi kuke son inci ta juyo tana fada yace ke ba bawan gidan ku nake ba da zaki dinga min barnan abinci haka in saka maki ido.
Gidan mu kan ai kaima kasan yafi karfin ka balle daga magana ka jefo gidan mu a ciki haka kawai daga zance ka nemi ka zageni tunda dama kana hasale dani ?
Na dai fada maki kada na sake gani ko jin an raba min girki a gidan nan idan ba haka ba rai zai baci wallahi ya fada a hasale ya juya zuwa dakinsa.
Asmau da saida ta gama gyara kayan ta fito tabar kitchen din ba gyara ta nufi dakin nasa daga kofa ta tsaya tana gaidashi da wuni ya amsa yana kwance ya dago yana fadin.
Wai Asmau sai yaushe zaki daina zama hakane don Allah kayane baki dashi kome da kika zabi ki dinga zama a haka don Allah ?
Kiwa kanki fada Asmau kece babba a gidan nan wanan halin da kikeyi yasa kike ganin kowa na rainaki don baki mayar da kanki abin kwarai ba Asmau don Allah ki gyara banson haka me kika nema kika rasa a rayuwanki ?
Naji ta fada ta juya ta fita daga dakin tana jinini a zuciyarta cewa ai dama ban taba fari a wajen ka tunda baka kaunata yanzu kome nayi banyi daidai bane.
Shiko tsuki yaja yana gyara kwanciyarsa haushine ya kumeshi Allah ya gani yana son Asmau amma halinta sam baiyi masa ba kazanta da yawan da abu da muhinmanci magana da har bata iya daukarwa kanta mataki shi yake damunsa da ita.
Yaso tun farko ya sameta irin yadda rayuwansa keson matarsa ta kasance bai samu hakan gareta ba yayi gyara ta kasa gyarawa yakai karanta har gaban iyayyenta an tsawata mata amma bata sauya dole ya gaji ya sa mata ido.
Yadda Saiba tazo mashi da karya ya dauka ta kwaraice ashe halinsu daya sak da kawar nata kishiya kuma a yanzu dole yai hakkuri ya zubawa sarautan Allah ido akansu.
Gashi shikan idan ka ganshi tsab tsab dashi zakice inda yake sai kin wanke kafa ki shiga saboda tsabtanshi saidai kuma bai samu mata irinshi ba.
Ji don Allah wai wajen miji tazo a hakan ga wani riga duk jurwaye ta kawo wani zani sama ta dora tayi daura gaba da shi wanan kayan takaicin ina zai kaishi don Allah.
Jin alarm din wayansa dake sanar masa da lokacin sallah ya mike zuwa masallacin nan unguwarsu inda suke bi sallah.
Ana idar da sallah ya shiga motarshi yabar gidaa tudun wada ya nufa ya gaidasu mama kana ya nufi gidan anty Ai da yake son zuwa ya ganta.
Yana gidan Habu ya kirashi a waya yana fadin J kana ina gasu malam sun iso aina dauka kana cikin gidane saida na aika akace kafita.
Habu kuyi yadda ya dace gani nan tudun wanda daga nan kuma zamu fita da Nurane kai habu ya daga ya dubi su mama da sauran jama,an dake wajen.
Baiso ace J din baya wajen ba za ai wanan rabon amma zai dage yaga an fitarwa kowa hakkinshi yadda ya dace .
Aka bude taro da addua tare da bayanin abinda ka,idan kado ya bada ikon abawa ko wani mai hakki kafin habu ya dora da kara masu haske kan yadda dukiyan nasu yake.
Masha Allah wanan bawan Allah yayi kokari matuka abin a jinjina masane sosai duba ga irin rikon amanan da yayi da kurciyanshi.
Abune mai wuya a samu kudi har riba a wanan shekarun don haka su godewa Allah su kuma godewa wanda yayi wanan jajircewan a garesu.
Habu yace ba wani bane illa yayan mu jafar shine aka dankawa kudin tun lokacin akan ya juya har ya fara daga baya yayi shawaran gara ya bada wa yan nan kudin ga wani ya juya ya fara sana,an kanshi amma yana bibiya ko wani lokaci malamin yace Na,am .
Shine dalilin da yanzu da yan uwan mu suka bukaci kudinsu aka fito dashi aka lissafa mun samu kudi ya ninka ninkin ba ninkin muke so a warewa kowa nasa kaso a damkawa masu shi abinsu.
Daidai lokacin kawu ya shigo falon don bai samu karasowa da wuri ba saboda kauye daya tafi duk akan rabon kudin don yana son a daure bakinsu wai.
Duka kudin su dawo hannunsa ba tare da an samu wanda ya mussa hakan ba a cikinsu don ya kula yaron sun soma sanin ciwon kansu a yanzu.
Yazo ya zauna sai cicika yakeyi yana batsewa don me za a fara bashi daga baya daya fahinci ba a soma kasafin kudin ba ashe shine ya dan washe fuskansa.
Malami na farko ya gyara zama yana fadi to ai abune mai sauki yanzu tunda da baya an raba ansan yawan abinda kowa a nan ya mallaka daga mazan har matan sai a soma cirewa kowa nasa kason ko kuma alabashin kasafa kudin a yadda wanan can kadon na farko yake har riban da kowa ya samu zuwa yanzu.
Da yake aikinsune sun saba nan da nan aka fara lissafin yadda ya dace ana ajewa kows nasa gefe daya da sunan da mama aka fara sai su maza kafin a debewa diya matan akasafa masu yadda ya dace.
Ba wanda aka cuta a cikinsu rabo na tsakanin da Allah malaman suka tsaya sukai masu inda Habu ya mika hannu ya dauki na farko yana fadin wanan na J ne.
Jafaru kuma a yanzu ai baida abinda zaiyi da wanan kudin kan a,a hjy ba yana cikin magada ba ?
Suka amsa da yana ciki malam yace don haka a kwashe mashi tunda yana da hakki anya Jafaru bai yafe kudin nan ba kuwa ?
Anty baraka ke fadin malamin ya sake fadin babu zancen yafiya a nan tunda ya gada shima dole a bashi hakkinsa ai.
Sai kuma wanan nawa saina yazid daya mika hannu zai kwasa mama tace kada ka dauki na yazid habu ka barshi za aci gaba da juya mashi kafin Allah ya dawo dashi lafiya ya karba mama ke fadin hakan.
Kallonta Habu yayi a cikin mamaki kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru ya kasa furta komai daga can Salima take fadin amma yaya Yazid yace abawa J nasa kason ya rike mashi a hannusa idan an raba ai.
Nina haifi yazid ba wani ya haifa min shi ba don haka nina san yadda zanyi dasu a wajena ta fada fuska daure habu ya ciro kudi daga Aljihunshi yana fadin wanan na maine J yace a baku ai maku godiya.
Ya hada kudinshi zai fita yaji salima tace yaya Habu kada ka fita kudina nace a ba ya j ya aje a hannunsa fa ?
Ba zan bashi ba akwai wanda zan ba a cigaba da juya maku kudin nan mama ta fada a tsawace ga salima din.
Dakata hjy malamin da zai fita falon a karshe ya fada yace wanan hakine fa yarinyar nan yanzu ba yarinya karama bace don ko wace ta mallaki hankalin kanta a yanzu.
Don haka yau ko cewa tayi ita zata rike abinta a hannunta za a iya danka mata dukiyanta don ita ta gaji abinta daga mahaifinta.
Kawu ya hade wasu yawu yana gyara haban babban rigansa sai aikawa malamin harara yakeyi daga inda yake zaune ganin malam ya tsaya jawo dogon aya yasashi magana.
Malam ina ganin kunyi abinda ya dace yanzu ai kowa yasan hakkinsa kamar yadda suka bukata don haka abarsu suyi shawara da uwarsu kuma.
Ni wallahi ba wani shawaran da zanyi ya habu ka dauki kudina kaba yaya J na fada mai abinda nake sonyi dasu nan gaba.
Salima zan safa maki fa ina fadin magana kina musayawa mama nace abu zan saya dasu idan sun kara yawa kuma har na nuna mashi abin ya sani .
Habu ya dawo ya tsaya gaban kudin yace baraka kwashi naki ke saratu ki dauka a ban na salima din tunda abu take son saya da kudin.
Idan abin bana amfani bane na tabbatar da J ba zai yarda ba baraka ta kwasa sai saratu ya duka ya dauki kudin Salima din ya fita dasu zuwa part dinshi.
Ranan Salima tasha fada sosai wajen mama Allah ya gyara batayi maya baki ba duk abin nan anyishi iya bata wajen don kamar an kadata fita unguwa tabi J ya sauketa gidan wani dan uwanta dubiya.
Yanzu yaya kaga yadda abu ya kaya kuma yaran nan kamar abin hadin baki kudin nan daga nawa saina Yazid koshi don bai nan,ne .
Nasan da haka za ayi shima karban abinsa zaiyi sai na saratu itama naga take taken ta tun kan a raba take fadin sana,a zata fara tunda karatun yakiya gareta ko Allah zaisa mata hannu.
Ni yanzu ai lissafin ya tsaya min saidai a kawo mu gwada ko zasu fara daukuwa a garemu hakana bai bar gidan ba ranan saida ya karbe kudin mama da yazid din.
Dana saratu da mama ta raba biyu ta boye rabi ta mikawa kawu sauran ya daure leda ya tafi yana mata sallama kada iya ta dawo ta sameshi .
Zance ya lalace yasan ko wanan rabonsane shiyasa yayi dabaran daya izata zuwa gidan dan uwan nata a ranan ayi a kare bata nan.
Habu ne bayan fitansu ya dawo raka malaman yake waya da j yana fadin gaskiya j akwai abinda yake damun mama gaskiya.
A nan dai ya kwashe komai daya faru wajen ya fada mai murmushi j din yayi yana fadin ba komai matsalanta a yanzu kawune.
Iya ta fada min dazun a hanya cewa kawu shiya matsa a fito da kudin nan a raba don kawai wata bukatanshi.
Dama ina hasashen hakan daga kawu mutumin nan ya kamata mu nuna mashi musan nufisa akan mu yanzu.
No kada ka soma ba yanzu ba Habu idan kayi hakan ranka zai bacine da mama don haka ka kyaleshi har gaba.
Chapter 126 · 0% Book details