Sashe 143
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
fadin saratu why zaki barta da yunwa don Allah meyasa kike hakane saboda Allah ? Idan wa yancan basu da hankali ko basu san zafin iya ba saratu ke baki sani bane ashe da gaskiya da ake fadin halaiyarsu kike amfani dashi ?. Yaya kafa san hali iya da surfa komai akai mata ba ai mata daidai ba ni shiyasa na kyaleta baki kyauta ba wallahi ya fada cikin daure fuska ya juya yana tsuki ya fita. Part dinsa ya nufa suna falo dukkan su a lokacin falon dai kamar kullum kaca kaca dashi Asmau ta amsa mashi sallama tana mashi sannu da zuwa. Ya amsa yana tambayanta ya suke da yaran ya dan raba ido ko zaiga yaran bai gansu ba yake tambaya yaran fa tace suna part din habu ina ji. Ok bakima tabbatar dako suna can ba ke nan ina zasu yaya banda can tunda get a rufe yake yaja tsuki ya nufi hanyar dakinshi kai tsaye. Saiban taja tsuki tana magana kasa kasa har yasa key ya bude dakin ya dawo baya yana fadin me kike nema a gidan nan ? Ki koma inda kika fito kinji na fada maki in a serious voice yake magana don bai nuna wasa ko sanya ba akanta fuskansa a daure. Ai saika bari mama ta dawo kaji abinda nakeyi don ita taje ta daukoni har gidan mu Ok zaman mama kikeyi ke nan to ki zauna zamanta din idan hakan yayi maki ya juya ya shige. Asmau ta kalleta tace kema da son rigima kike wallahi Saiba meya kaiki yi mashi tsuki don Allah ta juyo a hasale bayan ta mike tana fadin . Wa,azi zaki min kome ina ruwanki da zancen mu banda munafunci sai Asmaun tace a,a meko ruwana a ciki Saiba ni gaskiya na fada maki kibi abin nan a sannu fadan da yafi karfin ka sai ido ? ZAMFARA Tunda komai ya fito fili yanzu ba zancen boyo a wajen mijin anty baraka kuma ya fito fili yana soyewa da bazawaranshi da ake shirin daura masu aure. Ranan yarta tazo ta fada mata wallahi ga baba can na gani tsaye da Safiya kofan gidansu da leda suna hira duk da hararan da yaiwa yar saida ta fada data shigo gidan. Zuciya ya dibi barakan ta mike ta yafa hijab ta samesu a kofan gidan tundaga nisa ta hangoshi ya turo hula gaban goshi kafanshi daya yana ta cikin zauren gidan daya kuma yana ta waje ya dafa bangon kyauren na gidan. Yayinda bazawaran nasa ke tsaye daga ciki kadan amma ana hangenta waje ta karaso tana huci sai jin muryanta sukayi tana fadin. Macuci azzalumi Allah ya tona maku asiri kaida yar iskan taka yau ya juyo yana fadin baraka hauka kikayi ko me da zaki biyoni nan da rana tsaka haka ? Ba hauka nayi ba daga turu na fito ke kuma macuciya mai laluben ramin labewa ahir dinki da mijina wallahi don ba wajenki a gidan mu. Dakata baraka ki gyara zancen ki kice mijin mu don ya biya sadakina tuntuni in baki sani ba ki sani bakinki ya saba da fasin mijin mu a yanzu. Sadaki ko yaudara kudi garesa balle ya biya sadakinki dashi kudin nawa daya yaudareni yayi min dadin baki ya kawo maki wai sadaki ? Masha Allahu in hakane kema kin samu lada ashe tunda kin taimaka za a raya sunnan ma,akin Allah da kudin ki kai nayi maki murna gaskiya. Ke sakarai wa zakiwa dadin baki a baya badon baida kudin kika kisa ba sai yanzu an samu kudin banza za a dauko min wahala. Ke baraka ki koma gida tun kan ranki ya baci dani wajen nan don zanci maki mutunci fiye da tsamanin ki wallahi mijin nata ke fadan hakan cikin karfin hali ganin jama,a sun fara taruwa masu. Nan dai aka taru aka fara bata hakkuri da ban baki data koma gida tayi hakkuri har ya dawo gida hakan ba mutuncinta bane gaskiya. Dole dai ta hakkura ta koma gida din cikin hasala da mijin da bazawaran tashi tana zage zage kamar mahaukaciya da yawa sun san wanan aure za a daiyi ne amma safiyama bata da halin kwarai. Zata dai bata masu zamane kawai shida matarsa da suke zaman rufin asiri a tsakaninsu shekara da shekaru ba a jinsu ansan itace yan uwanta ke taimakonta take rike da gidan tunda shi ankoresa aiki tunda yayi siyansa dake kalubalanta ta gwaunati aka sallameshi aikinsa yake zaune gida. Yayinda wasu kuma suke jin haushin abinda safiya din tayi don me zata biyoshi har waje tana mashi tonon asiri haka a gaban jama,a ?