← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 242 OF 306

Sashe 242

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayi sati hudu a gidan mijin ummah banda dan damuwa da sabo da zama a dakin aure banda wani matsala a gidan kamar yadda na fada a baya. Ganin hakan yasa na kirkiro tafiya Abuja na samu ummah da zancen take fadin anya daddy ku zai yarda da hakan kuwa ? Ace kina nan mun barki zuwa kuma abuja amma zan fada mai naji ko zai yarda da hakan idan ya shigo yanzu ya tafi rigasa wajen abokinshi. Ina kwance dakinta da yamma sai gashi har dakin ya shigo ya sameni tare da ummah yana saye da coffe colour din jallabiya mai dogon hannu a jikinshi. Saida yakai zaune saman kujera ya soma fadin diyata maman ke fada min kina son ki karasa Abuja ? Nace ko anyi maki wani abune a nan din da sauri na dago kai na dubi ummah kafin na girgiza kai ina fadin ba komai daddy . Kawai dai ina son inje can din ne kawai nagansu sai ya gyara mike kafanshi yana fadin ayi haka kuma Rahama ? Bayan mijinki da yan uwansa sunsan ki wajen mu yanzu kuma suji cewa kin koma Abuja yaya kike son su dauki zancen a zuciyarsu ? Sai na sake kasa da kaina na dukar yacigaba da fadin kinga hakan ba zai masu dadi ba don hakan na nufin cewa mu nan mun gaza dake hakan ke nufin da sauri na kara dago kai na dubeshi yayi murmushi yana fadin yes idan mun barki zuwa abuja hakane zancen. Ba zani ba daddy na fasa yace good girl Allah yayi maki albarka kinji kiyi hakkuri har ki koma dakinki saiki tafi da bakin mijinki daga can na amsa mashi da toh kawai. Ya dan min nasiha nayi hakkuri don Allah na saki jiki kuma tunda nasan a yanzu bani kadai banr a jikina yasan kuma bada jimawa ba mijina zaizo mu koma. Ya dan jima nayi mai godiya ya mike ya fita daga dakin ummah tabi bayanshi suka fice a hankali na sauke ajiyan zuciya na koma na kwanta ina tunane. Sammako kawu ya bugo masu a gidan duk dai akan ya samu yazid din a gida a gaban mama don kada ya fita suyi sabani donshi yafi bukatan ayi komai a gaban mama din don ya hango rashin mutunci a idon yaron . Kamar kullum saida mama tasa yan matanta sukai mashi abin karyawa yanayi yana tambayan kada Yazid ya fita fa dubu gara a aika a fada mai ana nemashi. Kada yazo ya fice daga gidan ba tare da sun sani ba kuma yazo daga baya ya bishi gida yayi mai cin mutumci har wasu suci. Da mama dubu taga ya matsa yasa ta tayar da salima akan taje part dinsa ta kira matashi suna nemanshi ita da kawunsu. Salima taje ta samu har lokacjn basu bude part dinsu ba don yana ciki hakan yasa ta dawo ta fadawa mahaifiyar nasu cewa basu tashi daga barcin ba. Karfe nawa yanzu kije ki kwankwasa masu kofa ya bude muna son ganinsa a nan hakan yasa ta koma ta kwankwasa kofan . Suna zaune suna karyawa a falon nasu sukaji nocking matarshi ta mike ta bude kofan kamar kullum fuskanta yana a daure kamar yadda suke kiranta da mai dauraren fuska haka suka gaisa a tsatsaye da ita . Gashi kuma tana tsaye ta tare kofa alaman bata son ta shigo daga ciki fuska a daure donshi suke kiranta mai dauraren fuska bata da saki ko kadan. Dan uwanta ta tambaya take fadin yana ciki hakan yasa tayi kokarin kutsawa taja gefe ta bata hanya tashiga gaisawa sukayi take fada mai mahaufiyarsu da kawu ke nemanshi . Yake fadin yazo ke nan kice ina zuwa daga haka ta juya ta fice duk da kayan dadin dake zube a gabanshi yana ci da ace marainintane datace wanan fa yaya ? Shikuma jafar zaice zoki zauna kice kodama batayi magana ba idan ta shigo hakan zaice da ita bissimillah salima zauna mu karya. Haka ta juya tana kunduma masu zagi tana fadin yaya J duk yafisu mutunci yan iska masu tsoron matayensu kawai ? Ta koma ta shedawa mama cewa yana tafe tashige dakin kwanansu ta bar falon a lokacin iya na can tare da Jafar a part din da suke jinyarsa don maman tudu tayi tafiyanta gida tabarta dashi. Saida Yazid ya gama karyawa ya shigo part din dauke da dansa a hannunsa ya gaisa dasu ya samu waje ya zauna yana fadin fuskatan mahaifiyarsu yace. Salima tace kina nemana mama kafin ya kaiga rufe baki uwar tace ehh ga kawun ku nan yazo akan zancen kudin daka sameshi gidansa. Ok kudin ya kawo ke nan yazid din ya fada yana gyarawa dansa dake gefenshi zama ya kyalla ido a gefensu ko zaiga kudin sai dai baiga komai ba yasa ya fuskanci uwar dake magana. Kaida kaje gunsa da zancen kudi kaika bashi kudin da zaka sameshi kai tsaye don rashin kunya ? Amma ai mama kudinane ko hakkina don naje na sameshi ai ba zai zama laifi ba ko gyara zama kawu yayi yana kallon yazid din cikin mamaki. Eeh lallai yazid ni kake fadawa kudinkane ko yanzu da sauri yace haba mama kudinane fa hakkinane na tambaya ba wani abu ba idan yazo da kudinne sai aban su mana shike nan don Allah ? To baizo dasu ba mara kunya ko kuma radhin kunya zaka kawo muna yanzu tunda hakkinkane ta yaya an mayar da abu kaddara zakazo da rana tsaka kace kana bukatansu a yanzu. Mama ko kaddaranne a nuna min insan yarda na juyasu zuwa kudi don ina da bukatan kudi a yanzu ni banja ba bance aban na kowa ba nawa nake maganan abina a yanzu. Kai Yazid kagane ko kudin tun lokacin data bansu nayi dabaran sakasu a kaddara na sai filaye da gidajen kango sai a sayar a kara sayen wasu a jingine haka nayi da kudin. Ok to a kaini filin sai na saka nawa a kasuwa don kudi nake da bukata akwai kayan danayo oda zasu shigo min zuwa wasu sati insha Allah. Kai habu na fadama ka shiga hankalinka ba zancen kudin nan a yanzu sai ranan da kawu ya sayar ya kawo maka kudinka idan lokacin hakan yayi. Mama kudin nan kudinane hakkina da Allah ya wajabta a gareni ba don haka ina bukatan abina a yanzu ko hannun wa suke kuwa ? Kawu ina son kudina nan da sati daya kacal kudi ko kaddara a ban abina don ina da bukata akansu yanzu. Yazid ni kake mussu dani mama ta fada ya mike tsaye yana fadin Allah ya kara lafiya da nisan kwana mama ni na isa inyi mussu dake kudina nake bukata kuma shina fada nan da sati nake da bukatansu. In kuma har aka wuce sati gaskiya za,a samu matsala a tsakani gaskiya don kudina ba zasu wuce wanan rana ba in sha Allah. Yasa kai ya fice daga part din kallon juna sukayi tsakaninsu kawu ke fadin kingani ba Dubu aina fada maki kamar yasha wani abu daya zo min gashi kuma ya maimaita agabanki kuma. Ai kuwa bai isa ba yaya don na kula bayin kanshi bane don na fahinci an zugo yaron nan ne mai zaiyi da kudi a yanzu hannunshi ? Tunda kaf komai na dan uwansu yanzu hannunsu yake suke juya mai komai tunda ya kwanta din nan dole akwai wanda ke zugashi yayi wanan abin haka . Mama fa saare data dade tsaye kofan daki ta saurarensu tun shigowan Yazid takara fada hakan yasa uwar ta juyo a hasale tana fadin meye ke kuma ko kema zancen kudinne zaki tayar min da hankali kuma ? Mama in tayar maki da hankali kuma kawai dai nima zance idan za a sayar da kaddarorin a hada nawa don na fada maki ina son in fara sana,an kayan kitchen ne irin na Fatiq . Lokaci guda kawu ya debe hulan kanshi yanawa kansa fitara a hankali ga zufa daya tartso mashi a goshinsa salima tana kallon ikon Allah don ita kadai ta fahinci halin da kawu din yake ciki. Jin yadda Mama din suke fafatawa da saratu yasa ya samu da kyat bakinsa ya budu yana fadin dubu barinje sai dai kinjini kuma. To yaya har zaka tafi kyale yaran nan kada ka daga hankalinka ga zancen nan don Allah rashin hankaline irin tasu kawai sukeyi. Ya dai samu ya fice daga gidan amma hankalinshi ba a kwance ba don yasan akwai magana yau ko kaddaran da yake fadan ya saye baisan inda zaikai Yazid din ba. Hana rantsuwa dai akwai wani fili daya saya amma karamine da niyar ya gina nasa gidan na kansa su tare ciki da iyalinsa don wanan din da suke ciki ya tsufa sosai gashi kuma nagadone da yan uwansu dake jahar Naije zaune saukin abin basu taba bin ta kan gidan ba tun bayan rasuwan tsohonsu da aka dan samu matsala saboda makwabta sun sheda kudin iya yafi yawa a gidan nasu dasuka gina lokacin. Hakan yasa suka fitar da ransu ga wanan gidan harma da yan uwan nasu sai Jafarne ma yake yawan maganan cewa zai kaisu wajen yan uwan nasu shi kuma jiki yaki lafiya a yanzu. Su din kuma ba wai damuwa da zuwan sukayi ba don kawu ya tsorata mama din akan bin yan uwan nasu yace su din matsafane zasu iya tsafesu. Iya kance komai tsafinsu kawu yafisu tsafi ai don zuciyarshi bata da kai zai iyayiwa koma waye mugunta akan abin duniya idan ff,za,ff,fafamfaaftana masu wraffada kalaminta ke nan ga dan nata. Kwantar da hankalina da nayi yasa nayi fresh dani nayi kyau farina ya fito fili da kyau idan kika dubeni sai kin koma ina zaune a falon ummah nida saudatu mun na kallo da rana. Ummah ta shigo falon ta zauna tana fadin Yanda ta kiraki na dago na dubeta kafin na bata amsa da a,a take fadin munyi waya dazun take fada min cewa. Mijikin yanzy ya koma abin tausayi duk ya kara lalacewa ya rame halama kamar ciwonsa nason ya dawo mashi saboda rashin kullan da bai samu yanzu sosai dama kece dai karfin jinyan nasa ai ? Kaina kawar na mayar a tv ba tare danace
Chapter 242 · 0% Book details