Sashe 9
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallaman mama Dubu yayi daidai da jefo plate din shimkafan da Saiba tayi ya fado saman hijjab din jikinta kafin ya gangara ya sauka kasa daidai kafanta ya tsaya. A hankali mama tabi plate din da kallo haka kuma take kallon yadda sauran shimkafan dayake gangarowa daga saman jikinta zuwa kasa. Kaita girgiza ta dago ta saukewa Nusaiba kafin ta mayar kan Asmau data dafe baki cikin tsoro da firgici kai ta sada kasa tana mai tsananin jin kunyar uwar mijin nasu. Da kyat mama ta iya budan baki tace yaran nan har abin yakai haka a gareku daga haka ta juya don bari part din taga hjy Iya a tsaye itama cikin takaici take kallonsu. Gara dai da kuka gwada ga uwarku yau tunda ni kun raina min arzikina mata kamar dabbobi kullum fada dan abu kadan fada kamar karnuka. Akanku aka fara zaman kishine wai in ba auro mata ana haihuwan ku kun mayar da gidan yaro gidan yan tasha gidan dambe . Badon makwabta na tsoron jidalina ba da yanzu gidan nan ya cika da yan kallo tunda kun zama mutanen bamza. Kishi haukane wai mijin ku yana wajen nemawa kansa rufin asiri ku kuna nan kuna tona masa asiri a cinkin unguwa sai yaushe zaku bar wanan bakin kishin nakune wai ? A hankali mama da ranta yake bace ta zagaya Iya tani dake masifa ta karasa ficewa daga part din zuwa nasu wajen kokarin cire hijjab dinta da suka bata takeyi kada ya lalace ban daki ta nufa taja bucket ta jikashi tare da yayafa omo ta barshi a jiki. Fita tayi waje don bata zauna ba kayanta dake can ta waje ta shiga kwasowa zuwa cikin falon mahaifiyar ta din a daidai lokacin Iyan tani ta kara fada ta juyo zuwa wajensu rai bace. Ta samu mama na kokarin zuge zip din dan jakar kayanta data dauko wanda zatai dan kwana biyu dashi a nan zani ta dauko daga ciki tana sauyawa. Wuri ta samu ta zauna iyace ta soma magana tana fadin yau naga yaran banza a gidan nan yara kamar tashin gareji ace babu wanda zakaiwa fada yaji. Sallaman Asmauce data shigo tana sune kai hannunta dauke da cooler abinci tazo ta dire a gaban mama a daidai lokacin kuma itama Nusaiban ta shigo da ruwan data surka da postard cleak ya rine a cikin jug ta aje gaban mama din cikin girmamawa. A,a ku dauki abinku ni a koshe nake daga gidan mijina nafito yanzu koda bai raye bayansa basu barmu a cikin yunwa ba Alhamdullahi nagode. Zaune Asmau takai tana dan dukar dakai Allah ya gani tasan mama mace ce mai kawaici da kawar da kai daga abinda sukeyi bata kulawa koda ance ga abinda sukeyi a kullum nasihanta dasu shine su zauna lafiya suba mijinsu farin ciki ga nemansa. Fitansu koma bayansane ga harkokinsu tasan zaman kaunace ya hadasu da danta don haka suma dul biyun tana kaunarsu tunda dantane ya daukosu ya kawo matasu amana a cikinsu. Yau sai gashi iya shegensu yakai har plate din abincin danta suka watsa mata saman jiki ya watse a tufafinta ita yanzu me zatace da boyar Allah nan mace mai zurfin tunane da kawar da kai irin mama. Kaita kara sadawa kasa ta soma magana mama don,,,,,, Asmau jeki kawai kuci gaba kada ku bari zaman nan dai ina son ku sanin na bautan Allah kuyi akwai hakki da amana a tsakanin mu daku da mijinku dake can yana neman abin rufin asirin mu. Idan kun zauna lafiya kuji dadin hakan idan kuma kunki kome ya biyo bayan hakan kuka da kanku kada ku kuka da wanin mu nan Allah ya gani munyi iyakar yinmu akan ku kun kasa kwantar da hankalinku ku daina wanan shashancin kishin a tsakanin ku. Sauran mata da suke zaune da kishiyoyi ake ganin kamar zaman lafiyane a tsakaninsu kokari suke suna danne kishinsu a idon jama,a kowa da kuke ganin yana zaune lafiya danne abin yake kasan ransa shin ku ba zaku iya hakan ba don Allah. Mama wanan yarinyar yar rainin wayauce waini Asmau zata zubawa abinci a plate a kawo min don ta raina min wayau kome Saiba ke fadan hakan ga mama. Hannu mama din ta kara daga mata tana fadin ban tambayi ba,asiba don Allah komai mutum yayi kansa yaiwa ina dai son ku sani ba a wullakanta abinci a zauna lafiya. Wanan shine maganata dukkan ku nan ba zance bakusan abinda nake nufi ba tunda kowacen ku uwarta tana da kishiya a gida. Mama bani wullakanta abinci wullakancintane kawai ya mota innice nace ta ban abinci cewa take naje cikin tukunya in daba shin laifine ni har na zuba mata a plate mama ? Amma dai kinsan niba wullakantata bace da zaki ban abinci a cikin plate kamar nazo bara a wajen ki kema kinsan nafi karfin hakan wallahi. Yanzu dai sai kuyi ai garara ku nunawa uwar naku halinda kuke kwana kuke tashi dashi a cikin gidan nan ta gani ksllon Iya din mama Dubu tayi tana fadin mama kin hada kayan na soma wankewa ? Don dama duk aka kwana biyu mama tana zuwa gidan ta gyarawa mahaifiyarta waje tayi mata wanki da sauran gyaran waje sai idan yan matanta sun dawo hutu suna gari suke dauke mata hakan. A cikin matan Jafar din babu wace zatace bari ta dan gyarowa Iya part din ta matukar basu din bane sukazo sukayi wurin zai koma fes. Ganin mama din ta fita batunsu yasa Saiba fita cikin hasala tabar Asmau nan saida zata mike take kara fadin mama kiyi hakkuri don Allah. Jeki Asmau a kula don Allah kece dai babba a gidan nan kanninku da abinda kukeyi sukr koyi don Allah Asmau arika tausan zuciya idan rai ya baci. Fita tayi tana tunanen irin halin mama dubu na sanyi hali macece datake rike girmanta da kawar da ido akan duk abinda ke faruwa danta dasu iyakarta nasihan da zaiwa mutum amfani gaba idan yabi. Saidai ko tayi kokarin bin nasihan da ake mata hakan bai samuwa don Nusaiba taza fito da sabon fitinan da sai tabiye mata sunyi fitina. Ita wanan tana da dama sosai fiye da wacan fitsarariyar da tafita duk wani fitina daga wanan nusaiban yake fitowa a gidan nan Iyace ke wanan maganan bayan fitansu. Taron yarane kurciya shike rudinsu a wanan lokacin wanda sukeyi a kansa yana can baima san suna yiba zasu zauna su halaka kansu haka a banza kan namiji. Wata rana ko ance suyi hakan ba zasuyi ba ai don girma yazo a lokacin saidai su koma kishin mumuke wanda yafi wanan da sukeyi zafi. Mamace take fadan hakan ta mike ta dauko tsintsiya don ta fara gyaran dakin Iya din da yayi kaca kace ga kura ko ina a falon har makewayin data shiga yana bukatan gyara idan zai samu. Komai a wajen taron nan yana gudana daidai sun fara hasko wa duniya abindake wakana wanda hakan yasa hankalinsu daukuwa da aikin don abune da yake son natsuwa don kada a samu kuskure. Sallah ya tayar dashi da yunwan da yakeji ya fito daga cikin motar tasu mai na,ura zuwa lokacin wajen taron ya cika makil da jama,a tare da Sahabi suka nufi masalacin sukai ibada ya jima kafin suka fito tare da dan zaga wajen suna kallon irin baiwan ni,iman da Allah ya shimfidawa yan Africa. Malam Habu zokaga kayan nono a wajen nan Sahabi ya fada ya doshi wani hanya dashi yana biye dashi a bayansa koreni gasu nan birjit iya ganin mutum da matan fulani dake ta kaida komo a wajen. Sahabi din ya tsaya yana taya wani kwaryan nono hakan yasa Abubakar ya fara raraban ido yana bin ko ina na wajen da kallo direct ya nufi wajen wasu da suka tsabtace nasu da komai a cikin tsabta gwanin ban shawa . Malam zoka saya baida tsami ko karni lafiyanyyen nonoce tatsin yau din nan muryan wata bafulatana ke fadan hakan ya karasa gabansu cikin mamakin jin yadda take hausanta na yan Nageria sak a bakinta. Sahabine ya karaso yana fadin aina fadama sai inda kallonka ya kare a wajen nan yaji matar fulani din na fadin wanan na shanune wanan kuma na rakumi ga wananshi da akecewa wara da wani hausan nonoce sahihi ake dafawa ya hade haka. Sai wanan kuma cikwai ce mai dadi baida mixed a cikinsa zakaso ka kara idan kayi amfani da kayan don babu algus a cikinsa ko wani mixed . Kai amma ke yar Nageria ce ko sahabi ya tambaya tace meka gani tana murmushi a fuskanta. Kafin tace dashi daga dai can muke ta fada tana juyawa da alaman neman wani takeyi alokacin a cikin harshen fulatanci take kwalawa wata kira da YANDA yanda yanda tana mata hannu tazo. Sai ga wata doguwar yar matashiyar budurwa ta juyo wace aka kira da Yanda din takaraso zuwa wajen matar tana mata fulatanci. Ido ya kafe ta dashi yana kallon yadsa ta karaso tanawa matar magana acikin yanayinta. Yayi da Abubakar yake tsaye yana kallonta cikin mamaki yana fahintar me take kokarin fadawa yarinyar. Daidai lokacin kuma Sahibi ya juya harshe a cikin turanci yake fadin ko ya saye yana da wuya yakai gida bai lalace ba iyakarsa idan a nan zaiyi amfani dashi kawai. Sai sukaji muryan matashiyar na basu amsa da fadin ku saya daga nan har sati biyu baya komai koda ba a saka a cikin fridge ba. Kayan mu suna dakyau da inganci bawai ina yabo bane don kusaya ko don na cuce ku saboda nasan zakuso shi ko nan gaba. Ta kara fada a cikin turanci da alaman gajiya karara a fuskanta lokacin tana dan kakabe kuran dake taba koren nasu da wani dan gashin dake hannunta na dabba da akaiwa ado da duwatsu . Tsaye sukayi galala suna binta da kallo tare da tambayan wai dama kuna jin turanci haka ashe da zaginku mukayi shike nan kunjimu. Ta dan kai zaune tare dan murmusa tana fadin kadan kadan ba balle nasan ba kuyi kama da wayanda zasu zagemu ba ai. Dagajin hausan mamanku na gane ku mazauna Nageriane don hausanta daban da wanda kukeyi a kasan nan. Eh daga can muke koma ince a can