← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 204 OF 306

Sashe 204

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da zafinsa ya dawo kasan ba irin bakuntan nan wai ya dade baya gida din nan sam shi baiyi hakan ba da ganinsama karatu ya hudashi sosai magana kadan zaice Allah yace Annabi yace yanzune zai katse mutum shi ba ruwanshi. Iyaka dasu gaisu idan sun shigo ban dogon motsi ballema yasan dani a gidan har kishiyoyina duk sun kama kansu dashi suma. Kannesu ma sun kama balle mu din yana da kwana biyu da zuwa yayiwa Saratu tas a gaban kowa yake fadin tayi hankali yana da labarin komai akanta fa don haka ta shiga taitayinta dashi. Akan zancen abincine da yace matarshi bata cin tuwo kada a kawo masu sai saratu din tace ita din yar gidan uban waye ta tashi ta girka mana da kanta ita tuwo mama tace tayi shi kuma zatayi ta dafa ta kai masu.. Shine ya biyota har part din da abincin ya kwashi fadanshi yace kuma ta tashi ta girka masu wani a cikin lokaci dole ta tashi ta dafa masu din kamar yadda yace din. Ta kuma kawo bai kyaleta ba nan ya hau fada yana fadin zaman me sukeyi a gida haka tsawon lokacin basuyi aure ba sai shiga maganan manya da takeyi tana hada mutane fada. Hakan yasa zuwansa yai min dadi don kwana biyu bakijin motsin yar iska don kamar bata gidan ma zakice saboda ta natsu sosai a yanzu saina gane ba shiri a tsakaninsu kenan ashe ? Ranan dayayi wani shigo ya samu ina gyaran part din nagaidashi da wuni nacigaba da aikina ina jin yana tambayan mama wai ni kadaice ke jinyar dan uwansu. Mama ta nisa tana fadin kaidai fadi dan nan aini abin yafi karfin ganina yanzu nan dai ta zauna tana koro mashi labarin abubuwa da suka faru da farko. Sai kada kai yake faman yi yana acting a cikin mama kafin ya dan gyara zama yana fadi yanzu da wanan halin yake zaune dasu mama ? Tayi dan murmushi tana fadin to yaya zaiyi Yazid tunda mamanku tana hanashi daukan mataki yayi wani shu,umin murmushi ya gyara zamanshi yana fadin. Wanan Asmau tafi ban mamaki har da ita cikin wanan shirmen waiko tsoron kawar nata take ji da har ta yarda ta aure mata miji ? To za,ace dama dai ita din za ace tunda yanzu bata yarda da iskancin wanan dayan da suka hada kai da saratu suke iskanci ni in anbarni sai ince duk asiri tayi masu da basu ganin laifinta. Na rasa me Jafar ya gani a jikin yarinyar nan tun farko daya leke mata a lokacin sam zuciyana bai yarda da wanan yarinyar ba dama. Shigowan iya tare da matan kawu part din ya katse masu hiransu dashi sun gaisa da mama yana zaune ko kallonsu baiyi ba sai mama hafsatuce cikin karfin hali take fadin sannu yazidu anzo lafiya kwanaki munzo gaisheku da zuwa bamu sameku ba ance kunje bauchi kaida habu ? Ehh ai gara da baku sameni ba ko yanzun ma ba zaki taba samuna ba kiyo sabon shirinkine kikazo kaina kuma ? Basu mama ba harni dake shirin shigewa daki saidana juyo ina dubansa cikin dakewa ya mike tsaye yana fadin banga dalilin da zaku bar mai mugun nufi tana shigowa nan ba asalima gidan nan gaba daya ya kamata matar nan ta daina shigowa. Wani tsawa mama dubu tayi mai tare da ambatab sunab shi tana fadin kai Yazid kanka daya kuwa matar kawun naka kake fadawa wanan magana haka ? Mama don tana matar kawuna ba zan fadi gaskiya a kanta ba matar dake da mugun nufi akan mu kun sani kuma kuka barta tana shigo maku gida haka ? Ko Allah yace mu nisanci makiyan mu idan mun gansu yasa kai ya fita sai hafsatun ta fara salati tana kuka tana fadin . Ni wanan yaron ya kira da muguwa me yake nufi nice na dorawa jafar wanan laluran kome ? Iya ta amsa da fadin ,Yanzu ai gashi can baiyi nisa ba sai kije ki tambayesa ai hansatu mukan ina muka sani tunda bamu shiga zuciyarki mun gani ba ? Ba a gane mugu a goshi amma ana gane gaskiyan kowa a fuska don kowa na nuna shi nagarine ako wani lokaci kuka ta dan fara tana fadin . Zargina akeyi kan Jafaru kome iya haba shiyasa ashe duk nazo gaidashi sai a nuna min ba zan samu ganinsa ba ko ace min yana barci ko kuma ana mashi wani abu ashe ana zarginane da maita ? A,a haaa mukan bamu kiraki da manya ba amma koma meye kin sani ai koda yake shi maita bawai saika kama kurwa bane kake maye ko mugunta ai maitane shima. Da kyat mama ta samu hafsatun ta fita daga part din banyan mama tayi ta bata baki tana tausanta akan koma meye ba yadda take nufi suke nufi da itaba dole akwaidai abinda. Mama dubu dai tana zaune ta kasa cewa komai akan hakan nima ina tsaye daga kofa nakasa shiga dakin da zanyi a lokacin sai bayan fitansune mama din ta mike ta bisu. Iya ke fadin haka kawai yaron nan yayi min daidai daya fito mata fili da mugun nufinta ta dauka ba asan me take ciki bane ta kwaso kafa don bata da kunya zuwa munafunci. Wai iya hafsatun ta hurhurane yanzu maman tudu ke tambayan iya din cikin bacin rai iyan ke fadi ko maita take ai ba a mussu tunda kwadayi kekai mutane ga halaka yanzu. Hakanane fa idan kafaye saka abin duniya a rai sai ka tsunci kanka ga mahalaka yanzu mutane da yawa haka ke faruwa dasu ai mama ta fada ta kare da Allah ya kyauta . Ni dama naso nace bafa kowa ya kamata yana shigowa part din nan ban ganin yaron nan tunda muna ganin sauki a cikin lamarin nan. Yakama ace saina gida sosai zai dinga ganinsa a yanzu mutane basu da kyau kana tufkane ana maka walwala don haka kada kuga laifina a yanzu matakin da zan dauka don shigowa wajensa inma son samune zan daukeshi zuwa wanan dakin da matarshi ke kwana ya koma can din sai wanda aka yarda dashine kadai zai shiga wajensa. Barin shi falon nan hankalina ya daga sosai ina take tazo ta gyara dakin a mayar dashi cikibinyaso mu muyi amfani da dayan dakin shike nan aga abinda Allah zaiyi kuma. Tun wanan ranan aka dauke yaya a falon zuwa dakin wanda hakan yayi min dadi sosai don Allah ya gani zamanshi a falo sam bai min ba dama don ba dama nayi masa wani abin idon tsofin yana kanmu saidai yayi ta faman bin na da kallo duk inda na gilma da idanu. Haka kuma duk wanda yazo iyakansa falo yanzu ba kowane suke yarda ya shiga wajensa ba sai su shakikyansa kadai sukan shiga su jima a ciki wani lokacin tare dashi ni kuma in samu barci koyin wani abin. Na samu daman zama dashi a yanzu nayi maganan da zan mai duk daba amsa min yake iya yiba haka dai zai kafeni da idanuwansa . Bani kadai ba dukkan mu matanshi muna shiga gunshi mu kebe dashi na dan wani lokaci za,a zauna nan tare dashi koda barci yakeyi saina fahinci wanan tsarin na mama bani kadai yaiwa dadi ba ashe yanzu. Abin dana fara kula wata rana ina zaune da dare bayan nagama shafa mashi magani zamu kwanta sai kawai tunane ya dibeni sai kuka na fada jikinsa in kuka a hankali kamar a mafalki naji hannunsa na kadawa a hankali yana dagasu zuwa kaina. Innalillahi na samu ambata tare da katse kukan da nakeyi ina binsa da kallo amma ya kasa abinda yake son yi din don hannun nasa ya kasa daguwa yadda yaso din. Naja bakina nayi shiru daidai a yanzu nakan kama yatsunsa din ina masa massage dinsa har dana kafafu da duk inda jijiyansa suke kafin mu kwanta . Cikin irin haka ranan banyi aune ba su mama tare dasu yaya Habu da sukai tafiya suka shigo suka sameni ina masa hakan. Muryan Yazid ne ke fadin gaskiya wanan kina da fasaha sosai nayi wanan tunanen ince ko za a dinga dan masa hakan sai gashi ashe kina masa hakan zai taimaka sosai wajen karfin jikin insha Allah. Ni dai ganin sun shigo yasa na daina na sakeshi na koma gefe na rakube can dai na mike na dawo falo na samu iya zaune ta idar da sallah muka dan fara hira jefi jefi. Hiran dai bai wuce akan jikan nata ba take tambayana ko biba ta kara shigowa nan nace ninace ta daina zuwa don ranan da sukazo kuka tayi sosai har saida ta kwanta ciwo hakama yar uwarta da sukazo tare wai iskanta ya tashi itama da suka koma gidana a ranan . Ba kaji ba iya ta fada ai duk wanda keda iska yaga jafaru yasan da iska aka hadashi bashi kadai bane don irin yanayin da yake ciki duk mai hankali zai gane hakan. So sukayi suyi mai farat daya Allah bai yarda ba shine suke wahalal dashi haka insha Allahu Allah yafisu yafi sherinsu ai kinga har yau kawun ku ya kasa zuwa gidan nan . Da yasan ba komai aida tuni yazo gidan nan da fada tun ranan yace anwa yar gwal dinsa kazafi yaciwa mutane mutunci haka itama kinga ba wani mataki aida ta dauka ga abinda yaron nan Yazidu yai mata. Nan suka fito suka samemu muna maganan mun dan jima suna zancen kafin su fita muka rufe part din namu yaya ibrahim shike kwana a falo yanzu. Mu kuma muna daga ciki sai daga baya bayan yan gidan su Saiba sun kara zuwa dubanshi sai ga zance ya tashi saiba din taje wajen mama wai suna son a basu hakkinsu suma su dinga kwana dashi kamar yadda nakeyi. Mama dubu din tazowa su mama da iya da zancen iya ranan tayi fada sosai take fadin na kula dubu kema ba lafiyan yaron nan kike soba ? To anki a raba kwanan su mayar muna da jinya baya muna ganin sauki suja muna hasara ba za a yi hakan ba data zauna dashi a baya wata uwar take tsinana masa a lokacin banda sharan barcin ta da takeyi
Chapter 204 · 0% Book details