Sashe 205
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
a nan saman dogon kujera. Dole dai akaci gaba da hakan don dai kada tsegumin yayi yawa na fara komawa gida ko gidan yar uwata in zauna sai dare zan dawo gidan. Ma,ana dai su, su wuni dashi da rana ni kuma in kwana dashi da dare saiya kasance wahala da dawainiya ya fara komawa kan tsofin don su zasuyi ta fama dashi hakana har zuwa lokacin dana dawo. Suko matansa excuse din girki ko kula da yara suke bayarwa abindai ba dadi wallahi don gaskiya bai cancanci haka a garesu ba za ace dai ina fadane kawai don in yaba kaina in bata su gaskiyan zancen ke nan nake fada a yanzu. Burin su a fili yake shine yaya zai mutu su kuma suci gadonshi don takan ce kura da shan bugu gardi da kwatan,kudi. Gara dasu dai kome za ace ace su dai keda riba tunda su suka haifa sune kuma keda Jafar aje ayi ta aikin wahala din don neman yabo . Alkawari nayi insha Allahu ba zan kara biyewa shirmensu ba idan sunayi ko da dangwarana mace zatayi matukar muna cikin wanan halin na rashin lafiyan mijin mu. Gata da wani hali kamar tashin kauye da yawan habaici da sake magana kowa tana iya yiwa hakan abindana fahinta ke nan yasa naba banza ajiyanta yanzu. Ni kadai zan iya cewa ga cigaban da aka samu yanzu kan matsalan nashi saidai ban fadawa kowa hakan ba har maman tudu dake kula dashi din. Don ita mama dubu iyakarta ta shigo ta dubashi inda wani shawaran da zasuyi kuma zasu zauna suyi a kan matsalan iyakartavke nan tunda mama ta nuna ita din uwace gareshi. Ankai yanzu yana dan iya daga hannu tun iya iya motsawa har yakai ya fara dagasu yana dan juyawa saidai ba bakin magana gareshi har lokacin. Anty Salima ko nafisa sai idan sunzo gidan zakiji bakina ko in muna tare da iya wani lokacin tare da salima din mukan fita muje can gidan mu wuni. Ranan ma mun shirya din zamu fita don na kwana biyu ban leka gidan ba yasa nacewa mama din zanje in gyara gidan tace ya kamata shine muka shirya zamu tafi din. Suna falo zaune a lokacin dana fito duk daba wani shigar azo a ganine a jikina ba amma ta dago kai ta kalleni ta kawar da kan nata gefe daya. Tsanar da tayi min take jin yana karuwa a zuciyarta duk zata kalleni takan ji kamar ta daina ganina har abada a duniyan nan don bata kaunan ta bude ido dai ta ganni saboda haushin da takeji nawa din kishi ke nan. Nima dai din ina jin haushin ta saidai baikai nata ba don ma taki zaman lafiya danine ya kawo hakan da zan iya rufe ido in kawar da duk wani kishinta da nake ji a raina. Kishi mukayi da itakata kwashe ranan ta zauna ta kwashe min kaina da tsiya da komai haka na zauna tayi min kitson a kaina sai kusan goma muka dawo gida. Tunda muka shigo da sallama naga irin kallon da mama tayi min nasha jinin jikina tana zaune tana cin abinci muka gaidasu nake tambayan iya tace tana ciki. Na mike zan shiga naji ta kirani tana fadin Rahama ina kuka shiga haka dan Allah keda kike da mara lafiya ki bar gida don gudun bacin ran wasu ba zaki dawo gida da wuri kiga halin da mijinki yake ciki ba ? Yau jikin nasa da zazzabi ya wuni saida likitanshi yazo yai mashi allura ya samu dan barci yayi amai yakai sau uku gashi kin barmu da tabararrun nan a gida sai shirme suke muna sin kasa anyana komai akansa. Da sauri na fada dakin ban tsaya jin karasan zancen ta ba yana kwance yana barci nagaida iya ina karasawa wajensa na dan dafa wuyanshi da hannuna. Zubur ya bude idonsa ya sauke min yana kallona sai kuma ya mayar da idanun nasa ya lumshe a hankali sannu nayi mai na zauna a kusa dashi hakan baisa ya bude idon ba. Sai lokacin muka gaisa da iya dake zaune a kasa tana lazumi take fadin yau jikin nasa ya tabu bayan fitan ki masassara ya kamashi. A hankali nace haka mama ta fada min yanzu amma da sauki ki daina wanan fitan don kawai kina gudun zargi ko wani abu yau ai uwarsa taga amfanin ki don kwasan amaima jidali ya zamawa wavyancan balle kula dashi din kinga ai tun kafin magariba da suka gudu basu leko ba . Duk yadda kikayifa sai an zageki wasu kuma su yabaki ki daure kici jerabawan duk nan mun san dalilin dake saka kina wanan fita din hakan kuma ba wankeki zaiyi daga zargin kishiya ba tunda anki mata yadda take so. Na dan waigeshi yaban tausayi matuka na mike na kwabe kayan jikina dakin da akace yayi ta aman nashiga gyara na tsabtace shi na saka kamshi. Har ban dakin saidana gyaro na koma dayan dakin da suke amfani shima na gyaro masushi likitan ya dawo tare da Yazid sun kara dubashi sai lokacin nasan ya daao garin . Sun dan jima suka fito na samu nashiga wanka na fito na zauna na dan gyara jikina na saka rigan barcina falo na fito na hada mai shayi mai kauri koma dakin. Cikin dabara na samu na tayar dashi na bashi yasha saidai na kula kamar yana fushi ko kuma yanayin ciwone hakana yake damunsa oho ? Saida kafa ya dauke na rufe part din don mama ta fada min ya Ibrahim bai nan yaje Abuja da safe cab zai kwana kuma. Na jima zaune bayan na fafa mashi magani ina mashi addua nakan koma saman kujera in kwanta amma haka kawai nace na kwanta a kusa dashi ranan don yanayin da yake ciki din. Nakai kamar minti goma da kwanciya a gefesa kamar a mafalki naji saukan hannunsa saman jikina saida na dan zabura nayi mamakin jin ya rikeni a ranan. Cikin fargaba nake fadin yaya kaine kuwa ba bakin magana kai kawai ya daga min bai iya ban amsa ba hamdala nayi a zuciyana jin yadda hannunsa ke motsi a jikina din. Sannu a hankali naji abin yana rikida zuwa wani yanayi don ya wuce tsamanina a hankali na runtse idanuwana acikin fargaban abinda zai iya faruwa a lokacin. Ba lakka bane a jikinsa ko wani kuzari don haka na kyashi yana abinda yake tsamani zai iya a lokacin amma ya kasa sai ajiyan zuciya zuwa can kuma bayan mun rugume junane naji saukan hawayenshi a saman jikina.