← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 306

Sashe 137

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Musalin karfe dayan rana Salimace data gama shirin ta tsab ta fito daga dakin kwanan su da yar karamar jakkar hannunta saidai ganin saiba tare da mama yasa ta kasa magana lokacin ta zauna.
Kamar hadin baki saiga mariya ta shigo da abincin ranan data girkawa su mama din ta fara gaidasu iya ke fadin yar albarka yar tofon lada kamar kinsan tun dazun yunwa nake ji wajen nan zaune.
Ruwan shayi da biredi mai zaiyiwa mutum a cikinsa ba wani abu mai nauyi da mutum yaci tun safe malalatan yaran nan sunki su girka abin kwarai da mutum zaici har yayi sauransa yaci da safe ya dora a cikinsa don kiuyan banza irin nasu.
Amma iya ai kinji ina masu fadan dafa dukan da sukayi jiyan nima ba sonsa nake ba amma tace min wai ta zuba ko dole na kyaleta.
Iya bata tankawa mama din ba dake magana tace bude min nan kinji ban iya bude abin nan takecewa maria din data aje abincin gabanta.
Maria ta duka ta bude da sauri iya ta kyalla ido kan abincin tuwon alkaba da miyar danyan kubewa sai manyan nama guda biyar da miyan ja da ya cika kulan miyan bata san lokacin da hannunta ya dafa kan maria din ba tana fadin Allah yai maki albarka yar nan ya kareki daga idon mahassadanki alherin Allah ya bi rayuwan ku har karshen duniya.
Kaji iya da wani zance shi kuma mijinta daya kawo abincin fa mama ke fadan hakan ?
Iyan ta dago tacewa mama din ai kinji jam,i nayi mata ai bance rayuwanta ita kadai ba har kowa nata nake nufi a zancena dubu.
Idan nayi mata kamar habu din nayiwa ai don duk daya suke wajen mu daya kuwa iya mama ta kara fada iya dai tace miko min plas in diba kinji takecewa yanda din.
Ta mike zuwa kitchen da dauko mata plate koshi saidata tsaya ta wanke tas ta fito ta kawowa iya din ta zuba mata duk saiban tana zaune tana kallon abindake faruwa.
Maria din ta mike tana fadin ke kuma gaki da jakka a gabanki mana kamar me tafiya tana cewa salima ?
Kamar kinsan tafiya zanyi zan tafi Abuja yau din nan inje in huta da surutun iya da sauri suka kalleta suna fadin Abuja kuma ?
Tace ehh gidan Rahama zan tafi dazin mukai waya da yaya yace ya wuce can zani na dan zauna da ita kwana biyu kafin ya dawo nan ai lagos ne gidan kwamacala gidan kowa da kowa can ko ai kinga gidan hutawane nayi.
Maria kan tunda ta daga batace komai ba tasa kai ta fita tabarsu nan suna karawa da Salima din da Saiba dake fadin ohh dama nufin ku ke nan ashe gidan hutawane can din.
To bari yayan naki ya dawo muji in hakane kowama ai yana son hutu a rayuwansa wa zaku mayar dan kauye bakauyama kun kaita abuja balle mu yan birni.
Ke Nusaiba fita batun Salima don Allah shirmenta take fadi shi abujan dame yafi lagos din ?
Yafi mana mama Saare ta fada daga gefeb da take kwance ai tunda kikaji Salima ta fada nufin yaya ke nan can ne gidan hutun nasa nan kuma na kwamacala.
Wanan karon kingansa gidan nan sosai kamar yadda ake ganinsa idan yana gari komai dai mutum zaiyi ya tuna da Allah .
Halan Rahama din tafi wanine ko wata kai da za a tsabareta a gefe daya a rabata da yan uwa akaita can mama don bakiga gidan bane fa shiyasa ba zaki gane gaskiya Salima na tafadi ba irin ginan zamani din ban komai tsone a gidan gwanin ban sha,awa.
Kai haba don Allah akan dan uwanki kike fadin wanan maganan haka yar nan iya data cika baki da abinci take fadin hakan ga Saare din.
Ta samu ta hade tana fadin shike nan Allah ya bashi ba zai nuna ba akansa aka fara hakan ina nan kukaso ku tozarta shi kuga inda zai saka yarinyar nan yayi maku bazata akan hakan.
Yanzu kuma kuna son kakaro wani zance salima tace nima iya bada wani manufa na fadi hakan ba wallahi sheri dai nakewa mariya din ita kuma saare tana son maida zancen babba ta mike zata fita da jakkarta mama tace da ita dawo.
Da sauri iya tace ta dawo kamar ya ke jeki Allah ya tsare ki gaida ita sai munzo duk sukai shiru sai Saarece ke fadin toke iya ina ruwan ki ai gara a hanata zuwa din don bata san ciwon kanta ba gidan kanwar bayanta zataje ta tayata zama gototo da ita Rahama sa,artace don Allah ?
Ke ya isa haka don Allah mama ta fada a hasale sai saare din tayi shiru amma mama kin daiji abinda ake fada ko a bayan mu yau shi salima ta fada a gabana ko ?
Don salima ta fada mijinki ya fada maki hakan wai akankune aka fara hakane miji ya raba gida in kubi a sannu indai Jafarune Allah yai masa budi tunda kukaga hakan koku yana da niyar raba maku din mutum ya kasance mai hakkuri koda yaushe ba gagawa ba zancen yaran nan zaki dauka ya wahal dake a karshe to ki zuba mashi ido inkinji ta tawa.
Ta dade zaune kafin ta mike ta fice zuwa part dinsu a hasale take har lokacin tana shiga saiba na zaune tana cin abinci take fadin kinji ni da yar iskan nan Salima ?
Me tayi Asmau ta dago tana tambayanta taja tsuki ta zauna tana fadin wai nan gidan shine gidan kwamacala don haka lagos ne nan can kuma gidan daya kai yar iskan nan shine Abuja gidan hutu.
Dariya Asmau ta kwashe dashi tana fadin kai lalai salima dai yar takalo zancene yayin da nusaiba din kewa Asmau kallon shasha,sha tace wai ke ranki bai baci bane ?
Tace akan me shi kanin miji kana fushi da zancenshine Nusaiba ai lokacin daya gane kana fushi da abinda yake ma lokacin zai kara abinda zai bata ma rai .
Ina ruwan mu da Abuja ko lagos tunda nan ma bamu rasa komai ba nifa kinga raina bai baci da wanan abin bacin raina dayane shine ace shi mijin ya juya muna baya ya fita zancen mu bai kulamu bai damu damu ba amma ni duk wanan abin nasan wata rana kamar mu zata koma itama a dai fara aje yaya ki gani itama tabi layin mu din.
Kafin tabi kina nufin mu zama yan kallo Saiba ta fada tace dama ai haka abin yake kin sani dole in ankawo wata kayi hakkuri don baka zamanin ka kaina wani ni wanan yasa kikaga ban wani damu kaina ba tunda nasan haka abin yake dama .
Ohh Allah hakane ai bansan da cewa ni kadai ke yakina ba gara da kika fadi naji yanzu kai nusaiba ke nan da wani zance kike to ke wanan abinda kikeyi riban me kikaci wajen sa don Allah ?
Ta mike zuwa daki tabar Asmau din data bita da kallo zuwa kurewanta tayi murmushi tasan abin ya taba mata zuciya amma ta godewa Allah data taushi zuciyar nata kan abinda take ji din.
Da badon yan uwanta da iyayyenta da suka tsawata mata ba da haka zata biyewa Saiba din suyi ta hauka ana masu dariya tare miji dai na kowane ba na mutum daya ba don haka kowa tashi dabaran ta fitar dashi a gidan.
Suna isa Abuja direct airport ya nufa dashi don saura kiris jirgi ya tashi yana fitowa daga mota kirana na shigo mashi ya dauka yana fadin.
Amaryata ya kike ?
Saida na sauke ajiyan zuciya na amsa a cikin sanyin murya da lafiya lau yayana yaya hanya yaya ya habu ya amsa da yaya habun ki lafiya lau yake Rahama to ya akayi.
Na dan kashe murya ina fadin ba komai yaya sai dai kewa gidan yayi min shiru ya ba dadi sai naji yace ohh god ko in dawone to ?
Ke Rahama ba zai dawo ba ki koyi zama ke kadai mana ita maria da nake tafiya na barta kin fitane da zaki wani marairaice murya da sauri na kashe wayan na kifa kaina a filo.

ZAINANB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

5️⃣1️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Chapter 137 · 0% Book details