← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 239 OF 306

Sashe 239

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan nace dake ban shiga damuwa ba karyane don dole akwai damuwa da kadaici balle yanzu dana shaku da yaya haka ko yaushe muna tare. Sai naji dan kwanakin da nayi gida ya zama min daban a rayuwata ga wayana na kashe don kadama ya kirani in kulashi. Kusan kwana shidda a gidan ummuh inda na sake raina kamar yadda kowa ke ban shawara ina samu ina barci haka kuma babu aikin komai duk da nakan dan shiga kitchen wani lokaci da Saudatu mai aikinsu. Haka yaran daddy mata su anty Baby su ukku duk sunzo gidan dubani kamar yadda mahaifinsu ya umurcesu dasuyi min din mun zauna na fada masu damuwa ta suka kuma ban goyon baya kamar ta mahaifinsu da inzauna sai sun kawo kansu in kuma sake jikina na kama harkokin gabana kawai ba a sa zancen namiji a zuciya don sai ka lalace a banza. Naga karamci a wajen mutanen nan sai yanzu da zamana ya dawo gidansu na fahinci halinsu ashe ban fahincesu bane da farko mutanene masu halarci da sanin darajan dan adam. Inda ko wacensu take a gidan hutu gwargwadon hali don basu cikin wahala ko talauci kadaram kada ham a rayuwa . Gashi a fahintana suna nuna kamar mu kanninsune na jini haka sai naji kunyar kaina ya kamani a ranan na yadda bamu kullasu duk da suna bin mu amma ya dace ace ai muma muna maida kara a garesu shine mutunci. Ina kwance daki ranan misalin karfe biyar na yamma saiga ummah da wayanta a hannunta ta shigo dakin tana fadin wai barci kikeyine Rahama ? Na dago ina fadin a,a ummah na dai kwantane ta miko min wayan tana fadin mijinki a layi na dago na kalleta nace mi zan mashi kuma ni ina ruwana dashi ummah ? Ki karba saiki fada mai ta fada tana dangwaro min wayan a hannu na da sauri na cabe ina karawa a kunne yana kan layin naga ta juya ta fita daga dakin ta barni da wayan. Na manna a kunnena naji yayi murmushi yana fadin baki san me zaki fada min bama Rahama shiyasa kika kashe wayarki kenan ashe don kada indameki ko kiji muryata ? Shiru nayi ina saurarenshi na sake jin ya furta are with me na amsa da ina jinka mana rai bace cikin wani yanayin murya a daure. Naji ya sake murmushi yana fadin fushin hardani ke nan akeyi da nayi maki me kuma Rahama bawan Allah dake kwance haka har zai iya batawa wani rai don Allah kiyi hakkuri please ? Nace da kai fushi nakeyi ni kawai nagajine da cin mutuncin da akemin kuma a hana mutum ramawa ba a kuma daukan mataki a kansa. Ba gaskiya bane Rahama wanan bai isa hujja a gareki ba nidai abinda zuciyana yaban game dake shine kin gaji da halin da nake cikine a yanzu kawai kike nemawa kanki mafita ? Ohh abinda tunanen ka ya baka ke nan kai to shike nan in haka kake tunane look Rahama idan kin gama hutun ki dawo nima ina bukatanki a nan tare dani kin sani . Ashe zaka zauna zaman jirata kuwa don ba zan dawo wanan gidan da baida saiti ba sai abinda kowa yaga dama yayiwa mutum kuma a hana ka daukan mataki nagaji na hakkura na kashe wayan. A bangarenshi shiru yayi yana tunane yaushi nake fadawa hakan a gabanshi da farko bai yarda ba amma yanzu yaji gaskiya da kunnuwanshi. Maganan mamansu ya zama gaskiya ke nan ba wanan yasani tafiya ba saidai kawai gajiya da halin da yake ciki din da nayi inbashi ba baiga abinda zaisa nace haka ba shima tunda yasan yana iya kokarinsa damu ai. Shigowan mama tudu dakin yasa ya nisa ita ke fadin Jafar yau ina son in koma gida don na shirya zuwa gida in duba yaya da jikinsa dan uwanta da akace hawan jini ya kayar dashi. Ya dago yana fadin mama kema tafiya zakiyi ke nan yanzu muka gama magana da diyarki ai tana a bankanta na cewa ita ba zata dawo gidan nan ba. Ni abin ya daure min kai mama iya kokari inayi da yarinyar nan amma ace Rahama bata ga hakan a kaina ba yanzu. Shiyasa nake tunanen zancen mama gaskiyane da tace kawai dai tagajine take neman hanyan guduwa a yanzu din. A kul dinka Jafar na kara jin wanan zance irin haka a bakinka kai yanzu bakaji kunyan furta wai yarinyar nan ta gajine ba tunda ka fada yanzu a nan nasan zaka iya fadin hakan a gaban kowa Jafaru. Jafar ka tuna iri alherin yarinyar nan a gareka kana a cikin ciwin kama bata yi haka ba sai yanzu da Allah ya kawo maka sauki ana gani ? To mama ni banga abinda nayiwa yarinyar nan bayan wanan da zatace ban mata adalci ba a yanzu wani irin adalci take so a rayuwa kuma ? Ehh lalai Jafar da sauranka sosai wanan yasa har ake ganin damanka dana matanka ashe sam baka tsayawa kayi tunane akan abu ? Yanzu kai ya dace ace kanwaka da mahaifiyarka suna yiwa yarinyar nan cin mutunci kana kallo amma baka tsawata ba sai wani cikin yan uwanka yazo shine zai tsawata masu ? Kaga hakan yayi daidai ke nan a rayuwa don Allah kofa waye akewa hakan a gaban wanda yayi dalilin zuka gidan baka dauki matakin daya dace ace ka dauka ba a matsayinka na mijinta. Kayi tunane wanan dalilin kadai dana baka idan kana da tunane zaka gane gaakiyan yarinyar nan nayin hakan dolene ta kufuleka a zuciyarta. Sanadinka fa take zaune gidan nan yanzu amma irin hakan yana faruwa baka taba daukan matakin daya dace ba kan hakan Jafaru ? Shiru yayi yana sauraren mama din saida ta gama ya nisa yake fadin mama nagode insha Allahu za a gyara dama gudin nayi magana ace banda ta ido . Mama kin fa san halin mama sarai mama banyi bama tace nayi akan Rahama ni ina kyalewane don kada na gogawa Rahama bakin jini amma zan gyara insha Allahu. Daga wajen suka kara tattaunawa da mama din inda a karshe yake fadin saikin dawo zaki dawo nan ke nan mama da sauri take bashi amsa da fadin anya kuwa Jafar ? Shi kuma yace haba mama ki dowo don Allah kinsan zaman ki nan a yanzu yana da amfani sosai a garemu ta dan dago kai tana murmushi take fadin Allah dai ya dawo damu lafiya ya amsa da amin. A ranan ta tafi hakan yasa ya koma zama shiru shi kadai a daki sai idan iya tashigo dakin dayake yakan dan samu abokin hira bata zama kuma take fita. Makin Asmau tayi amfani da wanan daman ta mami mijin nata sai ya kasance a lokacin ita kuma take ikirarin wai aiyuka suna mata yawa saidai ta dan lekoshi ita da yaran ta koma . Hakan yasa ya shiga damuwa mai din bin yawa zaman kadaici ya dinga damunshi a dakin dole yasa zaisa a fito dashi kofan wajen part din ya zauna yana shan iska. Gaahi zuwan Yazid ya hana a dinga tayar da injimin da rana sai idan dare yayi ko zafi yayi yawa tun lokacin da matan yaya Jafar din sukace ai ana cutansu ana cin dukiyan mijinsu ba tare dasu ba don anga yana kwance baisan abinda yakeyi ba su kuma an mayar dasu mata ba a daukesu a bakin komai ba. Yazid a mota ya tsaya bai fito ba ya tura aiwa kawu sallama jin hakan yasa kawu ya fito don yaron ya fada mai wani mai mota ke sallama dashi a waje. Sai gashi ya fito da sauri yana dan waige waige ya hango motar dake tsaye nisa da gaban gidansa kadan ganin hakan yasa Yazid din fitowa daga motan dayazo dashi. A,a Yazid dama kaine ka tura ayi sallama dani baka shiga ba ka tsaya waje ya karaso yana fadin eeh kawu to bussimillah mana mu shiga daga ciki kawu ya fada. A,a kawu aiba wani abu ya kawoni ba nazone akan wani zance shiya kawoni to yazid ai da dai mun dan shiga daga ciki akan ita matar Jafarne daine ko ? Yaran nan basu jin shawara ai shi jafar tunda yazo min da zancen auren yarinyar nan banso ba naso hanashi amma ya nuna min yayi niyar hakan na barshi yayi abinsa ko uwarku bai kaunan ta sani. Dakata kawu ba wanan zance ya kawoni ba ninazo zancen kudinane da mama tace min suna hannun ka ina bukatan kudin a yanzu don ina son na kara jari ga sana,an dana soma. Kudi kuma yazid ita uwar taku tasan da zakazo tambayan kudin ka don ba kudinka bane ta ban balle yanzu kazo tambayana haka kai tsaye ? Ok hakane to zata zo din da kanta har in kudina yana hannunka ka tabbatar da ka bata kafin mu sake haduwa irin haka don ina bukatan kudina a yanzu don Allah. Yana fadan hakan ya juya a fusace ya bar kawu din da mamankishi tsaye yana bin bayanshi da kallon can Allah ya bashi ikon budan baki yake fadin. Waiko yazid kan ka daya kuwa koka fara shan wani abune haka jin hakan yasa Yazid din juyowa a cikin mamaki yake fadin. Yana nuna kanshi yana fadin ni kawu a hayaci nake don ko goro bana ci balle wani maye nayima kama da wanda ke shan wani abu makamancin hakan yanzu ko ? Sai yayi murmushi kafin kawun ya bashi amsa ya juya ya tafi har lokacin kawu din yana tsaye a inda ya barshi har ya tafi. Nisawa yayi ya juya yana wasi wasin a zuciyarshi don yasan bai jima da wanan maganan da dubu ba akan zancen kudin yayi mata maganan da yake ganin hankalinta zai kwanta yadda ya saba . Yanzu kuma kwatsam saiga Yazid yazo da wanan zancen kudin yadda yaga yaron yazo mashi tsatsaye a yau shine abinda ya daga mashi hankali. Yasan inda zai kamo shirinsa ai da uwarsa zaiyi amfani itace logon diyan da ita kawai zai hadashi ya daina wanan zancen. Shiko yazid yana tafe yana faman shirya yadda zai fitowa kawu din tunda ya hango rashin gaskiya tsantsa a idon kawu din zaiko gwada mashi bai
Chapter 239 · 0% Book details