← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 306

Sashe 136

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

GIDAN KAWU
Kawu dauda dake zaune yana lissafin kudi jin motsin matarsa hausatu yasa ya maida filo saman kudin ya taushe saidai yayi shuka a idon makwarwa don hausatu taga abinda yake nufi lokacin.
Jug din furan data dauko wanda yaji nono da sukari tana ajewa ta mike tana fadin malam meye duniya naga tun shigowan kudin nan ka tsiro wani sabon dabi,a a zuciyar ka.
Kana nuna baka son ma inmatso balle insan komai dangane da kudin nan karka manta komai daya faru har kudin nan suka shigo hannunka nice na shiryashi gidan nan ?
Kai ya dago yana fadin yanzu me kuma nace ko nayi hafsatu me nace akan kudin nan dole in kula da dukiyan mutane ai don yaran nan kinsan ba kirkine dasu ba.
Zasu iya hada kai nan gaba su binciko kudinsu a wajena donshine bani son wasa da wanan kudin kike ganin kamar wani abune hakan ?
To yanzu dai ba wanan ba malam ta kai zaune tana fadin kasan dai Allah ne yayi damu zamuci kudin nan muma a gidan nan tunda ya kwatosu ya dawo muna dasu hannun mu.
Katseta yayi da fadin to sai akai yaya ta kara gyara zama tana fadin to shine nakema tuni da yaran nan mardiya da dija kasan dakunan su yana son gyara ko kwashi muje din nan na bakin titi da ake kafawa aka kwasan masu zasuji dadi kasan mazan yanzu basu son ganin daki ba komai sai wullakaci da raini ya shiga tsakanin miji da mata.
Ko wani miji dai a yanzu so yake yaga wurin kwanci gyarare da kuma mace mai dan maiko ba yar bani bani ba kadai san komai basai na fadama ba .
Shi kuma yaron nan sale a samu abinda aka bashi ya huta da yawon tasha din nan da yakeyi idan kayi hakan ni kayi min komai wallahi nasan naci a gida ni in koshi tunda kai naga ba irin mazan zamanin nan bane da suke son ganin daki yana walkiya.
Hakane fa to zan duba saidai zancen Sale gaskiya ban maki alkawari ba tunda ko an bashi a wajen shan wiwinsa zai kare don me zan dauki dukiyan mutane in danka mashi da sukarye a banza.
Malam yau dai kome sale ya zamo dankane ba a canzawa tuwo suna su wa yan nan daka rike suka zamo abin kwarai ai yanzu sun gujeka sun nuna maka halin yan duniya.
A,a hafsatu muka dai nunawa juna mu dasu tunda yakai har yaran nan yanzu kamar sungane me muke kullawa a kansu don gaba daya yanzu Jafaru ya daina fada min komai nasa kinga kuwa kamar ya ganeni ke nan yanzu.
A bakin yan gari nake jin wai,wani harka ya samu na ma,adaine shine yaje gun sarki ya gabatar da kansa kinsan ko tunda kikaga hakan harkace babba amma yai bugun gaban kanshi yake gabatar da komai ba tare da sanina ba a yanzu.
A,a,a,a aiba ido zamu saka mai ba son mun kwaci wanan dan kudin a hannunsa yanzu dole mu sake shiri a kansa a nemo makashi kamar baya ?
Nagaji da wanan abin hafsatu tunda yaran nan ba mantawa sukayi dani ba gara dai in sun tuna dani inci din yanzu abin nan dana rufewa Halima yana damuna a raina tunda duk yadda nabi a karshe dai kwaliya bata biya kudin sabulu ba kan yaran .
Kai ke ganin haka malam da badon hakan ba aida baka samu kansu hakan daka gama fadi ba a baya saidai kaima ka koma cikin yan kallo a yanzu.
Haka dai ta gama dadin bakinta ta matsa mashi yasha furan yace zai sha don a yanzu ya fara zargin tana mashi asiri don bai iya kyatare zancen hafsatu din har wani shakkunta da tsoro yakeji nata idan ta fadi magana dole a bita koba dadi.
Yanzu ko ya daura dammataran kwato kanshi kan abinda ya dade yana buri a zuciyarsa duk da yasan hakan ba karamin abu bane wajensu hakan zai jawo masu.
Itama dai a bangarenta mikewa tayi cike da tunanen mijin nata da a yanzu yake kokarin juya mata baya don ganin ya damki kudin da suka dade suna shiryawa akansu sun shigo hannusa yake kokarin juya mata baya a yanzu.
Yazama dole ta kara shiri akan malam din don bata tsamaci kudin ba a hannunta zasu zauna ba sai gashi duk da suna wajensa yana kokarin karta ganima da idonta hakan me yake nufi ke nan ?
Takai wani lokaci a wajen tana tunanen hanyar da zata fitowa malam din dashi kafin ta mike ta shiga aikin gabanta tanayi tana saka da warwala a zuciyarta.
Chapter 136 · 0% Book details