← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 306

Sashe 115

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

koma gida nasan ana jirace damu mu koma a zazagemu. Ina gefe daya na takure a waje daya ina sauraren hiransu wanda nake ta auna abin a zuciya da nice mama bataso komai me nayi mata haka ta tsaneni lokaci guda ? Sallah magaribane ya tayar damu a wajen nashige daki suna falo nan sukai sallah ina zaune na kunnu wayata naji karan budan get din gidan muryan maigadin gidan yana tashi. Wai ashe maigidan ne ya dawo a lokacin yake mashi sannu da zuwa salimace ta leko tana fadin ke ga yaya nan wallahi dama ya habu yace kila yau din nan ya iso ai. Mukan zamu tafi gida ke ban yau ashe sai lokacin na dago ina fadin haba anty salima ku tafi gida kamar ya ? In kun wuce dawa zan zauna kuma a wanan gidan kaji munafuka angonki ya dawo kice wai dawa zaki zauna inba kina son sai dare yaya ya gargadamu mubi hanyan tudun wada da kafa ba. Don wanan kwaliyan haka muddin yaya ya gansa yau wallahi idonsa rufewa zaiyi yace me kuma ya tsayar damu ? Na girgiza kai ina fadin anty Salima bamu haka dake fa keda kuma nake samun sauki a wajen ki kin maye min gurbin mariata yau. Tayi waje tana dariya na soma jin muryansu suna mashi sannu da zuwa yana amsawa a cikin muryan nan nasa da dan maganan shi da sauri da sauri yana fadin a,a Nafisa kuna nan ashe sannuku da kokari fa salima ya akayi kunsha hidima fa. Can dai na daina jinshi a falon suma hakan saidai baifi ko minti biyar ba kuma naji yana fadin ya haka kuma ina kuma zaku da daren nan . Muryan Nafisa naji tana fadin gida yaya wai kada dare yayi muna a nan mu rasa abin hawa yace gida yin me kuma don Allah ku mayar da kayan nan ba inda zaku yanzu kamar wa yanda ake kora kuma ina ita Rahama din ?. Muna ga rasulu na fada karda kirana zaiyi haka gabansu shifa haka yake ashe da kowa tsatsaye ba ruwansa. Ina zaune a inda nake na maida hankalina a wayata naji an ruro kofan da sallama ta dan dago mukai arba dashi naji gabana ya soma faduwa . Shima hakan yaji gabansa ya fadi a yadda ya hangoni din zaune saman kujeran dakin na dan dogara jikina ga hannun kujera din da wayata a hannuna. Ga wani irin ni,inttacen kamshi mai kashe jiki dake masa barazana da zuciyarsa ya tako har zuwa gabana na dago cikin sanyin murya ina mashi sannu da dawowa . Ya lumshe ido yana amsawa da yauwa amarya kinsha kamshi ya kika zauna ke kadai a nan gasu can a falo su ko duk bakuntace har yanzu ? Kamar yadda ya dake ya nuna ba komai nima hakan na dake na fara bashi mamaki nace a,a sallah nashigo inyi sai ban fita ba. Taso kije wai gida zasu yanzu amma nace a,a saboda me zasu gida yanzu daga dawowata muje falon mu samesu . Jin hakan yasa na mike tare da daukan dan yalolon gyalena dake gefe daya daga dagashi sai wani kamshi ke fita na daban a dakin hakan yasa ya lumshe idonshi. Ina mikewa naji ya cabki hannuna lokaci guda gaba dayan mu saida kowa jikinmu ya amsa yayi wani yarrr tundai ni da tunda nake babu namijin daya tana ko gwada rike min hannu a rayuwata. Inda shi kuma tsaban taushin da yaji a hannun nawane ya dimautar dashi haka muka fito falon suna zaune tsit a falon sun kurawa tv ido sukaji muryanshi yana fadin. Ga dai matar gidan na kawo muku tunda kuna son yi mata tawaye ku gudu zuwa gida Nafisa tace Allah yaya daka barmu mun tafi tunda ka dawo me zamu zauna yi kuma a nan ? To ke Rahama kinji sai ki basu hakkuri ni dai ban korar maki suba kada kice don ni suka tafi na dan kallesu nayi murmushin da nasan zai dagulashi aiko saida tsikar jikinsa ya tashi nace aiba zasu tafi ba su barni ni kadai. Bari na kawo maka ruwa yaya nan na zare hannuna daga rikon da yayi min a cikin dabara na nufi kitchen a cikin wani tako da ban ma san ina yinsa ba lokacin. Inda ya shagala da kallon bayana ga rigar ta daneni ta baya mazauna da nakan juyawa anty maria don taji haushi suna boucing a ciki. Ya zauna yana lumshe ido a cikin gajiya ga wani bakon kasala da yaji lokaci guda yana sauka mashi tunda yai arba dani ya koma daya sani hakan zai samu taro da yabar yaran nan sunyi tafiyansu amma yanzu ya riga daya kwafsawa kansa kuma ai. Ruwa na dauko a cikin tumbula da zaki iya ganin ruwan karara kwance a cikin madaukin sai cup din glass irinsa dana hado dashi na kawo gabansa na dan rage tsawo ina tsiyayya masa lokacin ya sauke hannunsa dake saman goshi ya bini da kallo tare da ajiyan zuciya da shi kadai yasan dalilinsa. Ya miko hannu ya karbi ruwan tare da fadin thanks ya kai bakinsa saida ya shanye ruwan tas ya aje kofin yana fadin Salima yasu iya dai ? Au bakaje can ba ke nan yace direct nan na nufo ai nagaji sosai yau salima da safen nan fa na dawo Nageria na kuma hau jirgi zuwa Abuja daga lagos yanzu kuma gani gida aikinga akwai gajiya. Kayan na kwashe zuwa kitchen na barshi dasu nan suna dan hiran zumuci can na gama yan dabaruna sai gashi na kata fitowa da da try din dana hada na sake direwa a gabanshi. Kazace data sha gyara wace taji albasa da kabeji su tattasai da kayan kamshi nayi warming dinta a ovorn ga kuma lemun kwakwa da madara na kwali na aje na kallosa. Naga duk hankalinsa yana kaina nace bissimillah yaya dare yayi kada ka kwana da yunwa suma nayi masu tayi. Ai kema ko dazun da mukaci bakici komai bs ki zauna kici Nafisa ta fada nace aiko naci mana anty Nafisa mamaki kamar zai kasheshi a lokacin haka ya daure ya jawo zuwa gabanshi yana cire foilpepper din dana rufa ya kai idonsa sama. Ya kara lumshe idanunsa tare da hamdallah ga ubangiji yake fadin duk tare za aci ai ki zauna muci ya fada yana masu bissimillah.
Chapter 115 · 0% Book details