← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 230 OF 306

Sashe 230

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban san ya akayi ba ummah ta kira Maria ta sheda mata ina kuduna wurinsu nace daga nan kasan mu zan tafi amma sun hanani tafiya gida. Hakan yasa hankali a tashe maria din ta dinga lalubar wayana ina ganin kiranta na shigo min naki dauka a karshema na kashe wayan nawa gaba daya. Ina nan dakin ummah kwance sai gata da waya tana fada min in karba yar uwatace a layin, fuska na bata ina fadin banyin magana da ita a yanzu ummah. Kina da kafuwa Annini ita meye hadinta dasu da zaki ki fada mata damuwanki kuma ko baki fada ba ki karba ku gaisa mana da ita. Dole na mika hannu na karba ummah ta juya ta fita daga dakin ta batmu muna waya ina dauka a dakile nace hello naji tana fadin Ramaah baki kyauta min ba yaya zakisa kafa ki fito gidan mijinki bayan kinsan yana kwance ba lafiya. Kin kuma san yadda ya samu dake a zuciyarsa dole in kikai hakan ya shiga damu gashi ko ya shiga damuwa din don ana kokarin boye masa tafiyan ki har yanzu ya gane abinda ke _fa_ ruwa. To ya gane mana Maria ke kika damu da hakan ni yanzu ta kaina nakeyi bata shi ba don gara dashi yana gaban kowa nasa a gabanshi kuma akeyi min abinda akaga dama bai dauki mataki ba kin kuma sani. Haba Rahama wani mataki kike son ya dauka shida yake kwance bayan haka kinfi kowa sanin yadda suke tsoron mahaifiyarsu ai dukkansu mazan matan ne dai basu faye tsoronta bama nake gani. To suje can suyi ta jin tsoron ta ni ban sake komawa gidan nan wallahi da sauri naji tace ki daina rantsuwa don Allah haka Rahama idan baki koma ba yaya zakiyi da cikin jikinki ke nan kuma ? Nace ciki ciki ai zubarda shi zanyi don ba zan yarda in haifi cikin da zaizo duniya yan uwan ubansa na kirasa da shege ba . Ke Rahama wanan magana ina ya fito kuma nace a bakin Saratu don tace ba a shege waje sai a gidan miji macen data hada kwanan yan uwanta tayi ciki wanan dan ake kira da shege. Innalillahi ta fara ambata tana fadin ita Saare din ta fadi hakan gareki lalai kuwa inta fada akwai magana ke nan gaskiya amma don Allah ina rokonki da kada ki taba cikin nan don Allah saina kashe wayan don takaici daya rufe min zuciya. Sam ya J da kowa nasa har maria dake tare dasu a yanzu sai naji gaba daya sun fice min rai lokaci guda ina dana sanin saninsu ma baki daya don yadda nake ji din. Zuciyana ya dake sosai ba wani zancen kuka a gareni yanzu kawai solution nake nemawa kaina a yanzu wanda kuma zuciyana yafi yarda da in zubar da wanan cikin kaddaran dake jikina lokacin. Kwanciya nayi na lafe muryan ummah yasani dagowa don tashigo tana fadin ki tashi ki saka wani abu a cikinki tun dazun kina daki dunkule. Wayarta na miko mata na dago daga kwancen da nake ina jingina da gado ga abincin nan falo ki fito kici ki watsa ruwa ta fada a cikin tsigar umurni a gareni. Bin bayan ummah din nayi da kallo ina son in fahinci fushi takeyi ko goyon bayana don tunda nazo bata furta min komai ba. Kuma tana falon nayiwa mijinta bayanin zuwana din mikewa nayi zuwa falon inda na hango abinci a kuloli tsakiyan falonta waya takeyi daga kofan dakin ta juyo tana kallona kafin ta karasa fita daga falon gabaki daya. Abincin na bude inda naga shimkafane da miya sai ganyen salad amma miyar na kifine ko ta manta cewa ni bafulatanan asalice ban damu da kifi ba oho ? Su sun iya ci a gidan daddy Abuja tun wani ciki da tayi a yadda take fada muna a baya saini da Abban mune bama son kifi dan gara danima nakanci miyar kifi din wani lokaci ba tare da nayi amanshi ba . Shiko mahaifin mu har ya rasu sam baya cin kifi a rayuwansa na gwada ci din duk da budewana naji yana hawa min kai amma haka na daure na kai a bakina. Kamar kada ya sauka a cikina da sauri na mike zuwa waje dakin inda keda kasa da fulawowi na duka na fara shega amai na fitan hayaci. Sai mai aikinsu ummah dince tazo tana faman yi min sannu daga inda ummah din take taji kakarin aman nawa ta fito da sauri tana tambayan yaya haka kuma ? Na kasa bata amsa a lokacin don yanayin aman da nakeyi din saida ya dan sarara min suna tsaye kaina don har mijin nata ya fito yana tambayan ba,asin aman ? Na lalaba na koma zuwa daki na zauna a falo ina maida numfashi ummah ta shigo ta zauna takara min sannu kafin ta dora da fadin kardai wani abu kika sha don sakarcin da kikeson yiwa kanki ? Idona na kasa ina karewa jan lalen hausa dake kafanta yayi kyau ya karbi kafan nata da kyau na dago a cikin mamaki ina binta da kallo. Sake maimaita tambayan tayi daidai mijin nata yana shigowa dakin ga yar aikinsu a bayanshi dauke da ruwan sanyi ta kawo min shiya cabe tambayan da bata amsa . Yana fadin haba dai har me zata iya yi yanzu kinsan mai karamin ciki da jin tashin zuciya ai na sauke kaina kasa a ciki kunya na nuna mata abincin dake cikin plate din tabi da kallo. Kafin tace abincin bai maki bane in badon ummah bace sai ince tayi min ba daidai ba wallahi wanan tambayan don tafi kowa sanin bancin kifi tun fil azal a rayuwata tundai wanan na tekun mai bakin karnin nan haka ? Bai mata bane nasan tsohon ya fada yanawa kansa matsuguni a daya daga cikin kujerun falon a kasalance na basu amsa da KIFI ? Kifi ta fada a cikin mamaki tana bina da kallo muryan na gwada mamakin hakan tace dama har yanzu ke baki cin kifine Rahama ? Kaina gyada mata tace sam na manta wallahi na zata ai ta daina wanan matsalan na rashin cin kifi a yanzu tunda naga an dade ai ashe matsalanta guda da mahaifinta. Ai dama na fada maki akwai dai wasu sam basa son kifi a rayuwan yanzu me zataci ke nan ko akwai abincin da ba kifi a bata taci ? Yanzu aka dora abincin dare ummah ta fada sai tsohon ya mike zuwa part dinsa ya dan jima sai gashi da furan gora mai sanyi ya kawo min yana fadib ko zata sha wanan din a gwada a gani ko zai tsaya mata. Shina karba nasha na gama na koma daki na kwanta ina lumshe idanuwana rayuwa ke nan rayuwan yanzu sai a hankali yau wai ummah ce zatace ta manta da wasu halaiyan mu na baya data san mu dashi. Ina jin muryansu a falon da alama waya takeyi don naji shima tsohon ya karbi wayan yana fadin haba dai ta dai fadane ai akan me zata zubar da cikin dake da ubansa ? Bacin raine kawai yasa ta furta hakan amma ai Rahama yarinya ce mai hankali kawai dai sun tabatane take son ta rama abinda sukai mata din. Can naji ya koma fadin haba dai ba inda zamu barta ta tafi tunda tazo nan ai shike nan ku barta din ta huta hankalinta ya dawo daidai kawai ? Hawayene suka gangaro min a idanuwana naji wani bakin ciki ya tokare min zuciya da niyata shine in samu da safe in karasa inda na nufa don banda niyar zama wanan gidan gaskiya. Saidai nasan wa yan nan kattan sojojin dake gadin get din gidan yana dawuya in fice wani baiga fitana ba a cikinsu don haka na fara lalubo hanyar da zan gudu nan din don bansan illan daya kaini tsayawa a nan din bama da har na tsaya. Wana furan dana nasha ya rike min cikina bayan nayi sallah magaribane ummah ta shigo tana fadin kada inyi barci fa in tashi inci abinci nakoshi nace daga kwancen da sauri ta kalloni tana fadin me kikaci bayan furan dazun ? Shiru nayi ta koma fadin ki tashi ga Saudi nan tayi maki miyarki daban na nama kici abincin dole na tashi zuwa falon nata. Tuwon shimkafane miyar kuku yaji daddawa da kayan yaji kamshi shi kawai zai sanarma da hakan tsaye tayi a kaina tana fadin ko bai maki bane miyar ? Na dago a hankali ina kallonta a sanyayye na bata ama da yayi min ina lasan miyan tace to kici don Allah kada ki zauna da yunwa don Allah kinsan yanzu bake kadai bane. Ki kula sosai ko baki son abinci ki daure kici don Allah kada lafiyan ku ya tabu daga ke har abin cikin cikin naki kai kawai na iya gyada mata ban iya amsawa . Har zata fita sai kuma ta dawo ta zauna tana fadin ke banda abinki Rahama me zaisa ki bar gidan mijin ki saboda wasu yan uwansa can ke baki ga yadda yar uwarki ta koma masu kurma bane tunda ta fahincesu. Nasan ba haliku daya da ita ba duk da hakan ya kamata ace kin koyi hakkuri hawaye suka soma zubo min ga loman tuwo a hannuna. Falon yayi shiru zuwa can ta mike ta fita tana kiran saudi mai aikinta wai tazo ta zauna dani zata duba tsohon mijinta abinsu a yanzu ya daina ban mamaki. Nasan sauyi rayuwane Allah ya kawowa ummah a yanzu yadda tasha wahala rayuwa a baya saudi din tazo ta zauna dani a falon tana dan jana da fira sai dai ban saki jiki ba. Ta soma fadin wa yan zaria ai ai kasan halinsu kake iya zama dasu kina ganinsu kamar gidadawa sai kin zauna dasu zaki fahinci bakin kishi dasuke dashi ga sakar da haibaici ga mutum Allah ma yayi maku gyadan dogo mazan naku suna son ku ai da baku kai labari ba. Haka suke da sa ido ga abinda yayansu keyi da matayensu su koma kamar kishiyo dasu saidai ba a taru an zama daya ba don wayayyun basa haka gaskiya. Banda murmushi ba abinda nakeyi kawai na gama na wanke
Chapter 230 · 0% Book details