← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 306

Sashe 12

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsaye ta sameshi suna hada kayansu sallama tayi daga bayanshi cikin yar siriryar muryanta ganin kalkon mamakin da Sahabi ke mata a bayanshi yasashi juyawa da sauri yagame sahabi din ke kallo a wajen ? Kasa tayi da kai tana kokarin gaidashi da aiki ta hada da fadin ga kayan ka an hada komai yadda ya dace daga nan ko lagos zaka ba zaiyi komai ba insha Allahu. Ba lagos zani dasu ba zariya zan kaiwa mahaifiyata ya bata amsa tace Allah sarki aiko yayi daidai da bakin tsofi don komai baida tsami da zai hanata bukatansu. Mungode kwarai wallahi yadda ka taimaki rayuwan mu Allah ya taimaki naka kaima ta fada cikin yar siririyar muryanta. Wai tsaya Habu wanan duk kayankane wanan haka kome nifa ban gane ba wuceshi yayi yana fadin ba zaka gane ba kuwa kai matso ku saka min a bayan mota kunji ? Lokacin ibrahim ya karaso yana fadin oga kace da shirinka dama muma bari mu debo namu ashe dama ina son saya ina jin tsoro. Kaje gunta kayansu yana da kyau sosai tace dariya sosai Sahabi ya kwashe dashi yana fadin ashe mun saura dawowa garin da alama zamu dawo wani karon kenan kuma ? Yar filo akwai saura a wajen ku tace eh za a samu bari na duba idan akwai a wajen maman mu ta juya ta soma tafiya . Kai dan iskane yacewa Sahabi dake ta kwasan dariyan shakiyanci sahabi din yace dariya nake don yadda na hasko kayi tsaye ana shadinka kasan wanan aiba karamin shadi zakasha akanta ba wallahi. Shima zancen sahabin saida ya sakashi dariya in akwai abinda ya tsana a taba lafiyan jikinshi balle shadi ta ina zai tsaya kan mace ai mai shadi ko gudane balle ba adadi. Zama yayi saman motan yana sauraren Sahabi dake bayani akan shadi da yadda akewa wanda ya gaza motsin wayarshi ce da tayi dan tsuwa daga Aljihunshi hakan yasa yaciro ya duba alert ne na lokaci har yayi niyar mayar da wayar sai kuma ya fasa hakan sim din ya debe daga cikin wayar ya mike tsaye. Wani wuri dayaga ana sayar da waya ya dosa layin waya ya saya duk da tsadansa bai tsaya neman ragi ba ya biya ya juya ya koma inda ya fito. Ya gama turo komai a dayan wayan nasa kafin ya goge na wanan wayan yana gamawa tana karasowa wajen da kayan ibrahim. Kudi ibrahim ya ciro ya bata yana fadin Allah yasa dai yadda kika yaba haka yake don kada muje gida mu samu ba gaskiya bane yana da matsala ? Irin duban mamaki din nan ta danyi masa kafin ta rausaya kai tana fadin Allah ya tsareni da cutar daku idan na cuceku ina zan ganku ku yafe min ? Daga haka tasa kai ta juya ta zoma tafiya inda kayansu yake daga bayanta muryan Abubakar ne yake tsayar da ita a bayanta ta juyo ta dakata har ya tako zuwa inda take. Baiyi wani magana ba wayan hannunshi kawai ya mika mata bata karba ba kallonshi tayi cikin mamaki ki karba mu rika gaisawa idan nakoma gida. Kaita fara girgiza mashi tana fadin ka barshi bayan wanan alherin dakai muna mai yawa zaka kuma mika min waya ? Ko haka mun gode kasan girman taimakon da kaimuna a yanzu har in mutu ba zan manta da hakan ba a rayuwata zan kuma cigaba dayima addua a kullum kan wanan alherin. Haba dai ya fada yana dan dariya kafin ya saita kansa yana fadin wai zaman me kike a wanan kasan yanzu ko wasan nan ya kawo kuma nan ? Yanayin fuskanta ta sauya lokaci guda tana fadin na fadama kaddaran zaman mu nan sanadin mahaifinmu daya rasu shine zaman mu ya dawo nan kasan don bamu da kowa can Abuja da muke zaune. Nan kuma mun dawone a cikin yan uwa saidai duk da mun dawo cikinsu da zama har yanzu suna,,,,,, Yanda warre ? Wata bakar mace ta sa mata kira daga wajen saida kayansu hakan yasa ta juya da sauri da zumar ta wuce saka mata wayan yayi a cikin kwaryan dake rike a hannunta ya juya ya koma inda ya fito ta dan tsaya ta kalleshi kafin ta nufi wajen nasu saidai kafin takai tacire wayan cikin dabara ta kada a kasan lalitan dake rataye a wuyanta. Basu dauki lokaci a wajen ba taba da umurnin su shirya su soma hanya don ganin yadda mutane keta haramar bin hanya tunda wuri kada suyi dare. Lagos Nageria. Tafe yake cikin motarsa kiran kiran benz wace bai dade da mallakanta ba a yanzu sai kira,a dake tashi a cikin sautin malam Ahmed sulaiman kano. Yake dan bin kira,an shima kafin wayanshi ya dauki kara hamnu yakai yana rage sautin dake tashi na muryan malamin addini a Nageria don ya dauki kiran Saiba amaryansa daya gani din saman layi. Ya akayi Saiba i will call you bank idan na isa yanzu ina hanya ina tukine don Allah ? Sweet J kada ka kashe don Allah ka saurareni don bansan idan ka kashe wani ya rigani kiraka a fadama abinda bashi ba. Meya faru kuma ya fada cikin kaguwa da yaji kome ke bakinta a lokacin dama akan wanan Asmaun ne wallahi idan Asmau bata kama kanta dani ba sai na illanta mata rayuwa. Tseweeee ya tsoki yana fadin akan sakarcinku kika kirani ina saman hanya haka bashi bafa Sweet J mama mukayiwa laifi muka kifa mata abinci saman jikinta. Yana kokarin kashe waya yaji karshen furicinta a dan razane yace wata maman dai kodai Iya kike son kira kikace mama ? Mama dai ta tudun wanda ita nake nufi ta fada a sanyayye innalillahi taji yana ta maimamitawa son bai taba zaton iskancin matan nasa har zai iya kai haka ba ai ? Wallahi Sweet J ba,,,,,,,,, You are very stupid idiot of you don kina yar iska kuyiwa mahaifiyana haka ki kirani kina fada min sai ya kashe wayar gabaki,daya yana jin wani tukuki a zuciyarshi. Fuskanshi ya shafo da hannunsa yana gyara zama a cikin motan don yadda yake jin zuciyarsa ya kasa samun natsuwa da zancen data fada din . Duk yadda akayi wani abu mara kyau ya faru da mama din akansu shikan wai wani aurene yayi a rayuwanshi da kullum baida natsuwa a tare dashi kan matan nasa daya tara agida ? Yanzu wazai kira yaji meke faruwane wai don baima son ji daga bakin ko dayansu a yanzu wanan karon sam ba zai kyalesu ba iskancin nasu yayi yawa har abin yakai ga mahaifiyarsa haka ? Wa,iyazu billah a ina sukaga mama din har take fadin sun mata wani abu mara dadi hakane tunawa yayi tsakiyan watane ake a lokacin don haka mama tazo gidan ke nan gyarawa iya daki . Dama daga tsakiyan wata zuwa karshen wata take zuwa wajen mahaifiyar nata taimata kwalema don samun ladan mahaifiya a gareta. Har in mama zata iya tsayawa akan nata mahaifiyar haka su da karfin su mai zai hanasu tsayawa akanta har inda karfinsu ya kare akantasu mahaifiyar. Oh shet yanzu wa zai kira yaji abindake faruwa har ya shiga haraban nasu da mota sai a lokacin Abubakar ya fado mashi a rai . Da sauri ya lalubi waya yana neman layin Abubakar din sai gashi ya samesa ya dauka yana fadin na dauka ka manta da dan kanin nakane ai gamu nan yanzun muke shigowa Nageria ai. Sam ya manta da cewa Abubakar din baya gida ya kirashi ya sheda mai zasu shiga kasan Cameroon wani shutting don haka bai gida ke nan a lokacin. Saiya waye da fadin masha Allah Allah ya kawoku gida lafiya sai zuwa gobe dai ke nan zaku iso yace insha Allahu nagode yaya J . Suka kashe wayan yace common wazan kira ke nan kafin yakai karshen tunane aka buga glass din motan nasa meiyabi ce don yana kallonta ta bangarenshi. Kallon tsab yai mata kafin ya sauke glasa din yana kako murmushin dole a fuskanshi yace hey how are you tayi murmushi tana fadin . Mr handsome ka boye da yawa kwanan nan duk bani ganin ka na dauka kayi tafiyane ai da ban ganka ba kana jin dadin kafa garin nan ? Dan murmushin yake yayi mata kafin yace in baki ganni ba aini ina ganinki sometimes tare da wanan dogo saurayin naki. Dariya ta kwashe dashi kafin tace waiko ka fara kishi akainane haka da har zaka ganni kaki min magana wani kallo ya watsa mata na takaici ya karasa fitowa cikin motan yana facing dinta. Gata bakace bata shafa mai da matan yanzu suke yawan shafawa jikinsu su canza kala ba ita tabar bakinta na natural maikyau saidai gaskiya idan ace ta girmeshi da kusan shekara bakwai zuwa takwas ko goma ba zai musa hakan ba amma kuma wai sonshi takeyi a hakan ita. Yana dai son su rabu lafiya hakan yasa yake dan tsayawa ya biyewa shirmenta wani lokacin idan mutanen arzkin na kansa ayi hai hai a watse lafiya. Handsome dama ina son ganin ka muyi wani magana naga kai mutumne mai harkan bussiness so akwai wani brother nawa dake wanan harkan acan porthercout nake son in hadaka dashi amma kaje kayi tunane idan zaka iya don harkane dake son natsuwa sosai a cikinsa. Na yaba da hankalinka da irin natsuwan ka yasa nayima sha,awan wanan harkan ya dade yana neman dan arewa dayake da amana wanda zasuyi wanan harkan dashi sai nayima sha,awan hakan. Kallon ta yayi a tsanake yana karontota a zuciyarshi ba wasa a cikin lamarinta don haka shima ya natsu ya maida hankali kanta budan bakinshi tambayanta yayi da why me ? Sai yaga tayi murmushi ta dan kara matsowa kusa dashi tana fadin you deserve ita handsome kana da natsuwa sosai wallahi beside kuma ni din ina kaunarka har cikin raina don haka tunda you are pure baka harkan banza kai nake son friendship din mu ya zamo zumunci a yanzu dakai. Ina mai baka shawara akwai alheri sosai da zaka samu a cikin harkan nan har idan ka rike gaskiya a yadda kake din nan baka sauya zuciyar ka daga baya ba. Don mutane da yawa a yanzu kudi na canza masu akida saidai
Chapter 12 · 0% Book details