Sashe 39
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranan monday da safe na samu labarin abinda ke faruwa a gidan koshi abakin anty Salima da yanzu muke dan shiri sosai da ita. A wajenta nake tsuntar labaran abindake gudana gidan nasu don ni ban damu da nasan komai ba abu daya zuwa biyu nafi rikewa a raina shine nidai yar tafiyace ma,ana yar rakiyar aure. Nazo gidansu a sanadin rako yar uwata aurene saboda debe kewa a gareta nasan kuma rashin gata yasa aka hadomu tare ba wani abu ba don a ragewa mahaifiyar mu nauyi a gabanta. Idan bashi ba a shekatuna goma sha nayi girman da zan zama yar tafiya na koma Murfin Jallo ga yar uwata da yanzu auren nan kamar ta danballene ma nake gani don da da dan kuzarin ta amma a yanzu ta koma wata sau da ita bata da lakka ko wayau. Don haka tuna sanadin zuwana gidan bai bari na wuce iyakata ba iyaka dasu halin zama tare sun bani mafaka ni kuma in basu karfina wajen abinda ya dace. Zance bai tasowa tun zuwan mu gidan kaji sunan yar uwata a ciki balleni musan yadda muke takon mu dasu bakaji zance a bakin mu saidai a kiramu don shedan muna wajen abin ya faru. Koshj wanan zancen a zaton salima nasan da zancen take fadin gobene za a kai Maria asibiti ko ? Azotana irin zuwan da sukeyi suje awone take tambayana sai nake cewa eh gobene sai naji tace dani Allah sarki ni tausayi mariya ke ban wallahi a daidai lokacin da mutum yake son zama da mijinshi ace za a rikeshi asibiti ya zauna har sai ya haihu wanan abin akwai takura ai a cikinsa wallahi ? Anty Maria din zata zauna cikin asibiti har sai ta haihu anty Salima tace ba haka akace ba Ramaah koke baki fahinci zancen bane wai Ramaah ? Kodana dago kai hawayene ya bata min fuska ban iya magana ba ta juya ta shiga bandaki don dama wanka zata shiga muke hiran . Mikewa nayi na fito daga dakin zuwa wajen yar uwata da akwanakin nake ganinta cikin damuwa zaune na sameta a falonta ta kifa kai a saman hannun kujera. Nayi sallama na shigo fuskanta kawai na kalla nasan itama tayi kukan a lokacin nafara fadin meyasa baki fada min abindake faruwa dake bane Yanda ? Duk da sunan yanda din da suka san ma,ananshi a yanzu sun mayar da sunan akaina a gidan ni kaina a yanzu ina kokarin karbe mata sunan nata da mahaifanmu ke kiranta dashi na yan mata. Mezan fada maki Ramaah tashin hankalin da nake ciki kema ki shiga amma ai ba yau muka fara fadawa junan mu tashin hankali ba yanda nakirata da sunan da muka saba kiranta dashi din. Nacigaba da fadin ko a yanzu ban cancanci naji damuwanki bane kamar baya yadda muka taso daga mu sai Allah sai mahaifanmu a tare damu. Ramaah me kikeso na fada maki nace dake likita yace ba zan iya renon ciki ba sai da kulawansu duk na tayar maki da hankali kamar yadda nawa yake a tashe ? Kallon kofan dakin su da takeyi yasa na juya mijintane a tsaye yanayinshi kadai zaka kalla kasan yana cikin matukar damuwa shima din a lokacin. Hakan baisa nayi shiru ba don da yare muke maganan nace kinsan matsalan ki yanda bata asibiti bace dole sai mun koma wajen baffa an suhunta dashi zaki zauna ki tauye kanki a nan kuma ? Ba wai hakana bane Ramaah abinda likita ya fada suke bi duk da nasan abin nada alaka da baffa amma su nan birnine ai ba zasu yarda da hakan ba su. Gyaran murya yayi na sake juyawa gareshi karasa fitowa yake zuwa falon ya samu waje ya zauna yana fadin lafiya dai ko ? Kalloshi nayi cikin yanayin damuwa ina fadin ina kwana ya amsa sai naji tace zance take akan tafiyana asibiti wai lalurana bana asibiti bane sai naga ya tsuke fuskanshi lokaci guda. Yana fadin idan bana asibiti bane na meye ke likitace Ramaah da zaki fadi taki hasashen abinda likita ya hasaso gareta ke nan ba zatayi wani dogon motsi ko daukan abu mai nauyi ko wani abu da zai iya taba lafiyan mahaifan dake dauke da jinjirinta ba a yanzu ? Don haka dole sai sun riketa a wajensu suna bata kulawansu su saka ido ga duk wani motsi nata a yanzu shine kawai dalilin da zata zauna a wajensu din ai. Ummah zatazo daga Jimeta a gobe insha Allahu itace zata zauna da ita asibiti don haka wanan ba wani abin damuwa bane insha Allah. Duk da naji ummah mu zatazo zama da ita hakan baisa naji dadin zuwan nata ba don nasan wahala kadai zatayi a can din tuno da lamarin baffa da zuciyana ke min. Akan bakin halin baffa a lokacin a gaban idona naga yadda yake tauye Hanne data shiga huruminsa abinda bai kai ya kawo ba amma haka baffa ranan don fada kawai akan yara da suka kora shanunsu zuwa kiwo suka samu hanne ta riga su zuwa da nasu shanun a inda zasu sake shanun mu. Sukai magana ta kwashe taki kwashe shanayen nasu tace aita rigasu zuwa dole suka juya da nasu shanun zuwa wani waje suka sakesu kiwo. Bayan an dawo gidane baffa ya taresu yana fadin yau shanu basu koshi ba yasan kuma komai shi Hanne zatayiwa tsageranci zai nuna mata ko ubanta bai isa ja dashi ba balle ita. A gaban mu ya fito da wani babyn roba mai gaba gaba zakice mutum ne kamar wata jaririyace a hannunsa ya shiga dakinsa dashi a hasale. In gajarce maki labarin nan duk lokacin da baffa ya murda wanan babyn roban idan kafa ya murda haka hanne zatayi ta tsala ihu da sai mujita a namu ruggan saboda azaba. Idan hannun roban ya murda ranan hannunce zata lamkwashe ta dinga ihu tana neman taimako masu magani sunzo kala kala ankai hanne asibiti birni an kashe kudi yafi a kirga amma hanne bata samu lafiya ba. Ranan da na girsheshi yana murda kan wanan babyn roban cikin mugunta daya bayyana afuskansa yana wasu suraita naja baya a hankali don baisan ina wajen ba. A ranan muka samu labarin wuyan hanne ya kare tana batun mutuwa haka da baffa din ya fito daga daki idonsa a kaina ya sauka yana min alaman gargadi ban nuna nasan abinda yake nufi akaina ba lokacin. Don zuwa lokacin na daina tsoron baffa tunda yake kirana da shu,umma idan dare yayi yaji ina rewa kira,an da muka koya a abuja don mu din mun sauke alkur,ani a lokacin gidan Alh tun barinka nono zaka fara bin yan uwa karatu don haka ya gargadeni da na daina naki sai dai in rage sauti yake kirana da shu,umma abakinsa ni kuma tsoron shu,umancinsa ya fita raina. A wanan case na hanne na yarda baffa shu,umine na gaske don dashi mahaifin Hanne ke fadi tashi dashi aketa zuwa asibitin birni ana kashin kudi wani lokacin shine mai zuwa amso maganin kan matsalan hanne din. Shiyasa bahaushe yace makashinka yana tare dakai ko wani lokaci muna tare da makiyan mu bamu sani ba a duniya. Haka Hanne ta wahala sosai dukiyan mahaifanta yana tafiya baffa yana mata dariyan mugunta yana bin babyn roban daya sihirce da sunan hanne yana lugudewa karshe shanayen mahaifin hannene sukai rauni. Saida Allah ya nufi hanne tana da sauran rabon shan ruwa a duniya ranan baffa din ya tafi Adamawan cameroon wajen wani amininsa aka ga wuta ya kama a bukkansa. Ko yaji tsoron kashewa andai zuba ruwa har angaji wutan saida ya lashe bukan Baffa kaf yadda wuta ya kona roban haka jikin hanne yaji amma ta samu kubuta. Da Baffa ya dawo daureshine kawai ba ayi ba don duk wani kayan tsafinsa ya kone a wanan gobaran wasu tun yana yaro wasu kuma da girmansa ya karbo sihirin yake aiwatar da sherinsa akai. Har yau kuma ba a san nice na hada baki da dan uwan hanne yazo ya saka wuta a bukkan baffa ba a cikin wa yanda suka samu saukin hakan har da mahaifiyar mu da yanzu take iya mayar da magana a cikin iyalan baffa din daya rufe mata baki haka yasa na gane muma baffa ya kullemune a lokacin da sihirinsa don a lokacin muka fara samun sauki a cikin hakan kuma zancen auren Yanda ya taso har ya rasa me zaiyi yace ya barwa hardo mu da sharadin baiba da ko Nagge guda don shanun babanmu sun zama nasa a yanzu. Baffa mugune ko cikin muggai nasan zai iya illanta anty Maria tunda ya kufulemu a cikin ransa zai iya aiwatar da wani mugun nufinsa akanta yanzu. Allah yafika baffa na fada a hankali wa Allah yafi Ramaah naji muryan ya Habu yana tambaya nace baffa na juya na fita daga dakin rai bace. Part din iya na koma suna zaune dukkansu a falo mamace ke tambayana da Ramaah kin karya kuwa tana kallona. Kai na girgiza mata don shiririta Ramaah zaki zauna da yunwa a cikinki har wanan lokacin maza dauko kofi kizo ki hada shayi kisha ga kuma dankali a wanan roban ki diba kici tafada. Nima takan ban mamaki wani lokacin idan tace bata karya ba mutum ya tashi yayi wanan uban shara da wanke wanke amma kuma yakai wani lokaci yace baici komai ba. Zama nayi kamar yadda mama dubu ta umurce ni dan zuba ruwan zafi kadan na hada shayin na dan dibi dankali ina tsakura a hankali. Suna hiran su sai iyace ke fada dani kan na dibi abu kadan kamar za abawa jariri murmushi kawai nayi don zuwana dake tuna min da baffa a lokacin. Banda natsuwa a yau ina tunanen shu,umancin baffa a raina zai iya fiye da hakan a kan yar uwata tunda ya fada da bakinsa taje koba aure ba taji tayi auren kado din data saka kanta ya gani. Waiba muryan anty Asmau nake ji ba anty Saare ta fada tun dazun nake jin muryansu ai inji salima sai mama dubu tace yau kuma me suka tashi dashi da wanan fitina ? Turo kofan da akayine yasa mu kallon kofan don kofan yana bada kara idan an tabashi wanda naciki zai