Sashe 109
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ma yanzu da naji cewa ba a gida daya zan zauna da matansa ba . Sai abin ya dan min dadi a raina koba komai wanan zullumin da fargaba zai rage min akan ace muna zaune waje daya dasu. Nasamu training fiye da zaton ki mai karatu dan zaman da nayi da anty salma ta bude min ido ta wayar dani banda tsoro ko fargaba a baya har ina jin idan na koma zaria zamu kwashi yan kallo dasu. Sai gashi zancen auren nan na yaya Jafar a kaina yanzu ya jawo min cikas ga duk plan dina nima yanzu dole ta kaina nakeyi yadda zan kasance dasu . Balle nace zan taya yar uwata danayi niyar tayata zama da fitinansu yanzu kam nasan a kaina abin zai dawo gaba daya tunda dole in zauna kamar yadda daddy da mama suka roka a gareni. Shi kishi ko zaman aure ga ya mace halittane garemu mata wanda bamu san muna da baiwanshi ba sai in mun gwada. Haka kawai mace ke tsuntar kanta da iya irin rayuwan data zabawa kanta zatayi dma gidan miji don haka a bangarena idan na zauna ni kadai abinda nake tunane shine ta ina zan fara a gidan ? Da bangaren shi yaya Jafarne ko bangaren matanshi ko kuma bangaren mama da yaranta duk da nasan banda matsala dasu saida Saare amma yadda anty Nafisa ke fada min a yanzu mama ta canza sosai game dani. Nikan an sakani cikin tsaka mai wuya a wanan auren an tauye min rayuwata da yawa me zangane a wanan gida hakan ya zamo sonkai ga yaya Jafar duk da bansan ainihin manufanshi na zarga min abinda bai shafeni ba. KD Cikinta mahaifiyarta tayi da fada akan ta shirya ta dawo dakinta kafin tayiwa kanta aikin dana sani haka kawai zaki kwaso kafa kin dawo gida kin zauna don mijinki kawai ya kara aure ? Har uwar ta gama batace kalla ba don sai take daukan uwar bata damu da itaba yasa a kullum take nuna mata ta saita koma haka zikau ba wani magana akan shanmatan sa Jafar din yai mata. Saidai Halisa yarta ta shigone suka kebe tana fada mata irin matsin da uwarsu ke mata akan ta koma zaria din . Yaya takan fara magananta ke nan fa don me zaki koma zaria Jafar baizo ba ita bata tsayawa ta kwatowa mutum hakkinsa idan kuma za a kwato mashi ta hana,. Yanzu dai muje gidan anty Sabi,a muji kota samu aika sakon don nafi bukatan sai kin rikeshi zaki koma har in zaki koma din ne yar ta fada hakan yasa Nusaiba ta mike ta shirya suka fita ita da yar uwarta. Da kafa suka taka zuwa unguwar don ba nisa gidan Sabi,a din da alaman matar gidan tana da baki don motar da suka gani a kofan gidan. Sun shiga da sallama suna falo zaune suke amsa masu an fara gaisawa bakuwar Sabi,a ke fadin waiba Saiba umar bace ? Nice ta fada tana kallon mai maganan kafin tace sa,ade yakubu ko suka kwashe da dariya son tun barinsu makaranta rabon da su hadu don haka da murna suka rungume juna. Saiba ta kalli Sa,adatu tana fadin wai Sa,ade kece haka kinyi wani fresh dake kamar wata matar gwauna ? Murmushi wace aka kira din tayi tana fadin kaji ki dai da wani zance Nusaiba har yanzu dai halinki yana nan na zolaya ko ? Wallahi kina inane wai yanzu nusaiba ta kara tambayanta tace ina nan gefe daya ba kun manta da kowa ba yanzu haba dai ai kema kinsan hakan bai yuyuwa nakan tambayeki wallahi. Har yanzu kuna tare da mustapha ko haba dai daram kuwa muna calarba yanzu kinsan a can yake aikinsa . Kice min mutumiyar kinyi nisa da garin nan gaskiya na daina jin ki gaba daya wallahi lalai mustapha ya iya rikon aure kinga yadda kika koma wata babban mace ? Gaskiya da ganin ki kin samu kan mustaphan nan a hannu Sa,ade murmushin kasaita tayi tana fadin Saiba ke nan wani samunshi nayi kuma ? Takai zaune a gefenta tana fadin wallahi sa,ade kin kara hadewa ba irin mu ba nan ni gani wanan dan iskan zai kasheni wai wata kishiyar kuma ya kara auro muna yanzu . Cikin mamaki Sa,ade take kallonta tace saiba kanki daya kuwa da hankalinki kuwa ? Mijin naki kike zagi da dan iska meye a cikin kara aure don ya kara aure saiba ? Wai ina labarin Asmy ne har yanzu kuna tare kuwa ta bata rai tana fadin muna nan tana zaria muna nan muna bugawa da ita. Murmushi tayi tace kema Nusaiba kinsan ai dole ayi hakan kema kawarki ta kut da kut fa kika ciwa amana kina tunanen Allah zai barki haka ba jerabawane ? To amma ai naji ance kuna cikin rufin asirin ku don ina da labarin ku mijin ku bai rageku da komau ba na rayuwa. Naga tun haduwan ku kin kwacewa Asmy shi yana kuma yi maki yadda kike so to me kike bukata kuma ina ruwanki da kara aurensa ? Wallahi Sa,ade ba zaki gane bane ni yanzu ai nayi nadaman aurenshi uwarshi da yan uwanshine fa suke juya shi har mu . Haka basu kaunarmu ko kadan tundai ni basu sona musanman mahaifiyarshi da kaninshi wai shine yanzu don cin amana kanin nasa yasa ya auri kanwar matarshi fa. Ni kuma nace bai isa ba wallahi don ubansa sai naga yadda shegiya zata zauna a gidan nan ? Umm,umm subbahanallah Nusaiba har yanzu haka kike da wanan halin naki ashe wallahi gara tun wuri ki bari zaifi. Ni dai shawarata gaskiya dolene ki sauke wanan girman kan naki da wani jiji da kai har in kina son gane kan mijiki dole kiyi masa biyayya kamar yadda Allah yace ki kuma zauna lafiya da abokan zaman ki. Abincinsa shimfidansa da komai nasa hakama yan uwansa sai kiga kun zauna dashi lafiya amma idan kikace ba hakaba sai abinda kikaga dama zakiyi kinsan wallahi ko yar gwal kike ba zaku shirya ba ita Asmau fa da kika sama ? Na tabbatar ba haka take ba ita saidai yanayin zama dake sauya mutum wani lokaci don dai zuwa yanzu,,,, Bari kiji Sa,ade wallahi kinsan tun ba yau ba daga shi har Asmau basu isa su sake min halina ba don bawani mutuncin da zan tsayayi akan kishiya. Ke kika dauki wata tsiya wai biyayyan aure irin na matan da da suke wahala akan aure haka kawai in zauna ana juyani. Aure kuma nace bai isa ba wallahi kuma wallahi bai isan bane falon yayi tsit ana sauraronta a lokacin. Sai Sa,adatun tace waike hanashi auren zakiyi inace sai yaso zai zauna dake dai tunda ragamar auren yana a hannusa. Ai sai idan ya raga makine zai barki ki zauna har ki daga mashi hankali dashi da sauran matan nasa yanzu idan kin tada hankali yace ki bar masa gida fa ? Gabantane ya fadi sam ta mace zai iya yin hakan ta lamkwashe a waje daya tana tunane Sa,ade ta kalleta tana murmushi tace wallahi don haka kibi sannu. Gara kiyiwa kanki fada don namiji zai kara aure zaki tsaya kina wanan daga hankali haka duk gatan mace yau akace ta koma bazawara an gama dake. Don haka kibi sannu ku zauna lafiya kibar wanan cika bakin kada zance ya koma a kunnensa daga gefe halisa yarta tace shi nake fada mata. Shiyasa na kawota nan wajen anty ta dai dan bata dabarun mu na mata itama tayi kaddari kada dai ta koma baya a cikin kishiyoyi. Mafalki ke nan anty Halisa ai in banyi gaba ba babu shegiyar da zata shigo tayi gaba a wajensa bari dai in koma kawai ki gani. Haka dai suka zauna suna bata shawara amma a banza don ko daya bata dauka a cikin shawaran nasu ba lokacin har Saaden tayi masu sallama ta tafi.