Sashe 49
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan kwana hudu ya sauka garin da tarin alheri mai yawa dan tab motar dayazo dashi take da tsaraba. Mu mukai ta jidan kayan zuwa cikin gida dasu part dinshi muna tarawa a tsakar falo koda muka gama kwanciya nayi lokacin. Saida asuba da muka tashi yin sahurne nake jin yar wajensu anty Saare na fadin dama tasan zai dawo da alheri haka mai yawa. Don tana zaune yake tambayan su dame dame zai sayo a lagos don a rage kayan sallah suka lissafa mashi yace saura sai idan yazo nan zai saya. Anan na gane kayan da mukai ta jida zuwa cikin gida shi take nufi nikan ko kusz ban kawo da rabona a cikin kayan ba don haka ban tsoma masu baki ba nasan dai shima yaya Habu idan ya tashi saya zai sayo dani donshi ba zaice ya manta dani ba . Tunda sanadinsa nake zaune a gidan wanda kiri kiri matan dan uwansa suka nuna suna kyashin zaman mu a gidan mu kuma da muka fisu iya miskilanci muka nuna bamu san sunayi ba ma. Ruwan shayi kadai nake sahur dashi in kwanta ko ranan inga gama sha na shige daki na kwanta da yake azumi na kai bakwai ban fito yin shara ba saida gari ya kara haskawa na fito nayi shara da wanke wanke na koma na kwanta. Yanzu mama tana gida kamar yadda yayanta sukace ta dawo gida da azumi sai ummah mu da yar uwata ke asibitin gashi ita Yanda sai an hada mata abinci don ba halin tayi azumi din a lokacin. Abincinta na dora wanda a yanzu sau daya akeyi da ankai abin karyawa sai kuma na dare donshi nakeyin wanda ba zai lalace da wuri ba akai mata. Ina gamawa na koma daki na kwanta ban fito ba sai da azahar daidai lokacin kuma muke fara shirin abin buda baki a kullum. Saman gado naga kaya saidai ban tsaya ba na shige ban daki dana fitone na kula laces ne saman gadon ajiye a cikin leda ban kuma tsaya budewa ba na tayar da sallah ina gamawa na dauko dogon rigan da anty Salima ta ban nasaka dogon rigar atamface dinkin pitted ya dan matse min jikina kadan don zan fita kurman jiki. Falon na fito na samu mama tana gyaran kullum masa da za ayi ranan nayi mamaki ganin hakan gaida ita nayi ta amsa tana fadin Rahama kin tashi ashe yanzu nake zancen zuci a kanki ai. Natashi mama na kara fada masa zamuyiwa yayan ku yau tun da safe nake aikinsa na barkine ki huta tunda kin samu barci yanzu don Allah fitar min da kayan miyan can daga waje mu dora murhu zaifi sauki ba zan iya yin wanan aikin a saman gas ba . Na juya na dauki kayan miyan mai yawa a wani baho nauyin sa ya ban mamaki ina fita nake jin mama na kwalawa yan matan ta kira da su fito su sameta waje. Icen na hada da komao yadda ya dace a wajen gidan wajen wani dan innuwa kujera na dora mata sai na nufi wajen famfon waje da kayan miyan . Alokacin naga ashe naman kaine na saniya guda aka sare yasa roban nauyi sai kayan miya da aka zuba sama ya rufe wanan din. Mama ta fito tana fadin kinsan Jafar da hauka yace masa yake so ayi mai yau yasha ruwa da abokansa na lissafa mai tare da sako tun safe a hada mun wan kullum yanzu buhari ya kawo minshi daga can gidan da aka niko min. Nagane me take nufi yasa naci gaba da mamaki miyan muka fara hadawa tunda miyan naman kaine bamu tsaya sai markaden ya soyo ba irin miyan shinkafa. Wanda a lokacin mukai mashi hadin gaba daya bayan mun soya mai daban muka lema a saman markaden dake tafasa a wuta kayan kamshi da komai aka zuba muka shiga gyara wuta idan ya jaye. Saida mukai sallah la,asar ta fara suya da kanta a zatonta ban iya ba tunda ni bafulatanan dajice ai don a daji suka dauko mu. Sukan manta da kaddaran mutuwa ya mayar damu dajin da suka ganmu a ciki din amma komai na rayuwan bahaushe shine akidar mu. Saboda iya na koma ciki don tace ita sai an dafa mata shimkafa da miyan da zataci da ganyen salad kai azumi bakaci ganye ba aiba yi bane. Har nagama miya na dora shimkafa na fito anty Saare na samu saman tanda tana tuyar waina nace ta kawo in gwada wutan na gyara na bajeshi da kyau kafin na fara zuba man suyar cikin yan mintuna na tara waina karshe dai nice na karasa suyan mama tana ta masu kwakwazon hakan . Tace komai yar nan ta iya duk abinda kasa kanka a duniya zaka iya amma shiririta ya hana ku tsaya ku koyi girki da zakuyiwa mazajen ku nan gaba. Su wa yancan mashiririta kuna dai gani mijinsu yana son abincin gargajiya amma basu iya ba sai shirme daga taliya sai indomi wanan girkin macen arzikine ? Sai gashi kuma ya shigo da kayan shan ruwa niki niki aka jibgesu a nan inda muken yana fadin ke Saratu don shi da sunanta na yanka yake kiranta dashi. Ki gyara muna kiyi fruit salad a jefa kankara ta kalleshi tana bata fuska alaman itafa ta gaji lokacin mama din tace wai kai don me ba zaka kaiwa matanka wanan wahalan daka jajibowa mutane ba ? Ya dan marairaice yace mama ai sai naji kunya wa yan nan me suka iya don Allah banda shirme aida su fito su kama a samu a hada da wuri kada a makara. No please mama son Allah barsu a can suna zuwa wajen nan aikin zai tsaya ko su tafkawa mutane shirme yanzu dai a kara da ferfesun kifi irin na ranan da kika bani da safe. Ga wace ta hada can ai tana nuna mashi ni ta kara da fadin indai kaci abincin arziki a gidan nan itace ta hadashi ko yar uwarta . Mama wanda nace dake kamar hadin restaurants din nan fa itace na fada maka ko masa yanzu data karba tayi bakaga yadda ya fita gwanin ban sha,awa ba shine ma nasa su zuba maka. Ya juyo ya dan kalloni yana fadin don Allah ki taimaka kiyi min irinsa ga kifi nan a leda an wanke anyi komai sai ayi yadda ya dace ya miko kudi yana fadin gashi idan za a sai wani abune akara a ciki ? Da sauri anty Saare ta karbe kudin daga hannunsa uwar tace nan kikaci rani har damina ya sameki wajen son kudi tandan masan na sauke na shiga ciki dauko kayan hadin . Dan attah kadan da albasa sai kayan yajin mu na hausa da citta yafi yawa da tafarnuwa da species kadan na dauka daka na fito sharp sharp don lokacin daya karato na shan ruwa har na gama hadawa ina jiran ya tafasa. Naga suna shirme na karba uwar tagumi tayi ta zuba min ido tana kallon ikon Allah tsab na hada fruit salad din da yaji madara da kankanran da zai sakashi sanyi sai flavour don yayi kamshi. Tabarama manya guda biyu anty salima ta shimfida masu saman barandan part dinshi data share sai aka shiga jera kayan abincin harda shimkafan da miyan da mukayi da kunun tsamiya duk aka fita masu dashi wajen shan ruwan da alale da mama ta hada. Nikan tun da aka soma kiran sallah nashige ban fito ba sai suke kai da komo akan abokan yayan nasu abincin asibiti da za a kaiwa ummah na buda baki na fito dashi don dama na damu banji ana zancen kaiwa uwata abinci ba gashi lokaci ya shige wanda aka dauka don hakan yanzo lokacin dauka. Sai lokacin naga motoci zasu kai biyar a wajen nasan ashe yawa garesu don abokanshi na kurciyane dama haka suka taso sunayi a tsakaninsu. Ummah dataga har lokacin shan ruwa yayi ba a kawo masu abinci ba ranan yadda aka saba saita dan fita don tasayo dabino da ruwan sanyi a wajen asibiti. Ganinta yasa wata mace da suka saba take fadin hafsatu yanzu nake zancen yau banga an shigo maki da abinci ba kizo mu zauna mu buda baki kafin a kawo maki. Da kunya ummah tace da matar a,a ki barshi zasu kawo akwai abinda ya tsayar dasu ai kila amma suna tafe nasani haba hafsatu . Aiko ba sabo haka tsakanin mu akwai na musulunci don Allah zo ko dabino da lemu kisha ga ruwan sanyi kada kice a,a ki hana min ladan hakan ? Dole ta zauna suka sha ruwan tare saidai dabinon nan da lemon da ruwa kawai taci daga garesu suka mike don yin alwala. Nan suka zauna bayan sun idar suna dan hira matar tana buda bakinta tunda tasan baci ummah zatayi ba kota matsa mata. Ruwan sanyi ma gashi ranan tana ganinsu dashi amma haka taje gurin sayarwa ta sayo saida matar tagani take maganan bata kyauta mata ba meye amfanin zama taren da sukeyi kuma ? Irin halaiyan ummah na kama kai yasa matar sha,awan ummah din sosai gashi ita kome aka kawo mata saita nemi matar ta bata koda abin dan kadan ne amma ita bata saka ido ga kowa sai abinda ya kawota. Har mu dake zuwa mun san da shakuwar ummah da matar don bamu shiga mu fita sai muje mun gaida mara lafiyan su da matar a duk inda take. Ainihi matar daga kaduna sukazo ba a cikin garin zaria suke ba saidai suna da yan uwa sosai a garin don haka gidane masu zaria din. Tana zaune ta hango yaron yana nemanta ta kirashi yazo da basket da ledan poly bag yana gaisheta bai bata kayan a nan ba saida suka shiga ciki ya aje. Ya gaida yanda da ba,a bari su fita ko ina sai idan su suka bada umurnin mutum ya fita daga dakin zai dan fita yasha iska ya dawo ciki. Kai bawa ya godewa Allah aduk halin daya samu kansa a ciki rahamace hakan garesa daga Allah wata zatayi cikinta lafiya har ta dauka ta haife bata taka asibiti ba . Saiga wasu kuma don son haihuwan za a rikesu gun likita