Sashe 202
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
idona ba har ita da Saratu zasu zauna suna sakar min magana don ina tsoron su in kyalesu niba irin wace zata zauna kiwa abinda ranki yake so bane. Ya isa hakan tunda sunyi shiru kadama ta bari don Allah taci gaba tunda ita tafi kowa baki dama dan kauye ai bai iya wayewa ba aka ce . Allah sarki dadin abin kowa asalinsa kauyene abin bukata shine ilimi koda yake ba abin mamaki bane don kince hakan tunda baku tsaya kun ilimantu ba dole kuyi halin marasa hankali. Wanan maganan dana fada shiya harzuka su muka koma cacan baki da karfi dasu har mutanen gida suka farga da abinda ke faruwa a lokacin . Anyi daidai maman tudun wada ta dawo suka shigo suna salati da tambayan meke faruwa nan suka so juya zancen da cewa nice na jawo fitinan nan mama take fadin. Assha Rahama ina ganin ki mai hankali ya kuma haka a gaban mara lafiya kuke jidali haka cikin rashin hankali nan nima na mayar masu da yadda suka tsokaleni na kasa hakkuri. Tir da halin ki Saratu halin nan naki baiyi ba wallahi ko dai me kikayi Jafaru dan uwankine na jini baki kuma da kamar shi yarinyar nan kowa ya sani tana iya bakin kokarin ta wajen kawar da kanta ga duk wani fitina ga zancen nan. Amma saida kuka san hanyar da kuka bi akaji bakin ku haka hatta kayan amfani ina kule ke Nusaiba kwashe abinki kikeyi don kada tayi amfani dashi saida ta sayo nata ta aje a nan . To tsaya kuji wallahi daga yau tunda ciwon yaron nan ba damuwanku, yayi ba gaba dayan ku banda shigowa gaisuwa ku duba shi kada wace ta kara zama a wajen nan tunda ba damuwa da ciwon nasa kukayi ba. Na dauka abinku na lokacine zaku saduda ku natsu ta dalilin wanan abin daya samu yaron nan sai gashi rashin hankalin ku yafi haka ashe. Ke kuma ki koma can gidan ki idan kinso kizo ki dubashi ki koma kullum inma ba zaki zo ba dai kiyi zamanki a dakinki ba sai kinzo ba. Mama dubu ce ke fada cikin bacin rai damu duka ina yunkurin mikewa naji dayan maman tana fadin ai idan wanan yar mai kulan ta barmu zance ya baci don ko gyaran wajen nan da take wuni yi a kullum ya ishemu balle irin dawainiyar da takeyi da yaron nan . Ba wanu zancen raba kwana tunda rabon baida amfani mu dake nan da ita zamuyi ita su kuma da rana su dubashi dama ba yau ba na jima ina son yin wanan maganan. Don da gaiya za a shigo a bata wajen nan sai a barta da gyaransa ni abinku yana daure min kai yau ko auren kiyayya kukayi da yaron nan ai kwa tausaya masa halin nan da yake ciki haka ? Ai wa yan nan banjin zasu canza halinsu don na dade da fahintar hakan garesu ba kurciya bane ba kishi bane kawai dai rashin hankaline ke damun yaran nan iya ta fada. Tun wancan ciwon nasa na farko na dade da fahintar hakan tun karkice wanan Nusaiba sam kwakwalwanta baya ja karatunsu da suke kurin sunyi baida amfani a wajensu . Yau yaron nan koba mijinsu bane suke ganinsa a wanan halin ai duk mai hankali zai kara tsoron ubangijinsa ga hakan amma sam babu wanan a garesu sai sha,anin gabansu sukeyi cikin jin dadi da walwala kamar babu fitina irin haka a gabansu. Ku in kuna da hankali abin bakin ciki da tashin hankalin babba ya sameku a yanzu don bamu kadai wanan abin ya shafa inma kuna ganin mune da hasaran hakan kuje kuyi tunane kun fimu hasara kuda yake mijin ku. Ba kamar ke Nusaiban nan da wanan sakariyan mara hankali Saratu wace bata san ciwon kanta ba ban taba ji ko ganin dan uwan dakewa dan uwansa wanan halin da sunan so ba . Idan kinayi don wani manufane na zuciyar ki saiki matsa kiyi tayi dan uwankine dai jafaru kafin kisan Nusaiban nan Jafar kika taso kika sani ta dalilin shi kuma kika san Nusaiban . Kuka saratun ta fara sosai amma mama bata saurara mata ba daga mu har mama Dubu harma Salima duk mama din ta hada ta zagemu tas iya na tayata. Wanan ne dalilin da aka daina robon kwanan da akeyi din inda mama ta kafa dokan cewa sai su shigo su dubashi da rana zuwa goman dare bata bukatan ganin kowa a part din kuma. Daga wanan ranan komai ya sauya haka shima mai jikin a dan ganin sauki sosai ga lamarin nasa don dai yanzu alaman sauki yana baiyana a gareshi . Matsalan dai shine har zuwa yanzu din bai magana ba kuma motsi zai daiyi alaman yana son abu da idanu . Masu magani kuma kasuwan su ya bude a dauko wanan yayi bajintarshi wani yazo abu dayane ban fasa yi mashi amfani da maganin gidan mu ba din wanda daga iya sai maman tudu suka sani sai kuma ya habu da mahaifiyarsu. Kawuma yana zuwa dubanshi sai dai yadda iya kan zage tana nuna masa bacin rai yasa ya daina zuwa sosai yanzu din don ko yazo daga waje yake tsayawa wani lokacin bai shigowa. A cikin hakane wata rana ya habu ya shigo yana fadawa iyayyen nasa matsalan da aka samu da dukiyan yaya din dake can ikko . Ida yace zaije da kansa ya gano halin da ake ciki duk da bawai yasan komai bane akan dukiyan nasa amma dai zaije da kansa shida yaya Auwal zasuyi tafiyan sai wani abokin shi jafar din. Sun je din sai dai basu gane komai ba don da alama kamar dai dukiyan na shirin salwanta sun dawo a cikin bacin rai suna bayani ga iyayyen nasu kan abinda sukaje suka sama a can din. Wanan ya kawo cecekuce ga yan uwa inda wasu ke ganin kodai ya habu yabi bayane ya karbe dukiyan ba da sanin kowa ba. Wanan tsegumin daga yan uwansu na dakinsu ya fara fitowa har maganan ya dawo kunnen iyayyensu ranan maman tudu tayi fada sosai inda taketa ta,alka laifin hakan ga mama akan duk ita tayi sake da har hakan ke faruwa. Hakan yasa ya habu din yayi fushin zuciya yake fadin har na nan arewa da yake kulan mashi dasu zai dawo da dukiyan a tara a waje daya. Ana cikin haka Allah ya jefo Yazid a wani dare ya iso zaria dashi da iyalinshi ni dai ina zaune ina murza mashi magani a kafa naji ihu a cikin gida. Saida na saurara nagane ba fada bane wai ashe murnan zuwansune sukeyi saigashi anzo fadawa iya zuwan nasa iyan ta fita ta bar mu dagani sai mama tudu dashi. Ki natsu ki kara mayar da hankalin ki kinji yar nan insha Allahu ladan ki yana ga Allah shine kadai zai saka maki da alherinsa Allah ya tayar da kafadan mijinku lafiya. Nagane dani take yasa na amsa da amin tacigaba da fadin a kullun nikan ina gani sauki a cikin lamarin yaron nan kibar wa yan can marasa hankalin suje suyi ta gulma da zasuyi iya ka su zageni shine kawai amma ni ina da hankali ba zan bari a batawa yaron nan maganin saba. Ba tauyeki nayi na dora maki laluran nan ke kadai ba nasan kece kadai zaki masa abu tsakani da Allah uwarsa ma ta sani amma tana jin tsoron magana yasa na ari bakinta nayi hakan. Sallaman bakin nasune ya katse mata maganan take masu sannu da zuwa sau daya na dago kai na dubesu na mayar da hankali wajen abinda nake masa. Ya karaso yana fadin ya subbahanal dan uwa kaine a cikin wanan halin innalillahi wa inna alaihim raji,un maman tudu take fadin ai kaga sauki a yanzu yazid. Nan na juyo ina mashi sannu da zuwa ya amsa har lokacin hankalinsa yana ga dan uwansa dake kwance sambal a saman katifa Suna da matukar kama da yaya habu har kamar tasu ma ya baci don sai kace ko tagwayenesu da yaran nasa biyu sai matarsa da gabinta irin bakaken larabawan nan na sudan akwai kyau sosai gareta gaskiya. A nan dai muka gaisa da ita din don itama hankalinta na kan dan uwan mijin nata dake kwance nagama na gyara wurin na kwashe kayan zuwan kitchen . Nafito na samu iya ta dawo falon suna kara gaisawa yana zaune daidai satin kan dan uwan nasa dake kwance . Naji yana tambayab koya ganesu ita mama din ke fadin ya gane ka baka ga yana kallon ka ba yana murmushi. Wanan matarshi ce yake tambaya mama take bashi amsa da itace matarshi ta ukku sauran fa ya tambaya take fadin suna part dinsu. Zasu shigo yanzu tunda sunji kazo yake tambayab yanzu wani mataki ake ciki dashine mama munyi waya da habu yace min yana kaduna tun safe. To yazid matakin ke nan mu zubawa sarautan Allah ido kome Allah yayi daidaine don asibitin da kansu sun bamu shawaran agwada na gargajiya a gani suna zuwa kuma nan gida ana dubashi ko wani lokaci halin da muke ciki ke nan a yanzu. Wa iyazu billah ya fada yana girgiza kai ya mayar da kallonshi ga dan uwansa a lokacin ne matan yaya jafar din suka shigo yi masu sannu da zuwa ita Saiba ke fadin ashe kuna hanya bamu sani ba ? Yace mun taso tun shekaran jiya yau muka taso sai yau muka samu karasowa sannun mu da wanan halin da dan uwa ya shiga ciki suka amsa da sannun mu dai din . Kalman data fito a bakinsa shine shi kawu din yana zuwa dubab shi har yanzu iya ko kun hanashi zuwa don in ina nan ba zaizo ba ?