← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 306

Sashe 131

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

GIDAN IYA
Gidan iya kamar yadda na samu suna kiran gidan da haka suna isa da mota Saiba da Saare suka hango tsaye saareb na magana kamar cikin fada.
Ita kuma Saiban tana gyada kai ya kallesu yana fadin kingan suko yaya yarinyar nan Saratu na rasa meke damunta sam bata da tunane wallahi.
Saratu ai kowa yasani ita da wana matar taka kansu a hade yake ranan da aka kawo yarinyar nan saida Iya ta shiga rigan arzikin ta a cikin mutane tayi mata kaca kaca ta shiga hankalinta.
Suma a bangarensu ido suka zubo masu saidai basu daina maganan da sukeyi a lokacin ba har su yaya suka fito daga motan suka nufi hanyar part din iya suna wajen tsaye.
Shiya fito a karshe daga motan bai ko kallo inda suke ba shima part din na iyan ya nufa ya shiga suna wajen suna shirya abinda suke gani shine daidai gulmata dana yar uwata sukeyi ba wani abuba.
Inda Saare ke kara ingiza Saiban akan kada ta yarda ta ban daman da zan samu wurin shiga ga miji don nufin mu mugaje gida ko ?
Tunda mu mama ta haifawa yayanta inda saiban ke jin tankar taje gidan ta sameni tayi min tsinanen dukan tsiya don a ganin ta tana iya murzata idan ta samu gamina.
Sai saratun ta hana tace wanan su bari idan yaya ya bar garin ko ita zata rakata ayi hakan illa dai ya zageta dama an saba hakan ai kanta.
Tasan kuma mama ba zata kyaleshi ya sakata a gaba ba zata tsawata mashi sun dai dauki mataki a kaina lokacin.
Saiban ke fadin ita ta rasa me J ya gani a jikina da har yaje ya aureni ba tare da ya tsaya tunane ba ?
Keko aiba kai sake bane wanan abin da gani ai aikin asirine asiri mukai mashi muka sameshi ai daba haka ba ai ina ni inashi da za ace wai nice yake aure.
Gaisawa aka fara yi a tsakaninsu da iya mama dake daki taji muryansu ta fito suna gaisawan da ita lokacin shima ya shigo.
A,a gaku kamar tare kuke tafe mana kun shigo lokaci guda haka mama dubu ke fadan hakan .
Sai Anty Rukkaiya tace daga can gidansa muke ai tafiyan nasane dama munzone gun sarakan mu da kayan tausan gabansu.
Kaya kuma kayan tausan gaba kamar wani abin bin bashi tunda anyi angama haka ba wani shiri har wani kaya kuma za a zo sayan bakinsu dashi ?
Yau aka fara hakan idan mijinki bai maki bake shi yana da ra,ayin yiwa iyalinsa hakan kuma nice nan nasashi yin hakan gareshi ba wani ba.
Meye amfanin samu dama idan kana da zarfin yin abu kayisa a cikin lokacinsa tunka lokaci ya kure maka don wata rana sai labari.
Kwarai kuwa anty Rukkaiya ta fada daga ta karbe iya dake magana ai har yanzu mama dubu ana hakan ai silan zaman lafiya maigida yake nema ga iyalansa ga hakan.
Suna dai ta fadansu dagashi har mama shiru sukayi lokacin kowa da irin abinda yake tunane a zuciyarshi idan yake auna zancen mama da rashin son hakan da yayi din karara.
Ita kuma mama sai auna irin yadda dan nata ke kashin kudi akan zancen matansa ko wani lokaci har yaushe ya gama da zancen wanan auren daya dauko balle ya dauko wanan din ?
Ina kayan suke yanzu ta fada tana sauke ajiyan zuciya tana kallon yaya Ai don tasan halin Rukkaiya har take ita ba kamar Ai din ba.
Suna mota ta bata amsa sai lokacin ya dago yana fadin mama aina jima da sayansu tun lokacin dana hada lefen Rahama suma na hada masu nasu don ban garine ba a kawo masu ba.
Allah ya kyauta ta fada tana daukan jug din kunnun kamu da aka dama mata tun safe bata sha ba salima yasawa kira daga falon.
Ta fito tana gaidasu ta juya wajenshi yake cewa Salima kira saratu kuje mota kaya na nan bayan mota ku kwaso sai kije ki kira min su Asmau suzo nan.
A,a kaiko a can za a kai masu bakaji bahaushe yace tausan kirjiba a yaren mutanen sokoto wanan ai na ban hakkurine ba zasuce dai bakayi masu ba ai iya ta tare da fadan hakan.
Kai tsohuwar nan tasan komai wanan gaskiyane mu da mukai masu laifi aimu zamuje mukai masu har daki ko yaya Ai ke fadin hakan.
Salima dai tana tsaye yace jeki ku dauko salima ku kawowa su mama su gani kafin a mika masu ya fada yana kallon Salima din.
Ta samu saratun zata shigo don su gaisa da yan uwan nasu take fada mata zancen yayan nasu ta wani bata rai tana fadin kaya kuma kayansuwa kuma ?
Ni inana sani ta bata amsa a takaice ta wuce ta bata kara furta komai ba zuwa wajen motan nasa ta bude bayan motar da dama saida ya bude ya fito.
Dankari kayan su waye haka wai ta kara fada tana karasowa wajen motan ita dai salima takaicine ya kume ta sai gashi ya fito shiya taimaka masu ya fitar suna shiga dashi.
A tsakiyan falon iya suka tara kayan shiya shigo a karshe da wani daya dauko ya aje gaban mama yana fadin mama ga naki nan.
Yaya Ai ban fada maku tun can cewa wanan na mama bane wanan kuma nasu iya dasu salima ikon Allah kai Jafaru kace yan tausan gaban suna da yawa nikan naga abin da yawa.
Salima jeki wacan na wajen ki dauka ki mikawa matar habu duk suka kalleshi ya fuske yayi niyar hakan shiyasa ya fada a gaban kowa yaya Ai wanan nasu Asmau ne idan kun tashi sai su kama ku mika masu.
Ikon Allah lokacin abu ayisa kanina kayi kokari Allah ya saka maka da alheri anty Rukkaiya ta fada cikin nuna jin dadinta ga abinda dan uwan nasu yayi.
Kai haba ai hakan ya zama riya nime zanyi da wani kayan tausan gaban uwargida kuma da sauri Rukkaiya tace a,a keko maman Habu.
Wanan ai sai dan da yasan darajan iyayye da yan uwa yake wanan wani ai kome za aji bai dameshi ba albarka kawai a yanzu zaku saka mashi.
Sai lokacin ta sauke ajiyan zuciya tana fadin Allah yayi albarka an gode anty Rukkaiya tace Allah kuma ya basu zaman lafiya ya kawo zuria masu albarka a ciki muzo suna haka kafin shekara.
Ya mike yana fadin zan lekasu tare suka fita da salima daga part din ta dauki na Yanda ta nufi part dinta dashi cikin farin ciki.
Lokacin anty Rukkaiya ta mike tana fadin bari mu bude muga abin arziki muba ido abincinsa abu yayi kyau wallahi jafar kayi ko yanzu da mama ta yarda tayi wani aurene bayan baba ai a kara haifo muna irin jafaru bamu fushi.
Aka kwashe da dariya na mama aka fara budewa sai am barka sukeyiwa kayan turmi biyarne da lace har da dadduman sallah a ciki yaya Ai tace kin gani maman Habu a samu na muna addua kenan tana daga dadduman sama.
Turaren ciki suka dan fesa dakin ya dauki kamshi wanan aikin anty salma ke nan gaba daya an yaba komai a wajen .
Rigiji rakwaf inji hausawa don Asmau dake zaune a falon tare da maigidan don ita Saiba daki tashige tana jan kamshi.
Shiko tunda ya zauna bai daga daga wajen ba yana zaune tare da Asmau da yaran suna hira sai gasu suka fara gaisawa yaya Ai ke fadin ina yar uwar takine ?
Tana ciki ta fada tana kallon hanyan dakin Saiban ta yunkura ta mike zuwa kiranta lokacin ya mike ya shige dakinsa ya rufo.
Saiga su sun fito tare suka samu waje suka zauna ta gaidasu a tsatsaye da ina wuni suma suka amsa da lafiya.
Yaya Ai ta soma magana take fadin to Asmau Nusaiba gunku muka zo wanan kayan nakune na fadan kishiya aci da hakkuri don Allah.
Tsuweee Saiba taja wani tsuki da kowa wajen ya kallota yaya Ai cikin rashin damuwa da hakan take fadin hakkuri dai za ayi tunda shi kowa keyi abinda muka gada ke nan.
Da fatan zaku zauna lafiya da yar uwar taku itama daga can muke munyi mata fada daidai gwargwado da azauna lafiya don Allah tunda yanzu an zama daya.
Yaya Ai zaman lafiya kam ai babushi tunda tun farko ba a nemi a zauna lafiya ba yanzu daidaine J yazo ya auro muna wanan yarinyar a matsayin kishiyar mu ?
Haba dai don Allah ayi muna adalci mana don Allah abinda akai muna anyi daidai ke nan ga hakan ?
Yaya Ai tace adaiyi hakkuri dama hakan muka gada ai a rayuwan mu tunda mun fito musulmai Alhamdullahi ai kishiya inga hakkuri abokiyar zamace saidai wanda basu gane hakan ba .
Yanzu dai ga kayan fadan kishiya nan mun kawo maku don bai zaunu bane ba abayar a cikin lokaci ba a yi hakkuri don Allah.
Babu komai yaya mungode Allah ya bamu hakkurin zama da juna mun gode ai muna godiya ta mike zuwa dakinta itama nusaiban ta mike tabar wajen a fusace .
Anty Rukkaiya tace ikon Allah yar nan da karfin hali kike kuwa kema ai wata kika sama kika shigo kuma tayi hakkuri ba a hakkuri haka aka zauna dake ?
Ashe taji sai ko ta dawo tana fadin in ita taga tana iyawa ta zauna ni banga ina iyawa ba dama anzo a fada muna maganane a fakaice yadda aka saba ashe ?
A,a Nusaiba kar kice zakiyiwa su yaya rashin kunya a nan gaskiya Salima ta fada don tunda suka shigo da kayan ba wanda ya fita a cikinsu.
Wanan hayaniyar yaji ya fito yana fadin wai meye meke faruwane wai haka ?
Yana kallon Salima din .

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

4️⃣9️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
Chapter 131 · 0% Book details