Sashe 162
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
akanta nasan dan kauye bala,ine duk abinda ake fadawa bakauye gaskiyane ko wanan zancen auren naka waya zuzutashi ga uwarku haka banda ita da mijin nata ? Duk wani makirci da aka kulla nasan ga hansatu ya fito kallon su nakeyi kawai sai ranan da dubu ta gano gaskiyan zancen da idonta. Don yanzu kowa baida kima ko mutunci a idanunta banda dauda a duniyan nan ko kara dauda ya gitta dubu bata iya ketara mashi shi a yanzu na dauka zumuncine na tsakani da Allah sai yanzu na fahinci makircin hansatune hakan. Habiba taso muje falo na fada don wani zancen da suka somayi ba jin Biba bane harni wanan yasa na fadi hakan muka fito don mu basu waje su samuyin zancen da kyau. Aikuwa dai sun samu kuma har ya amaryar mata da abinda ke damunsa din inda yace mama taki fahinta a tsaya ai bincike kan zancen gashi duk inda yaje magana daya ake fada mashi. Jikin iyar yayi sanyi cikin damuwa tace Jafaru kasan da wanan maganan baka fada min tuntuni ba ta ina yanzu zan somashi dole a zauna dasu muji yadda abin yake ? Ka bari nasan yadda zan bullowa wanan zance din dauda dauda na fada maku kune baku san dauda ba ai komai dauda zai iya idan akace tunda yana rayuwa da muguwa. Kirikiri kaika sani saida Allah ya kawo rabuwan muna dawo gidanku da zama na samu sa,ida da kaidin wanan yarinyar duk da hakan ta riga tayi min illa a rayuwa saidai aina musulinci kawai a zauna lafiya. Abincinsa nan nakai masa yaci don har biba tayi barci a nan falo da muke kallo saida ya fito daga dakin na tayar da ita taje ta kwanta na rufo masu kofan dakin nina na sameshi a dakinsa. Washegari dole zan fita school ga kuma iya a gidan donshi tun karfe biyar natashi na fara aiki kafin gari ya haska na hada mata abinci har na rana na samu nashiga wanka saidana shirya na shiga mu gaisa da ita. Inda na sameta zaune a kasa tafi ganewa zaman kasan nake gani muka gaisa nake fadin zan shiga makaranta iya gashi zamu barki ke daya na wani lokaci a gidan . Allah dai ya tsare ya kare tayi min na koma kitchen na kwaso kayan abincin ta na kawo mata dakin na jera take fadin duk yaushe aikai wanan aikin haka yar nan ? Murmushi nayi ina fadin yanzu da safe nan na girka ai har na rana don kada infita in jima a can din ban dawo da wuri ba. Allah yai maku albarka ta fada tace kwarai magananki gaskiyane mijinku yana cikin damuwa yar nan jiya mun zauna dashi ya fada min komai kuma hankalina ya tashi. Tun za a ke shiri ba sai an dawo ba habu nake son yazo garin nan ina gidan nan ya tara min iyayyenku muyi zancen dasu muna kallo yaro zai halaka ba a dauki mataki ba ? Sam basu da tunane wallahi dan nan shine jigo a garemu kaf amma sun kasa tsayawz su fahinci gudun kada in makavjqra nace ina zuwa don ina biyewa zancen iya ba zan samu class ba ranan. Dakinsa naje na sameshi yana barci na fito wayan yaya ibrahin na kira shi yazo ya kaimu school ranan din ban tayar da shiba muna tsaka da lectures ya kirani yana fada na bashi hakkuri na kashe wayan nawa gaba daya. A gidan kawu fadane sosai sukayi ashe ranan da iya tazo gidan mu har saida mama dubu ta kaiga zuwa gidan don sulhuntasu inda take fada sosai kan yadda abubuwa suke taso mata a yanzu . Cikin fada take fadin abin yayi yawa mana zaman lafiya yana nema ya kaurace muna ayanzu shigowan yarinyar nan cikin mu ni bai min dadi ba wallahi. Na kula da zance nan nason zama gaskiya don tun ranan da jafar yace ya auri yarinyar nan Rahama abubuwa suke nemansu tabarbare muna. Ko sam hakan ba zai yuyu ba wallahi ba zan bari akan wanan abinda mutane suka camfa ace kan mu ya tarwase ba dole yasan yadda zaiyi da ita ya rabu da ita. Yar uwa mai karatu Ina kike tunanen wanan zance na mama ya fito da har mama din ta riks tansa bakin saratu data fara furta hakan a lokacin aurena da abin yai mata zafi take fadin . Iren fulani irin tsiya zasu tara muna a gida fulani da akace aurensu matsalane don sai gida ya watse ta dalilinsu shine su zasu kwaso muna su suna cika gida ? Ko ita yarta banda matsala da fitinan tsiya meta kawowa mutane ga ya habu nan kullum jiya wa yau ba a ganewa samunshi haka aurensu yake kamar auren buzaye wallahi baban wata kawarmu yayi ai mungani. A take zancen saratu din yayi tasiri a zuciyar mama don a ganin ta gaskiya saratu take fada don gashi habu dai ba ruwanshi da taimakawa kowa saishi da matarshi suke cin abinsu. Hakan kuma itama matarshi YANDA bata yarda kowa yasan sirinta ba balle aji a zauna gulma sai haushin hakan ya zamo biyu ya hade ga saratu din . Wani lokaci kiyayyan abin hannunka yanasa a kika, haka kuma kiyayya kan baiwa ko daukaka da Allah yayima yana sa mutane suji sun tsaneka. Abubuwa da dama suna saka mutane sukika saboda hassada da bakin ciki da kyashi da sukeji naka ,wani lokacin kuma rashin gamon jini nasa kaji haka kawai ka tsani mutum a ranka irin wanan yana cikin dabi,an saratu don idan mutum bai mata ba zata fara bakin ciki dashi dole kuma dole kaida ke tare da ita ka nuna kaima baka kauna wanda ta tsana din. Exam din mu yazo dole na maida hankali ga karatuna idan na fita gida sai yamma zan dawo gida cikin irin haka wata rana shi yazo daukana lokacin matarshi nada sati biyu da haihuwa. Bayan mun kama hanyane naji yana fadin Rahama ina ganin yau a can gidan zan kwana ba sai kinyi girki ku dani ba. Duk da naji zancen a bazata amma na daure ina fadi a fili Allah ya bamu alheri iya abinda na iya fada a bakina kenan lokacin. Shiru ya dan biyo baya kafin yace mama ta matsa min akan Saiba ta karbi girki zuwanta biyu ke nan gidan ki wajen iya akan hakan yau iya tace bayi hakkuri nabi abinda take so din. So don Allah kada ki dauki hakan wani abu a zuciyarki haba dai yaya ni hakan ma yayi min dadi don laifina da ake gani kan hakan ? Na banza tunda sunsan bakece kikasani yin hakan ba ai duk wanda zai zageki ya rage maki nauyine ya daukarwa kanshi alhaki don ra,ayinane naga daman hakan. Ko yanzu kuma hakan bashi zaisa ta samu yadda take so a gareni ba na fada masu har Asmau din ta karbi girkin ta . Allah ya kyauta na fada ina gyara zama cikin dan siririyar murya sai naji yace me kuke bukatan a sai maku ne a gidan ? Dan kallonshi nayi nace ba komai kamar a hasale yake don yadda ya hauni da fada yana fadin ya zakice ba komai ? Komai ke nan kuna dashi a gidan nace to yaya me zance tunda nasan komai muna dashi yanzu saidai in za a karo munane mun gode amma ba abinda babu gaskiya. Alright bari in naje masu sayayya sai a hado da naku barin saukeki sai in fita in duba abinda ya dace kinsan iya na gidan yanzu. Duk da nasan banda matsalan hakan don kina iya kokarin ki a kansu amma ina son ki kara kula don Allah iyace makamina Rahama kin sani idan ta tsaya muna komai zai tafi yadda muke so don haka nake son ki kara kula don Allah har ta gama zaman ta kada ki yarda a samu wani matsala daga wajen ki please. Ni dai banda insha Allah ba abinda na iya fada lokacin don na fahinci kamar akwai matsala ko kuma ranshine a bace dai yake hakan. Koda ya saukeni bai shiga gidan ba ya juya ya fita na shigo na samu su iyan da Biba a falo zaune gaidasu nayi na zauna suna min sannu da dawowa. Bayan na zaunane take fadin aina fada baki tsayawa ko ina yanayin karatunkine kawai haka amma baki barin mu da yunwa ko wani abu. Dazun uwarku tazo gidan nan naji dadin da bata sameki a gida ba duk da taso ta dauki hakan da zafi ta juya zancen da wai baki zama gida ? Nace ba inda kike zuwa banda makaranta ai tazo ranan da ba karatu idan bata sameki gida ba wai banson a fadi zancekine nace hakan. Wa yan can gantalalun da take magana meye amfanin zaman gidan nasu ba moriya ke ai neman abinda zai zama maki alheri ga rayuwa kike fitayi. Su kuma fa da zaman gidan bai amfana masu komai sai komawa baya a kullum miji na kumsan bakin ciki a kansu. Batayi fadan hakan ba sai ke da kike fita gun amfanin rayuwanki su yayanta da sukai karatun har wani gari waya matsa masu ? A raina nace aisu yayantane basu laifi niko tsintana sukayi daga sama dole ta kyashewa karatuna din don tun farko ai bataso hakan ba Allah dai ya nufa da sainayi kuma in zauna a karkashin danta da bata so. Ni dai a fili mikewa nayi ina dariya nace iya bari in dan rage kayana in watsa ruwa na nufi dakina ina kwalawa biba kira data dauko min ruwa insha. Naji iya din na mata fada akan hakan da bata ganin yadda nakewa duk wanda ya shigo ai kaba mutum ruwa arzikine ba sai ya roka ba. Wanka nayi na fito na zauna ina cin abinci muna dan taba hira da iyan take fadin mijinki ya fada maki yau matanshi zasu karbi girki ko ? Don sun kaishi kara yafi a kirga wai yazo ya tare a gidan ki ya fita batunsu nace yayi hakkuri ya koma can din Allah ya isar masa da duk tsiyar da zasuyi mai tunda haka uwarsa ke so. Ga abin magana da zata tsaya tayi magana akansa ta kasa sai inda ake ganin mutuncinta nan take neman