← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 306

Sashe 121

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayansa yai kara alaman kira ya daga yana fadin ina gari ai jiya na dawo gani fitowa yanzu insha Allah ya gama wayan ya kallo Habu yana fadin musa ne ya kira zan fita yanzu muna son muje mu gana da mai,martaba dashi kan wani zance. Lokacin kawu da ya kasa motsi ya dago yana fadin ai baka tafi ba ba a san yadda za ayi da kudin nan ba yanzu Jafaru ? Yace a,a kawu ayi yadda ya dace a kasa kudi dai anga yadda suka kama ga takardan nan Habu sauran bayani suna ciki kaima kuma nayima bayani a baya. Akwai gina dana dora dakai da Yazid wanan nayi niya ba zan fasa ba in sha Allah don ma wanan gidan da zan maida matana a can da ake gyara da yanzu na kammala maku ginan ai amma na dakatar ina wanan gyaran a yanzu. Duk dai wani bayani leter on zakaji idan mun zauna yanzu barin je in samu musa mu karasa dashi don tafiyan nada muhinmanci sosai a wajena. Har ya daga ya juyo yana fadin anty baraka yau ne zaki tafi idan an raba ko kina nan tukunna ? Kafin tayi magana iya ta karbe da fadin yoo me zata zauna yi an raba an bata kasonta tunda dama donshi tazo mijinta nacan yana jira ta kawo mai kasonta shi da yayanta ai gara dai ta tafi tun yau din zai fi ai ? A gaskiya mama zamu samu matsala fa da Iya ni kadai iya ta gani da zata tsargeni kan zancen nan in ma tsarguwane ai saratu ya kamata ki tsarga iya bani ba ita data daga waya ta kirani inzo ga halin da ake ciki. Amma in aka tashi magana iya tace waini haba iya kada ki hadani da dan uwana mana don Allah ? Iya tace ai ke kikazo da zafi kina sakina sakin magana akan dan uwan naki yanzu aikin fada da bakinki cewa ga haddasanar data jawoki ta fada maki karya da gaskiya kuka hau ke da iyayyen ki da suka biyewa haukan ku. Har cewa kikayi a nan jafar baya taimaka maki da komai a rayuwa sai kin rokeshi amma baki fadi alherin dan uwanki zuwa gareki ba sai yanzu daya fada a gaban mu. Nina sani kuma na fada ko a bayanshi jafar namijine namijin dutse da ba a gane gabanshi sai dai bayanshi . Yaron nan kamar yadda ya fada yana iya kokarinsa wajen ganin ya daga gidan nan ya kare martaban kowa amma kuka fahinceshi a mumunan zato irin haka ? Yanzun dai aiga kudin nan ya aje maku agaban ku sai ku rike kuda kuka fishi iya rikon ya dai fita bakinku yanzu kan ya cinye kudi ya handame komai shi kadai yana aure aure yanzu sai ku samu sabon camfi ku zarga mashi kuma tunda kun zama yan sheri. Kai dauda ga kudin nan sai ka dauka tunda hakkinkane yadda naga ka damu akan zancen nan bai kamata yadda kake da yaron nan ace ka goyi bayan haka gareshi ba ai. Nifa iya ba goyon baya nayi ai masa wani abu ba illa goyon bayane tunda masu abu suna bukatan abinsu ai masu abin kafisu bukanshi nake gani iya ta fada. Habu ya mike da niyar fita lokacin mama da jikinta yai sanyi ta kasa magana tace kai kuma ina zaka ana batun kasa kudi shi ya fita yace yana da uzuri kai kuma zaka fita yanzu ? Mama ai dole sai an kira malamai a cikin harkan nan bamu zamuyi bugun gaban mu ba wani yazo daga baya yace an cuceshi kuma. Zanje tudun wada in dauko su malam idi suzo a yi yadda shari a yace bayan sunji abinda kowa ya mallaka da farko aka hada akai wanan abin. Wani malam idi zaka kira anan ko iyamu bamu isa mu fasala kudin nan ba ba tare da mun kira wani bare ya shigo ba kawu ya fada. A,a kawu Allah yace Annabi kuma ya fada ya umurce mu dayin adalci a cikin lamarin mu don haka kudin nan ba wanda zai tabashi sai masana sunzo su kasa subawa kowa nasa a hannunsa kamar yadda yake a shari,a. Kuka mama tasaka ta mike zuwa daki wayan habu dake ta haske a hannunsa ya kasa dauka saboda maganan da yakeyi a lokacin. Anty Baraka ke fadin wayan ka habu tun dazun ake kiranka fa ya kai hannu ya dauka yana fadin yazid ne ashe ? Ya daga wayan yana sallama yace yazid ya akayi suka tsaya gaisawa sai ya saka wayan a hands free kowa naji yazid din yace zancen kudi idan an raba a mayarwa J da nawa kason yacigaba da juya min sai nadawo. Nima yaya na fadama abawa yaya J ko kai nawa salima ta fada daga gefe kawu ya dago kai ya kalleta tace kada abawa kowa nawa abarshi a hannun ku don Allah. Kai wanan abin dame yayi kama yau ace yanda yaran nan suka taso maku a cikon biyayya wai kune kuma masu raba kan yayan nan yanzu ? Ban taba zato ko tsamanin haka ba gareku dubu yau ace kune kuka fitowa yaran nan da wanan lamarin don mutum daya ko biyu zuwa ukku sun zugaki suna son ganin farincikin ahalinki ya ruguje. Yau badon yaran nan wasu nada hankali a cikin su ba kin hada fitinan da koke baki iya rabashi dubu saukin abindai ba a taru duka an zama daya ba. Bayan fitan su da salima na kwashe kayan abincin daga dinning zuwa kitchen na tsaya ina wankewa nan anty Nafisa ta sameni a kitchen din. Muka gaisa take tambayana yayama ya fitane nace tare suka fita da anty dazun nan muka tsaya muka dora abincin rana wanda muka hada sakwara dakan hannu tunda ba wani yawa garemu ba leda hudune har maigadi itace ta daka nayi miya muka gama nashirya komai kafin mu shiga daki yin azahar. Daga nan na dan kwanta don in huta sai wajajen karfe hudu saura ya dawo gidan shima a gajiye ya shigo don tun fitansa bai samu ya huta ba yana ganawan da yace zaiyi din ya fito mutane kuma suka taru akansa. Tunda sunga har yayi matsayin da zai gana haka da mai,martaba to lalai yaron akwai kudi ko ilimi a wajensa ke nan dole dai yana da madafa. Irin kudin daya basu yasa suka gaskanta hakan da suke zargi ana tambayan dangidan waye ana fadi suka gane mahaifinsa kowa waye shi agarin. Ina kwance anry Nafisa ta shigo dakin tana fadin Ramaah ina son inje gida in dan leka su inna kada ace nazo nan na zauna kuma . Haba dai anty amma zaki dawo ai na fada da sauri tace bako yau ba sai idan yaya baya gari kada inyi rashin hankali mana Ramaah in yaya ya girmeni aike baki girmeni ba ? Hankali kuma hanjine ai mai yasa kikaga ya raboki da gidan yawa ya kawoki nan ke kadai aidon ku huta dukkan ku yayi hakan na noke fuska ina murmushi. Tace to kingani in sha Allahu idan bai gari nayi maki alkawarin zuwa har in kwana amma yanzu kan nima ina son dan uwana ya samu natsuwa a rayuwanshi ya gane yayi auren zamani shima irin na sauran maza. Na mike tsaye na sake fadin da kijira yaya din ya dawo sai ya kaiki mana tace ai banson ya dawo ya sameni dinne yasa zan wuce yanzu. Don Allah Rahama kiba marada kunya ga wanan aure ido aka saka aga matsala koda kadanne kema daga wajen ki ace mashi gwai don haka ki daure ki koyi son shi a zuciyarki. Har duk wani abinda kika iya ta bajinta ki gwadawa yayashi Rahama ki kawar da kunya dajin nauyi a yanzu shi mijinkine ba wa ba don haka saikin zage kin dai san bakin ramin kura kike. Haka kuma ki kara hankali da mu yan uwansa kindai san komai za azo a dinga bukin cikinki kamar da gaske sonki akeyi sai idan anji sirinki a koma bayan ki ana zunden ki. Duk abinda ya shige maki kai ki kirani in sha Allahu har idan na sani da yardan Allah zan haska maki shi a yanzu zan nisanceki kada a zargemu amma akwai waya na nan komai ke nan zamu dinga waya dake in sha Allah Na dago kai cikin yanayin damuwa ina fadin nagode anty Nafisa a gaida ummu amma ina zuwa don Allah na fada zuwa dayan dakin dake rufe turmin zani na dauko mata da wani dogon riga sai su sabulai da turare na dibo kayan buki mai yawa na kawo mata ina mata godiya. Har bakin kofan falon na rakata tace na tsaya nan ta tafi na sauke ajiyan zuciya na juya zuwa ciki ko ina na gidan nabi da kallo wai yau ni Rahama nice ubangiji yaiwa wanan baiwan a lokaci guda haka. Alkawari na dauka zan zauna da yaya tsakani da Allah in masa biyayya kamar yadda shari,a ya kidanyawa mace tayiwa aure biyayya kamshi na fesa a falon har zuwa dakinshi dana shiga ns gyara mai hakan yana daga cikin abinda ke hadashi fada da matansa nasani yasha korafi kuma a gabana cewa ko muhalinsa babu mai iya gyarawa a cikinsu sai inya gyara da kanshi. Na koma daki ke nan na tayar da sallah naji dawowanshi bai shigo ba sai daidai na idar ya shigo har dakin nawa da sallamanshi na na shafa addu,an na juyo ina amsawa tare da furta sannu da dawowa a gareshi. Yauwa amarya ta yaya kike ya amarci kuma ya fada yana karasowa inda nake zaune saman sallayata ya rage tsawonshi zuwa tsugunni yana fadin ya gidan Rahama hope ba matsalan komai dai ? A,a bakomai na fada ina kokarin dagawa ya mike yana miko min nasa hannun alaman in kama in mike ai zan iya na fada . Baki son na taimaka maki ke nan ya fada a,a kada dai in wahalal dakaine kawai banso amma da karfina ai zanyi iya mikewa. Wayau ko ya fada to ban yarda ba ya fada banyi aune ba sai naji ya sukuceni baki daya zuwa bakin gado dani ya aje zakice ba yaya Jafar bane a lokacin. Hijjab din wuyana daya kula ya
Chapter 121 · 0% Book details