← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 180 OF 306

Sashe 180

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yan gidansu dana hango a wajen yasa na doshi emergency din kai tsaye takawa nakeyi amma bansan inda nake takawan ba har nakai wajensu. Suna min sannu da shigowa ga kallon tausayi karara a fuskokinsu inda nikan har lokacin zuciyana sai harbawa da take min tana wasi wasin ko waye a wajen ? Ganin yar uwata dake cikin taron yan uwa yasa na dan fahinci bata ita bace kuma ba mijinta bane ras naji lokaci guda da matansa da suka iso a daidai lokacin suma hankali a tashe. Wuni sukayi don na tsaya gaidasu yaya isah dake tsaye suna magana da ya Habu suka amsa min hayaniyar da saiba keyi tana fadin akan me ba za a bari mu shiga muganshi ba ? Wanan yasa ya habu katse maganan da yakeyi ya doshi wajen hankali a tashe yana fadin ke Nusaiba kada kiyi kokarin daga muna murya wajen nan fa ? Kowa da kika gani wajen nan abu daya ya kawomu nan saboda shi muka zo nan din kowa kuma yayi hakkuri yabi dokan likitan . Ko in an barki kinshiga suna aikinsu da abinda zaki mashine a yanzu wanda yafi nasu din don haka kada ki kawo muna rigima a wajen nan don Allah ? Har na taka nakai inda su maria suke tsaysaye din cikin damuwa a cikin yare nace yayane ko ta amsa min da shine tana rike hannuna . Cikin yare take fada min in natsu in kwantar da hankali Allahne mai komai kada inyi abinda zan zubarda imanina a gaban mutane don Allah. Yanzu likitocin nan suna dubashi ne su can sunce basu ga komai ba shine nan suke nasu kokari ko zasu gano abinda ya sameshi din. Ajiyan zuciya na sauke ina bin bangon dake bayanta nakai tsugune a wajen tare da noke kaina cikin gwiwana salima ta dafani tace kiyi hakkuri ki natsu kinji Rahama don Allah. Kamar dai irin ciwon nan nasane na baya ke son taso mashi amma wanan karon ya canza sallo ne yazo mai da wani nau,in kuma . Ruwan dake hannunta na mika hannu na karba na dan tsiyayya na shafawa fuskana ban sauke idona akan kowa ba sai mama dake zaune a kasa tayi tagumi a cikin tashin hankali. Kallona ya koma kan saiba dake fada har lolacin saidai ba cikin daga murya ba haka nayi tabin mutanen wajen da ido ina nazarinsu daya bayan daya a takarshe idona ya tsaya kan Saare dake magana tana murmushi na juyo a hankali na dubi yar uwata ina fadin . Akan me zasu kawoshi asibiti Yanda bayan sunsan ciwonsa bana asibiti bane komene ai mama ta sani da kawu . Maman dana ambata da kawu yasa salima kallona itako maria sai fadi take ta fada min kada inyi wani abinda zan jawa kaina matsala fa. Koma meye ga yaya Habu nan ai dole zai dauki mataki ba zai kyalesu ba shima don haka inyi shiru kawai don Allah. Itako salima din cewa tayi dani ai mama tunda taga halin da aka iso dashi take zaune wajen nan bata daga ba don baki cewa yana da rai fa ko motsi yaya baiyi Rahama idonsa a kafe suke waje daya. Innalillahi na ambata a cikon tashin hankali ganin an bude kofan yasa kowa kallon likitan daya kira ya habu suka nufi hanyar office dinsu dashi. Ya dan jima a wajensu ya dawo tare da likitan lokacin ya habu din kewa yan uwansa bayanin abinda likitan ya fada. Su maza suka fara shiga saibama ta kusta sai naji maria ta rike min hijjab dina na dago na kalleta don na yunkura na tashi nima tsaye lokacin. Ki bari su shiga ai dole ya habu ya bari ki shiga ki ganshi a natse wanan yasa na tsaya ba don naso ba zance kusan mune karshen shiga wajensa din. Kuka masu kuka keyi irinsu saiba sai da wasu yan uwa tunda naga yanayinsa naji duk jikina ya mutu a wajen muryan ya lawal naji yana fadin tun a can fa haka yake bai motsi bai komai ko ka nuna hannu da alaman ma bai san kayi ba. Komai ya bace min akai sai wanan kalman ta (Lillahi ma,fis samawati wama fil ard) shine abinda ya fado min a zuciyata lokaci guda nake faman nanatawa a harshena. Na doshi wajen gadon da yan uwa da matansa suka zagaye ku dan bata waje ta isa wajensa don Allah ya habu ya fada daga bayan mu hakan yasa wasu juyowa suna kallona. Har na karasa ban iya furta komai ba sai wanan kalman daya tsaya min a saman baki don komai ya bace min a lokacin. Shi din ma daddy Abuja ya koyar damu hakan aduk lokacin da wani abin damuwa ko furgici ya shigemu dashi na taso a bakina don haka kila yayi saurin zuwa min a kaina ayan karshe a cikin bakara. Tsaye nayi ina mai kura mashi ido tare da nanata kalman a cikin bakina sannu a hankali na kara matsawa kusa da iya ina fadin sannu yaya Allah ya baka lafiya ya sahalema wanan halin daka tsunci kanka a cikinsa. Magana nakeyi amma abinda iya da yaya Isah suka fada lokaci guda yasa nayi shiru na kurawa bakinsa din ido don cewa da yaya Isah yayi wallahi ya amsa mata adduan nan da amin. Wallahi bakinsa yayi motsi kuma wallahi amin yace da sauri mazan suka matso sukace yayi magana fa kace iya tace kwarai ya amsa nima naji hakan wallahi. Dama likitan yace a gwada kawo mai na kusa dashi agani ko za,a samu reaction indai hakane kuwa dole Rahama zata tsaya kusa ke nan . Yaya Auwal ke fadin hakan ki kara magana mugani ko zaiji don Allah yaya isa ya fada daga gefena din. Saida na dan kara matsawa kadan na rankwafo nace yaya kana jin mu don Allah idan kana ji ka dan nuna alaman hakan ? Nakai hannuna na shafa fuskansa a hankali yayi wani irin ajiyan zuciya mai karfi da kowa ya firgita saina fashe da kuka na kifa kai a jikinsa. Ku dagata kawu ke fadi daga inda yake tsaye muryan iya ne tace ku barta dashi hakan na dan lokaci mu gani ? Hawaye yakeyi fa yaya isah din ya fada hakan yasa wasun mu da dama kara kuka a dakin har iya duk dauriyanta saida ta fashe da kuka ta soma fadin. Allah ya saka maka Jafaru ga dul wanda ya sakaka cikin wanan halin ubangiji yabi maka hakkinka akan mai shi ga alamu sun nuna karara akwai wani boyayyen lamari a cikin matsalanka. Duk wanda ya sanka yasan a yan watanin na baka daidai kamar kulum kana yawan fada min iya banda lafiya ni kadai nasan yadda nake ji a jikina . Iya bana barci wani lokaci har tunane gushe min yakeyi iya ina jin na kusa barin ku wallahi tana kuka sosai take fadan hakan. Iya ki daina wanan maganan don Allah ai sai a dauka ba ayi imani da Allah ya kawo mashi hakan ba imani ya kamata ace munyi ayanzu ba irin wanan zancen ba don Allah ? Me kake son in fada akan abinda nasan shine sila akan matsalan yaron nan dole in fada tunda abu ko yaushe sai kara gaba yakeyi akansa. Kiyi hakkuri iya in sha Allahu za a dauki matakin hakan ya habu ya fada nikan a hankali nayi kokarin dagawa daga jikinsa amma sai naji kamar hannunsa dake sarke da nawa ya dan rike hakan yasa na dan dago ina kallonshi. Tabbas hannun nasane ya rike min nawa a hakan da yake din na bishi da kallo kamar yana son kifta idanunsa saidai ya gaza hakan a lokacin . Na fahinci yana kokarin yi min yadda yake min ne lokacin da yake da lafiya idan mun kasance a hakan dashi nayi yunkurin dagawa daga jikinsa zai rikeni ya hanani wani lokacin yace mu tsaya a hakan dashi shine yanzu abinda yake kokarin yi mi a lokacin. Muryan Asmau naji a bayana tana fadin sannu yaya J Allah ya baka lafiya jin hakan yasa na dan dago ina fadin ga anty Asmau nan yaya tana gaida kai. Hannuna na zare na hada da nata dana kamo na daga daga wajen takai zaune inda na daga tana mashi makamancin abinda nayi mai din a lokacin. Idanuwa kur akan mu dakin yayin da saiba ta karasa itama ta zauna kamar yadda Asmau ta zauna din tana maganganu gareshi. Dole kowa zai tausaya a wanan halin ga dan uwa a cikin wani hali babu mai halin ko ikon kwatosa daga jerabawan nan sai Allah sarki buwayi gagara musali kafai yakai ya kwato maka dan uwan daya fada cikin irin halin nan. Kuka ka munyi shi har mungaji mun godewa Allah mun koma muna rokon Allah ya bashi lafiya sai dare karfe tara na bar asibitin zuwa gida. Koshi yaya habune da yai tsaye a kan mu cikin daure fuska yake fadin duk mu fito mu wuce a kaimu gida babu wace zata tsaya a nan cikin mu . Za a bar iya da yaya Auwal da yaya isah su zauna dashi a ranan naga dadin kyautatawa yan uwa da yaya J keyi don suma sun nuna mashi kauna kwatankwancin yadda yake nuna masu din. Tare da yanda muka bar asibitin a motarsu suka saukeni gida tana ban baki da lurar dani na dangana nayi aikin hankali. Don taji an fara surutu da tsegumi wai duk halinda yake ciki saida nazone yayi motsi har aka gane wani abu a gareshi. Kinga ke nan suna nufin wani abu ke nan a kanki yanzu kwarai kuwa nima naji suna fadan hakan wai badon zuwa ta ba ko motsi baiyi ba tunda suka daukoshi tunma a can din da hakan ya sameshi Nasir kanin su yaya din daya dauko mu yake fada. Maria tace na kula suna son kawo wani zance ga hakan sai tace amma ai yaya Isah yace itace ya kamata ta zauna tayi jinyarsa idan hakan ya taso . Saidai sunsan wanan matar tasa yar kaduna zatayi fitina akan hakan amma yaya Habu yace a barshi da ita kawai yanzu naji suna maganan idan anga asibitin baiyi sai a koma gida a cigaba dana gargajiya. Sun dan jima a gidan
Chapter 180 · 0% Book details