Sashe 63
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai daren sallah ya J ya dawo zaria don haka Habune ya gudanar da duk wani shirin sallah a gidan kamar yadda al,ada yake ga musulmin bahaushe. Part din iyayyensu dana yayanshi komai ya tanada musu a nan da daren kuma ya dauki mama ya mayar babban gida inda tace dakin mijinta zatayi sallah tare da yan uwanta. A can ma suyi hidima sosai daga sutura kudin cefane shimkafa dasu mai duk Habu yakai masu kowa nason samun albarka duk da karfin abin Jafar ya turo da kudn yi amma ya dora da nasa don samun akbarka. Nama kuwa a can aka kada shanaye biyu kamar yadda mahaifinsu keyi a baya shida mutanen unguwa a hada a saye a raba ko idan kana da hali ka yanka kai daya ka bawa wa,yanda Allah yaci dasu rabonka. Suma wanan karon dai sunyi hakan shanu daya nasu da babban gida daya kuma mutanen unguwa da yan uwansu masu aure aka yayyana sai albarka ake saka masu da fatan gamawa lafiya, Allah yasa mu dace Allahuma amin. Duk,da da dare mama dubu ta dawo bayan shan,ruwa hakan bai hana mutane suji dawowanta ba suka dinga shigowa masu godiya nayi masu yan koken abinda zasuci ta bude shimkafanta aka dinga diban mata don yanzu Nafisa idan mama bata nan itace ke zama a part dinta don haka koda ta dawo bata koma wajen uwarta ba nan mama din tace su zauna tare da ita. Saiga Jafar ya shigo wanda dawowanshi ke nan ya dai shiga gida sun gaisa da iya da matarshi Asmau daya samesu a waje da wasu mata da iya biyu da iya tasa aka dauko daga unguwarsu su taimaka masu da aikin gida dan aikin yayi yawa. A ranan Ramaah tasha ambata a bakinsu saidai ba Ramaah don tana can inda aka san darajanta wurin da ko kamshin aikon da akeyi bana ji saidai a debo anunawa matar gidan ko yayi idan bata nan kuma nice zasu tambaya ko yayi ? Tunda ya shigo ya zube saman kujera ya dafe goahinsa da hannunsa daya uwarta dubeshi tana fadin lafiya kake kuwa Jafar ? Saida ya nisa ya sauke hannu ya dubeta da idanuwansa da sukai ja jajir yake cewa uwar kansa ke masa wani irin ciwo wani irin ciwon kai da bai taba jiba yakeji da kyat ya iso Zaria yan,zuma dayasha ruwa saida ya hade magani ya samu fitowa. Allah ya sauwaka uwar tayi mai kafin ta dora da fadin aidole kayi ciwo Jafar tunda baka hutu ga azumi ga yawan tafiye tafiyen da kukeyi ga rana da zafi. Cikin karfin hali ya murmusa yana fadin dolene mama idan ka zauna sai a cuceka ai tafiyan da sauki tunda da jirgi nakeyi bada mota ba. Sallama akai mai ya fita wanan yasa bai dawo ba ya wuce zuwa gida da kyat yakai gida zuwa dakin shi cikin dare ya kira dan uwansa Habu da waya dole sukaje asibiti dashi a daren. Allurai akai mai da magani masu karfi aka bashi suka dawo gida don zaiyi barci sosai akace idan yasha maganin . Ba wani barcin ya samu ba amma ya danji sauki sosai zuwa safe haka yai karfin halin zuwa sallah idi a dadafe ya dawo gida ya kwanta. A kullum isan sunje sallah a ka,ida zasu wuto gidansune direct su gaida iyayyensu da makwabta da ake zaman arziki da iyayye tare da sauran yan unguwa. Wanan sallah rashin ganinsa yasa ake tambaya anan mutane suke jin baijin dadin jikinsa abokansa suka fara tururuwan zuwa gaidashi harma da manya. Mama dubu sunzo da abokan zaman ta da Habu ya kwasosu sunzo gaidashi suga yanayin jikin nasa suka sameshi a falo zaune inda abokansa suka barshi. Suka shiga yi mashi sannu da jiki basu jima ba don sallahne aka mai dasu gida har mama din don tabar Nafisa tana mata aiki a gida. Zuwa yamma kuma saiga Habu ya kirata yana sheda mata zasu koma asibiti da zafar don kan nasa ya matsa da ciwo. Sai lokacin hankalin mama dubu din ya soma tashi da zancen ta fahinci wanan abin ba karamin abu bane ke nan tunda za a koma asibiti kuma again . Da zatazo Nafisa ta boyota suka zo tare don asibiti suka nufa suma a lokacin suka samesu a can kai dai yake fadi yana mashi ciwo sai dafe kan yakeyi yana juye juye cikin damuwa da yadda yake jin wani irin azaban ciwo . Tun safe da nayi wanka na bude ledan kayan da aka sayo min din ina duba wani zan saka a jikina cikin jallabiyan dana ya saya min din. Don bandasu banda wasu sabbin kayan da zan saka a jikina lokacin inyi fitan sallah dasu na azo agani haka masu kyau gashi zamu tafi sallah idi gidan. Tsab kayan suka karbi jikina simple makeup nayiwa fuskana nayi rolling din gyalena ka,idan anty Salma nabi da take fadin idan zan fita na gyale kawai zan sakawa dan kamshi mai taushi yadda ba kowane zaiji ba sai idan nabar wajen za a iya gane hakan. Ire iren roll on oud din data ban na murza na koma gaban madubi ina kallon kaina a cikinsa ni kaina a ranan nasan na fito diya mace sak dani. Kila rabona da tsayawa inyi kwaliya irin hakan tun ina karama a gidan daddy da anty salma da hjy suke tasa mu a gaba dole muyi gyara. Don acewarsu ba a ganinsu fes a samemu a kazance cikinsu don dole ake gyaran mu fes a lokacin a gaskiya wasu mutane tun a duniya kake sanin su din na dabanne . Don wallahi nidai ba zan iya ko kwatanta alherinsu gareni ba tsakani da Allah bansan ta ina zan soma fada ba gaskiya saidai haka a ciki labari na dinga tsankwaro alherinsu garemu. Rita yar aikin antyce tazo kirana wai idan na shiriya in fito inji anty din nace gani tafe muka fita tare da ita na jawo kofata muka fice a dakin. Falo na samesu zaune harda mijinta da yaransu biyu ko wanin su yasha kwaliyansa gwanin ban sha,awa dasu sai photuna sukewa kansu . Gaida mijin nayi wanda anty salma tafishi hausa sosai a bakinta yake fada cikin hausan da bakuwar fulani kina gidan nan yau nake tambayan anty ki ai? Akwai wasan barebari da fulani shi yakan so ya zolayeni da hakan amma ban saba da in sake da mutum haka inta zuba ba saidai inyi murmushi kawai in soke kai. Na fita daban a cikinsu donsu bakakene sosai ni kuma din bafulatana don haka da gani ba sai an tambaya ba za a gane ba hadin kifi da kaska. Bamu jima ba muka fito shi ya dauki dan nasu babba na dauki karamin muka nufi wajen motanshi kusan kowane a gidan za a tafi mota biyu nagani a jere don haka aka bar mutum biyu sune basa sallah ta musulunci a ciki mu. Mota daya muka shiga dasu ni ina baya da yara su kuma suna gaba zuwa idin da baida nisa sosai mun samu an kusa tayar da sallah don haka bamu waji nima ba aka tayar da sallah. An sauko lafiya muka nufi mota aka dawo gida sai lokacin akewa juna barka da sallah gwanin ban sha,awa kudi masu yawa mijinta ya bawa kowa na gidan sai ince nawa yafi nakowa yawa a cikin mu har wa yanda basu sallah su Rita an basu goron sallah a ranan kuma ya wuce maiduguri wajen iyalansa nacan. Don ita tana tare da mahaifiyarshi bata zama a abuja sai maiduguri din a yadda anty salma ke fada min bayan wucewansa take fadin shine dalilin aurensu don ita ta zauna a nan Abuja kuma zaman nasu gaskiya akwai sauki sosai don kusan dukkansu yan uwane dama. Abincine na alfarma muka zauna akaci kafin dan wanan jigilan kowa ya nemi wajen hutawa don sun fita zata saukeshi a airport saina koma dakina na kwanta. A ranan na gwada amfani da wayana wajen kira layin nan na cikin wayan da bantaba kiran kowa a cikinsu ba na danna na salima yayi ringing gab da tsunkewa ta daga tana sallama tare da tambayan waye ? Nice Ramaah na bata amsa daga bangarena sai naji tace a,a Ramaah yau an tuna damu dadin abuja ya hana ki kira ko koda yake nasan ba waya a hannunkima. Dan dariya nayi nace abuja akwai dadi gaskiya anty salima na tambayeta kowa nagidan tace duk suna lafiya saidai ya J ne ya dawo jiya ba lafiya amma da sauki. Nayi Allah ya sauka nace ta gaida kowa ta amsa da insha Allahu zasuji muka kashe wayan yar uwata na kira muka gaisa na tambayeta jikinta tace da sauki ta ban ummah mun dade muna hira ina bata labarin anty salma din. Bayan mun gama waya nace Yanda ta turo min number ya habu in gaidashi da sallah ba a jima ba kuwa ta turo min muka gaisa a yadda naji muryanshi kamar yana busy a lokacin . Zan kashe naji yana fadin nagode Rahama gamu nan mun dawo asibiti ne da J da baida lafiya idan na shiga wajen Maria zan kiraki ku gaisa naji ya kashe wayan nasa dip. Tun lokacin nima naji hankalina ya tashi kuma lokacin sallah azahar nayi sallah na kwanta sai barci sai gashi ina mafalki da baffa. A wajena gaskiya mafalki baffa bai zama alheri a wajena don baffa ya tsaya min a rain har ya zamo shine singn of bad luck dina. Idan wani abu zai faru da na kusa dani ko wanda nasani zanyi mafalki baba yana aikata mugun abinsa to kwana biyu sai wani abu ya faru da wani na kusa dani ko wanda na sani. Baffa mugun bafulatanin dajine ba arabi ba boko sai duhun kai da yake amfani dashi dip yake baida imani ko na miskara a rayuwansa . Inda na shamaceshi kuma sai yafi ji dani saboda zafin namana don haka lokacin zaman mu wurinsa nice mai masa dake dake da kula da wasu kayansa na tsubbu da tarkacen tsafinsa Dage dansa daya biyo halinsa wajen mugunta. Shine kan nuna min aikin da sake sakin da nake dakawa baffa amfaninsu da aibunsu don yana bashi siri sosai kamar shine maganijisa dai zance. Don haka nima