← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 263 OF 306

Sashe 263

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aminun yana inane mama ta kawar da shirun dake falon kaina a kasa ya J yace da ita ga uwarshi nan itace ta bashi mafaka a nan . Don ni tun jiya da yazo gidan nan ban yarda dashi ba koransa nayi don yadda yazo min nan a gigice sai hakan bai kwanta min ba. Itace ma ta saukeshi ta bashi wajen kwana a nan gidan dan idan tannei zai koma tun a jiyan ai da bai kwana a gidan nan ba . Wai dama ita Rahama tasan yana nan shine bata kira ta sanar da mutane ba don isa kuma ta ajeshi tabar mutane suna wahala hankali tashe ? Ke zanci abu kazan ubanki wajen nan ke meyasa kike yar iskane wai kamar kinfi kowa baki ban hanaki idan manya suna magana ki tsoma baki a ciki ba ? Me kika dauki kanki ko kin fi wanan biyun ya nuna salima dani baki da suka kama kansu agaban manya basuce komai ba ? Na dago kai nace ya Yazid don yaya ya kori Aminu ni sai na yarda ya bar nan din a yadda na ganshi nasan inda zai nufa kuma idan ya bar gidan nan ? Kwarai kuwa kedai yar nan kinyi daidai haka ake son macen arziki ta kasance dama ta kula da mijinta da kowa nasa wanan shike nuna halin alherinta . Bar sakaran nan da bata san komai ba sai rawan kai da iya makircin banza meye na ganin laifin yar mutane a nan daga ta taimaka muna da bata rikeshi ba yanzu har muzo a sameshi nan. Bakin saratu shi zaija maki matsala bansan irin bakin wanan yar ba a rayuwana yaron nan a nemansa an kuma ganshi a inda ya dace . Barta kawai dai idan itace mai mugun halin nan irinsune masu iza dangin miji nisa da dan uwansu wanan zata iya haka tsab yazid ya fada. Yanzu ina Aminun yake mama ta sake tambayan nasan don Yazid ya katse zancensane kan yarta ta fadi hakan a lokacin. Biba je baya ki kira yayanki Aminu kiyi maza ki dawo don Allah kada ki tsaya da sauri Biban ta fice don kofan a bude suka barshi saida ta dawo ta rufe tana fadin gashi nan zuwa anty. Bai jima ba shima ya shigo da sallamanshi yayi kyau a cikin kanyan dake jikinshi duk suka juya suna kallonshi sai yayane tun bai zauna ba yake tambayanshi. Dama da kaya kazo shine ka shigo min gida jiya da shigan iskanci kamar dan ginan zinari mutsu mutsu dakai ba dadin gani. Da sauri yaron yace a,a uncle mummy ta ban kudi jiya naje nan kasa na sayo kayan nan ya fada yana kallona daga inda nake zaune nace kudi na bashi nace ya sayo yan suturan sauyawa don yadda yazo. Ba dole ku gamshi hakana ba uwarshi tace ya dawo daga wajen ball ne ai ya samu a na rikicin ya kwaceta sun tarar mata kamar jaka zasu kasheta ya bambara uban daga shakar da yaiwa uwar shine haushinsa da dan don me bai bari ya kasheta ba ya bambarashi . Allah ya saka maki da alheri yar nan aiko hakan kin wadatar wallahi angode kinji kinyi komai wallahi iya ke fada min hakana. A Rahama ai dabance gaskiya ni halinta yana mun sosai wallahi wai har wanan sakaran zatawa mutane maganan iskanci don samun wuri. Tayi mana tunda ta sabayi tana cin banza naso ai ace bakai magana bane takai karshe a dazun din naci muruncin ta idan ba Rahama din datayi masa haka ba ni yaushe zan tsaya kallon dan Barakha yanzu ? Kallom J din kowa yayi da yake wanam kalaman nasa yace kwarai ko a zaron ku zan manta da cin mutuncin da kuka so min ne a baya ? Yau gashi wace kukai min donta itace kuma ta kama dan barakha aitayi amfani gareku kuje kuyi tayi idan muna funci abin yine ni dai nasan ban hada dukiyana dana kowa ba ? Yanzu kuma meya kawo wanan zancen ga yar uwarka Jafaru jinin barakha jinin kane hakama naka jinin natane dole ka rile dan barakha a duniyan nan itama ta rike naka. Ma tukar ana son ayi zumunci mai,,,,,,, Wani zumunci kawu irin zumuncin ku da mama kake nufi kome yan uwana dai masu kaunana saboda Allah zanyi zumuntan dasu . Kyaleshi kawu wani abu ya hau kanshi nake gani a gaban mu Jafar yake wanan magana yanzu ka yankesu ka soya so wa yanda baka so din. Basu dai sona mama ai su suka nuna min hakan ke zan fada maki da ga yau ki fita hanyana da duk wata iyalina Saratu. Na fahinci lamarin ki babu alheri a cikinsa ko daya don haka ba ruwan ki da iyalina na fada maki bake kika auro min mata ba ba a karshinki take rayuwa ba ko gaisuwa na yanke tsakanin kedasu. Bake kika ban abin hannuna ba balle ki kawo min izza da isa a cikin iyalina na fada maki . Basu ba harni yar kallon lankwas nayi ina mamakin yaya J a lokacin don irin maganan da yake zarowa a bakinsa. Eeh lalai Jafaru yanzu na kara yarda cewa an wanke na fulani kuwa an baka kasha don yadda ka zare din nan kai da bakinka kake fadan wanan maganan ga yar uwarka ? Don tayi magana fadan gaskiya da wanan wawa yakasa fahintarta shine kake fadan haka a gaban kowa yamzu ? Mama nine wawa kuma sai yayi murmushi baiyi magana ba yazid ke nan ashe akwai abindaya kulla a ransa ranan. Shiko yaya yace meta fadawa Rahama yanzu in ita bata da hankali ai ita da iya sun bata amsan daya dace ina magane akan shiga da tayi part dina jiya tasani meya hadata da Asmau jiya ? Waini karata ta kawo a wajen ka dama ni kike tambaya karanki aka kawo wajena don kina yar iska ni zaki tambaya don ban isa a kawo karanki a wajena ba ko ? Wai meye hakane kukeyi yau zaku tararwa mutum daya kamar kuna hake da ita dama kun zauna baku barmu munyi abinda ya kawo mu ba kan yaron nan sai zagin yar uwarku kukeyi. Sakaiyan da zakuyi min ke nan a yanzu na fatana inga kanku ya hadu tun da raina kai jafar kake fadin wai ka yanke alakarka dasu don mace ? Ita Asmau ta kasa fada min ko meya sai ta kiraka nan don munafunci ta shiryama karya da gaskiya ko mama akan me zata kiraki tunda bake kika ajeta ba . Eeh lalai kuwa na tabbatar a yau din nan haka kace Jafar mama me zance tunda wanan yarinyar bata son a zauna lafiya itace kadai kika dauka a yanzu kin haifa cikin mu ? Yaya tashi muje ta fada tana mikewa tsaye cikina duk ya duri ruwa a lokacin don yadda naga ranan ya rikide min ya koma malam jafar dinsa na gaskiya dake tsayawa ya fadawa ko waye gaskiya. A,a fa mama nima dana ganta dashi sai da nayi mata magana nace hakan bai dace ba ace ta shiga har dakinshi ta dauko mai abin amfaninsa haka ? Tace ina ruwana ai ba nawa bane ni kuma na kyaleta tunda kona fada maki kema zakice aiba nawa bane ta taba salima ke fadan hakan bayan sun mike din. Mama ta juyo ta watsawa salima din harara sai kawu ke fadin a,a dubu abin amfanisa fa akace ta dauka cikin zafin rai tace yaya don Allah ka barni ko ran jafar saratu ta dauka laifineb? Balle kayansa ai bansan a jirace yake damu ba gidansa ka zauna a gindin mata suna rabaka da yar uwarka dama ai haka suke so don burinsu ke nan ? Gaskiya kai Jafar kuma bai kamata ka fadi hakan akan yan uwanka a gaban mu ba don dai kokarin uwarku duk a kanku yake karewa taga ta kammalaku a waje daya. Wasu kalamai yazid ya fada a cikin larabci wanda shi yasan meya fadi kai dai fada masu in aya ka jawo koda yana da hakkon kan iyayyensa don tauye hakki bala,ine ? Muje yaya mama ta kara fada tayi gaba ya biyota a baya suka fice gidan kallon Aminu yaya J yayi yana fadin ka tashi ka bisu. Sai yaron yayi kasa da kanshi bai motsa ba ya kara fadan bakaji me nace bane ka zauna kuma ? Uncle ayi hakkuri don Allah a barni nan ni ba baeun ka gidan nan ba ban son abinda zai jawo muna magana kan zamanka nan kaga yar iskan nan yanzu ta fara fadan ba daidai ba. Ba abinda zai faru ka barshi a nan har aji ta iyayyensa jafaru tunda nan din yake son zama gashi anzo ba a gane komai ba yar banzan nan mai bakin tsiya ta hana akai ga matsaya kanka ? Waikai meya farune fada muna muji yazid ya fada aiyo yanzu naji maganan hankali wurin nan nan din Aminun ya shiga basu labarin abinda ya faru kamar yadda mahaifiyarsa ta fada a waya. Yazid yace ni yanzu yaya abinda naga yafi tunda har shi yace ya bar masa gidansa kan wanan zancen a barshi nan ya zauna mugani uban zai dawo hankalinsa ya nemeshi idan bai nemasa ba fine sai a rikeshi a nan din dama da gida biyu aka sanshi ai. Yanzu kai ka saurareni kaji abinda yaya ya fada wallahi naji wani tsegumi ko kyam daga gareka game da zamanka a gidan nan ko yaya bai koreka ba ni zan turaka kabar gidan nan. In shaAllahu uncle ba za a samu matsala a wajena ba ya fada wanan dalilin yasa Aminu din zama a gidan mu kuma yake amfani da hudubarsu a gareshi dama halinshine hakan shiru shiru bai magana . Haka burin da mama taci akan zataci min mutunci nida jafar ya tafi a fushin da takeyi dashi gashi ya nuna bai ma san tanayi ba. Zai kira Asmau da safe kafin ya karya su gaisa yaji lafiyansu haka kuma da rana zai kira suyi ta hira da yara don ita dai za ace gata nan daine da halinta. Ban faye damuwa da lamarin su ba don haka banyi mamakin rashin zuwanta gidan mu wajen mijinta ba kamar yadda shima din bai
Chapter 263 · 0% Book details