← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 306

Sashe 112

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

karyan da yayine a sayar abawa kowa hakkinsa mu rike abin mu ai abin yayi yawa wallahi. Barshi kawai dai Allah ya kawoshi lafiya ai yazo yai bayani zamuji mai zai fada iya dake addua ta shafa ta juyo tana fadin. Kaiya Hafsatu shi babba gyara aka sanshi dashi ba barna ba kina fadin zancen nan kawai don ki tunzara yar uwar mijinki ta saba da danta. Baki tunanen kema kin haifa ai hafasatu na rasa dalilin da yasa kuke son a tozarta yaron nan yau ko ace yaron nan da dukiyan nan yayi auren nan aiba zakuyi masa haka a bainan jama,a ba dai. Jidalin nan tun daren jiya kuna abu daya a kansa har mutanen nan sunzo sun tafi yanzu ko hakan da kuka gani baku tunanen wani abu akan yaron nan Jafaru. Kuna nan kun kasa kun tsare kuba zai zauna wa dan uwasa wajeba tunda kusan babu waje a sashenshi ? Amma ya gwatsale ku ya nuna maku shi dan yaune ya riga ya tanadi inda zaisa matarshi ko ya barku nan zube da takaici. Naso ace yadda kuka shirya mashi ya faru da sai ince ke hafsatu da mijin ki ku fita min a gidana shi jafar ya gyara gidan su zauna sai Allah ya gyara hakan. Iya saboda jafar sai ki kori su yaya gida iya waya saka yaje yai auren da zakice su tashi su bashi waje Allah dai ya gyara nace dake iya ta sake fada. Matar kawu bata sake magana ba tayi shiru don dama itace mai dumi a falon kana jin muryanta yana tashi tana bada labari. Anty Asmau kikace yarinyar nan ce ya aura ni sai naga kamar ba ita bace wallahi wanan fa kanwar matar Habun gidan nan dai yar doguwar nan ? Ummm,humm bari ke dai safena wallahi itace ya narka kudi ta gyaru mana tunda ba abin kai sake bane abin daga can sukaji muryan Saiba cikin tashin hankali tana fadin. Wallahi bai isa ba yaya dama na fada maki akwai yaudara cikin zancen nan wai ki duba imaging gidane fa ita kadai a ciki ya kama mata sannan ace wai mutum yayi hakkuri ? Asmau ta dan dubi yar uwarta dake kusa da ita tana dan sakin murmushi don duk da zafin hakan da takeji tafi jin zafin saiba a zuciyar ta don da alama ta manta duk itace sillan hakan a rayuwansu. Abinda tayiwa rayuwansu na shigowa rayuwansu ta bata masu zama ita da mijinta da tun suna kanana suke soyayya sai gata kwatsam ta rusa masu duk wani mafalki nata lokaci guda. Wanan yasa bata kai Saiban jin zafin zancen auren ba da farko yadda Saiba ke cika baki yasa tana dan shan jinita ga zancen amma yanzu da tayi arba da yadda yarinyar nan Rahama tashigo a tsatsaye yasa ta ji wani dadi yana kume mata zuciyanta na muguntan kishi. Don haka zata koma gefe daya tasha kallo duk da ba zata yarda a mayar da ita tatakan gida ba zata dan turza itama ganin ba aimai da ita baya ba a gidan. Wanan abin yaiwa Asmau dadi a zuciyata duk da dai kishin kowa nadashi amma ko hakan da Jafar yayi ya nuna ita din ba kowa bace a yanzu kamar yadda yayi mata a baya yayi matukar mata dadi a zuciyarta. Ganin saiba data fito daki fuuu ta nufi hanyar fita tasan part din mama zata nufa aiko basu rufe baki ba wajen tafawa sukaji hayaniya ya kaure a gidan. Mikewa tayi da kyat saboda tsohon cikin dake jikinta ta marawa part din iya baya Nusaiba ta samu zaune gaban mama tana kwasan kuka tana fadin wallahi mama ba zan yarda ba. Tunda duk kan mu a nan gidan ya ajemu da kowa don me zai dauki yarinyar nan ya kaita wani gida wallahi Allah mama ban yarda saidai ya sakeni idan baisona ne ? Shigowan Asmau da yar uwata yasa ta sasauta zancen tana fadin don ya nuna muna iyakar mu muba kowa bane a yanzu zai muna haka ? Ikon Allah iya data dauro alwala zatayi sallah take fadin hakan yanzu ke Nusaiba namijine don yayi abinda yake gani daidai a gareshi zaki tsaya kina wanan bori haka ? Iya don Allah kiyi sallah abinki an tabasune dole suyi magana iya tace ina tabawa wajen nan ina nan kuke da safe kuna mashi dariya don uwarsa tace ba zata bashi wajen zama da yarinyar nan ba ? Jin dirin motansu matar kawu yasa iya tayar da sallah don kada su shigo su bata mata lokaci bayan wanda ta bata din a baya. Sai gasu sun shigo da sabon labarin da suke bayarwa wanda ya tayar da hankalin duk wanda ke wajen don Jafar yai masu bazata yau. Asmau da taji zancen yana batun hautsana mata rayuwa tacewa yar uwarta suje don a gabansu komai ya wakana. Saiba sai sabon kuka data saka lokaci guda cikin tashin hankali ba wanda ya farga da fitanta don kowa da abinda zuciyarshi keyi a lokacin . Matar kawu dai iya ta rufe mata baki haka mama tana ji a ranan in Jafar baiyi hankali ba zata iya mashi baki don saura kiris akai wajen yadda take jin yaudaran da yayi mata da yayanta yana ci mata zuciya lokacin. Wai ace yau Jafar ne yayi mata wanan tozarcin da bata taba tsamanin hakan gareshi ba duk cikinsu Yazid ne mai rawan kai da kuma tauri amma Jafar shine salihin su. Don haka wanan karyan da akace ance ya shimfida a gidan wanan yarinyar dole ya sayar da komai nasa a yanzu yaba yan uwansa hakkinsu. Kwandala ba zata daga mashi kafa daga ciki ko kudin bai kai miliyan goma ba zai san inda ya nemo aka basu hakkinsu inyaso shi ya zauna haka din tunda shiya jawa kansa hakan . Kamar Jafar ace mata ukku ina zai kai mata ukku da shekarun nan nasa sai taji duka matan nasa tana jin haushin su a lokacin. Ita saiba da tazo tana wani babatu ba zata yarda ba ta bari ta gani idan yaci dadin amarcib da yarinyar tunda harsu abin zai shafa yanzu taga karyan iskancin kowa a gidan yanzu. Itako maria tasan hanyar da zata fito mata ba tace ta iya kisisina ba daga ita har uwarsu suna ganin sun kitsa yar uwarsu tazo aci arzikin su dasu to za a ci din ta gani . Tasan dai gudu ya kare mai a yanzu tunda yarinyar nan ta tare gidanshi dole ya dawo garin yanzu taga ta iyakar gudun da yakeyi din nasu yanzu. Muryan matar kawuce dake fadin hjy Dubu ni zanje gida nabar kawun yara da tsaron gida tun dazun yana gidan shi muka bari da zamu fito. Mama dubun ta dago tana fadin hafsatu zaki komai in kinje kyaba yana labarin abinda ya faru ko sai ki sanar dashi da safe ya sameni nan ina wajen iya. Wai ina salima ta dauko maku ajiyan abin shan dana bata dazun ? Wai Salima ai tunda muka dawo kaduna suna wancan gidan da aka kai amarya gaba dayansu basu dawo nan ba anty Baraka ta fada . Kaji wata ja,iran watau tasan komai tun safe kallon mu takeyi shine ta kyale mu ta kara jin abinda ake fada to za a fasa fadane tunda ya kwamshe kudi shi kadai yana faca ka ?
Chapter 112 · 0% Book details