← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 306

Sashe 108

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwana biyu a cikin zazzabi na samu sauki har lokacin ina gidan mama saidai anty salma takan zo ta dubani lokaci lokaci amma ba wanda ya kara min zancen auren Jafar dake kaina yanzu. Saina dauki hakan da kila gwadani sukayi ko zan yarda da zancen amma ganin ban yarda ba yasa aka fita zancen nasa. Hakan ya bani karfin gwiwan sakin jiki da har na fara fitowa falo muna dan hira da mama satina daya cur a gidan anty salma tazo a wani yammaci zata tafi na mike nima nace tare zamu tafi ai. Ta juya ta dubi mama mama din tace kuje mana duk da daddy bayanan idan ya dawo zan fada mashi ta koma gidan ki hakan yasa muka tattaro muka dawo gidan anty salma din. Sai a ranan kuma ta ban wayana dake hannunta duk da ina son wayan a tare dani ganin bata ban ba nima ban tambayeta ba saina share zancen wayar tawa din. Sai gashi ta mika min abina ba tare da kona tambayeta din ba wayan da cajin shi full haka yasa na kunna don a kashe take nayi tunanen mutane da yawa zasu nemeni sujita a kashe. Data na kunna na aje saman gado inda sakonni suketa shigo min kai tsaye bandaki na shiga nayi alwala don magariba daya kawo jiki idan na biyewa wayan za a samu matsala dani lokaci don shedan zai rinjayeni in shagala da zancen sallah. Na idar nayi addu a na shafa naji wayar tana sauti alaman kira yake shigo min lokacin na mika hannu na duba anty Nafisa ce akan layin. Ina dauka tayi sallama na amsa naji tana fadin haba matar yayana duk sallon amatcin ne haka ko waya baki dagawa sai kinga dama halan angon ya fitane. Ke kuma shike nan ko buki kinki fada muna muzo musha wallahi Ramaah ban zaci hakan daga gareki ba sam na dauka kome ke nan nice ta farko da zaki fadawa ai. Anty Nafisa ke nan nida ke kwance banda lafiya mezan fada maki satina daya ina gidan mama banda lafiya wallahi sai yau na dawo gidan anty salma dazun nan taban wayan na kunna kece ta farkon kirana yanzu. Haka madam Maria ta fada min cewa baki da lafiya to yaya jikin naki nace da sauki anty Alhamdullahi ya kuke ya su mama dasu inna ? Lafiyansu kalau Ramaah ga inna ma tana gaidake da jiki sai naji taba inna wayan ta soma fadin halo Rahama yaya jikin ya mutanen wajan ku ? Lafiya kalau inna na fada take fadin to kiyi hakkuri da kaddara kinji auren jafar alherine a gareki in sha Allahu ki fita zancen kowa ki kama mijin ki. Kada ki damu da zancen su yaya Dubu duk bari zasuyi tunda mijin ki yana kaunan ki kowa tasa ta fisheshi haka zaman gidan miji yake dama. Kada ki kula kowa kiyi abinda zaki burge mijinki dashi Ramatu ita wanan da tayi yaji karma ki tsaya kula ta ki zage ki nuna masu akwai banbanci a tsakanin ku. Barta can ko Allah yayi dawowan ta gidan kada ki yarda ki biyewa shirmensu na rashin hankali kin daiga yadda yar uwarki take dasu. Jafar mutumin kirkine yasan ya kamata kwanciyan hankali da kulawa yake bukata in sha Allahu zaki alfahari da hakan na gode inna na iya furtawa a cikin kyarmar murya. Na sake jin tana fadin na fada maki ki fita zancen su yaya dubu da sukeyi na asiri kikaiwa Jafaru keda yar uwarki har ya aureki. Lokacin naji muryan Nafisa tana fadin nikan inna zaki cinye min kudin waya bamuyi magana ba ta amshi wayanta badon inna ta gama zubanta ba. Naji tace min Ramaah to yaya jikin naki nace lafiya kalau anty Nafisa ta sake fadan yaushene tarewan naki koda yake ai kamar ba yanzu ba ko don ance yaya baya Nageria ya tafi kasan waje. Wallahi ban sani ba na fada maki ai dazun nan na dawo gidan anty sallma bansam komai a kai da suke shiryawa ba. To bari na barki saina sake kira mukayi sallama ta barni da waya a hannu ina mamaki a raina nace watau zancen auren dai yana nan a kaina ke nan ? Ni Rahama yaya zan iya rayuwa da yaya Jafar a matsayin mijina da fitinan gidansa ta ina zam soma wanan badakal auren da ya hau kaina yanzu kuma ? Har nayi sallah isha,i na koma saman gado na kwanta maganganun inna kemin yawa a kai na kasa hadasu a waje daya. Ni Rahama nice zanwa yaya Jafar asiri don ya soni ba yaya Jafar mai mata ba ko wani irin namiji ba zan iyawa a siri don na mallakeshi ba a ina ma zan samo asirin da zan masa din ? Zancen maganin na dashi ya fado min a rai gabana naji ya fadi na furta na shiga ukku shiyasa taimako yake da wuya a zamanin nan. Ko dai sun dauka maganin na asirine da zaisa ya soni nayi mashi a lokacin harwa yasan da zance haka banda nafisa da ya habu sai shi jafar din. Shigowan anty Salma ya katse min tunanane ta shigo tana fadin ke abinci fa bakya jin yunwa ne kika kwanta ,? A hankali na dago idona da sukai ja duk da ba kuka nayi ba a lokacin amma bacin rai yasa idanuwana sun sauya min lokaci guda ba yadda na dawo daga gidan mama ba. Meya faru kuma take tambayana muryan can kasan makoshi nake fadin ba komai anty tace ok ga abinciki nan nace jummai ta sako maki a kawo maki nan baki jin dadi ba lalai bane ki fito. Allah sarki anty salma ba abinda ya dameta ita hankalin ta kwance komai nata cikin gata ba tsamgwaman rayuwa nake fada a kasan zuciyana sai naji tace ke Ramaah ? Jafar din nan naki wani irin mutum ne shi gaskiya mutumin arzikine sosai wallahi a cikin matansa akwai mai cikine ashe ? Kai na gyada bata jira cewata ba taci gaba da fadin dazun nan ya turo min da kudi da za aiwa mai jego da jariri sayaya har daku daba haihuwan kukayu ba bayan lefe da na tausan gaba daya saka aka hada mashi. In wanine yana zancen aure a gabanshi aiba zai tsaya tuna hakan ba har ya tsaya hada kayan haihuwa kan wa yan nan yan iskan matan nasa. Ni wallahi Ramaah tun bangasu ba bakiji yadda na tsani halaiyansu ba haka kawai su hana bawan Allah shakat a rayuwansa don iskanci da samun waje wai meyasa matan hausawa akasarinsu suke hakane ? Naji ance wai ita dayan matar nasa tayi yaji tana gidansu tun ranan da taji zancen auren shi kuma yace a barta can ba inda zaije tunda bashi ya turata ba. Kala bance da ita ba akan zancen har jummai tashigo tana jera min abincin ta gaidani da jiki ta fice a dakin kallona tayi tana fadin ki tashi kici abinci kisha maganin ki. Kada mijinki ya dawo ya samu kin fada yace amanan daya ban ke nan na bari kika koma haka nidai banyi magana ba ta kare ta fita tana jaddada min da inci abinci fa. Sannu a hankali cikin hiran anty Salma nake ta tsuntar magana wai ashe har kudi yaya Jafar ya bayar a saya min wasu abubuwan da nake bukata. Saidai tace kudin suna hannuta don ita dasu mama sun hada min kayan daki komai daddy yaba da kudi a saya min gwargwadon hali ta kara ta sai min moderate din kayan kitchen na zamani dasu. Da anty Salma tasan zancen aurena akan jafar yana daga min hankalu da sam zata dingayi min zancen ba amma bamu zama bata sako min zancen shi a gabana duk dade gyarane irin ta yayyu take min a lokacin. Ina kuma karuwa sosai ga wasu abu da take ban duk da tare muke faman dirka da ita wani lokaci kuma ni kadai zata ba in shanye tas a gabanta. Training din rayuwan gidan miji aiko zama tsakanin mama da daddy dole kayi course sun tsufa amma rayuwansu zakice yarane har yanzu su balle anty salma dake cikin ganuwan kurciya a lokacin tana shanawa da mijinta. A cikin hakan muna waya da yar uwata har da mama saidai suyi ta kwantar min da hankali sam ban tsamaci hakan ga yar uwata ba na dauka zata shiga damuwa fiye dani sai gashi naga akasin hakan gareta. Ranan da mama ta kirani tana tambayana jafar ta kashe wayan ta barni da mamakin ta don dai ban taba tsamanin hakan wajenta ba yadda takeyi min maganan . Itace fa mai min addua Rahama Allah ya baki miji nagari inda zaki huta kema sai gashi a yanzu lokaci daya ta sauya min. Yandace ta kirani take fada min abinda ya faru har mama din tazo ta karbi wayan wai suna tuhuma Jafar ya daukeni ne mun fita tare dashi shine yasa tazo ta tabbatar da hakan a kaina. Bayan ta tambayi Nafisa tace da ita muna waya ina Abuja har yanzu amma hakan baisa ta yarda ba a yadda nake ji a bakin anty salma zancen tarewana wani satine insha Allah. Hakan ya kara saukar min da faduwan gaba ta ina zan fara ina zan kama yaya zanyi in zauna wanan gida da sunan auren jafar a kaina. Har wata zuciya tana ban shawara da ingudu in koma garin mu sai na tuna ai can aka daura min auren alkakan a kaina dole dai na tsurawa sarautan Allah ido. Sunje Zaria kwana su daya suka dawo saidai kaduna tace min zata ashe zaria sukaje gyara min daki saida ta dawo tana santin gidan take fada min ai sunje sun yimin jerene a zaria . Gaskiya Rahama kinyi sa,a sosai gidan ki ke kadai ba wani hayaniya ko saka idon da wani zai maki irin ta maria ke kadaice a babban gidan saidai gaskiya gidan nada girma sosai. Mun samu ya gyara gidan ya saka komai amma muka saka kayanshi a falonshi Kayanki da akai maki nan muka gyara maki naki falon hakama daki biyu muka gyara maki sai muka bar wancan a matsayin turakan maigida. Ni ba tsayawa saurarenta nakeyi ba ba don duk abinda zata fada ba burgeni yakeyi ba saukinsa
Chapter 108 · 0% Book details