Sashe 10
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
aka haifemu rayuwace ta dawo damu gida bayan rasuwan mahaifiyar mu rikon mu ya dawo nan. Sosai ta bashi tausayi tsab ya gama kallonta yana karance yanayinta turancine neat a bakinta amma kuma gata ta saje da dabi,un mutanen wajen ba zaka taba cewa ita din tasan ko zo inkasheka ba da hausa balle turanci. Yanda din ta kawar da shirun take fadin ku saya zakace nace idan kuje dashi aka saka a fridge zaiyi rabin shekara a can bai baci ba wanan karon a cikin hausa tayi maganan tana kara bude manyan koren dake gabansu. Sahabi bai yarda da zancen ta ba don abar zancen yake fadin wai ina zamu samu abinci mai kyau a wajen nan ? Ta dan juya kafin ta fara masa kwantace ganin baigane ba yasa ta kwalawa wata yarinya kira da Maria zoki nan saiga wanan yarinyar dake firgitashi tun zuwansu garin itace aka kira da Maria din. Yarinya ce karama saidai da gani ba sai an tambaya ba don kamarsu da yar uwar nata da aka kira da yanda sukayi kama sosai ita wanan din dai ta girmewa yarinyar a shekarune kawai zace sai dan haske da karamar ta dara babban dashi. A cikin yare take fada mata ta kaisu wajen saida abincin yan maiduguri ta amsa da to tana watso masu idanuwanta masu kama da madaran tana wani irin juyasu alaman suje din tayi gaba suka bi bayanta . Zansu tafi babban matar ke fadin ya zancen sayan kayan sahabi yana kokarin fadin su barshi kawai shi kuma Abubakar din yace dasu a bari su dawo zasu saya hakan yasa yaga fara,a a fuskan yar budurwan data kashe zuciyarshi da mamakinsu. Sun kama hanya tana gaba da dan kwarya karami a hannunta bata ko tsaya wani jerawa dasu ba tasha wani kwana suna biye da ita har zuwa wanan wajen da basu san dashi ba. Oya mun gode ki tafi kada a nemeki Sahabi ya fada sai ta amsa da to tana kallonsu saidai taki gusawa daga inda take. Abubakar daya kula yace da yarinyar yaki zo nan Abubukar ya fada yana kallonta da sauri ta biyoshi a baya zuwa inda suka nufa. Tare suka shiga shagon yasa aka hada mata take away guda ukku ana mika mata ta juya a guje cikin murna bata ko tsaya godiya ba ta nufi sansaninsu kai tsaye da gudunta a cikin murna. Murmushi yayi ya juya wajen sahabi dake mamakinshi yace mutumina yaya dai nisawa yayi yana zama ya soma fadin tausayi suka bani wallahi. Haka duniya take ai dama ba ko yaushe mutum ke samun yadda yake so ba a duniya sahabi ya fada yana kallon abinci gabansa da aka aje masu. Abincine lafiyayye mai kyau irin na hausawa ga kamshin man shanu yana tashi acikinsa sukaci sukaiwa yan uwansu take away. Duk abinda yake hankalinsa na gun wa yan nan mutanen don hakane ya saci jiki ya koma sansanin nasu saidai ya samu basa nan don lokacin yamma tayi sai wata mace dake zama a kusa dasu. Yake tambaya take fada mai ai basu kai dare a wajen sun koma gida saidai gobe tunda safe zai samesu sun fito insha Allahu. Washegari kuwa rana ta biyu da taron mutane sun fara tattara kayansu don shirin komawa garuwansu daga ciki har dasu Abubakar duk daidai su sai an rufe taron suke son su kama hanya komai dare a ranan. Bai manta da zancen yaran nan ba don da zancensu ya kwana a zuciyarshi yana son ya san wani abu a game dasu din. hanya kama ya nufi runfarsu tun daga nisa ya fara hango ita babban wacce yake kyautata zaton mahaifiyarsuce ga wasu yan Nageria suna sayan kayansu. Don kayan nasu gaskiya yayi kyau sosai haka ya karasa gaban ya dan tsaya yana dakon su gama cinikaiya da wa yanda ya sama din a wajen. Karamar ya fara gani a gabansa tana binsa da kallo kafin ya tsinkayo babban dake tafe da amalanken shannunsu dake dauke da kore. Yana wajen suka sauke kayan tsab suka jera kafin ta dago ta soma gaiyar dashi a cikin dan fara,a kafin tace dashi na dauka kun muna wayaune ai kun tafi koda yake bakai kama da mayaudariba ba kai kan. Jiya kuma sai kukayi wahala haka kuka saya muna abinci mai yawa angode Allah kara arziki me za a baka daga ciki ta fada tana kallonshi tana dago kai ? Samu tayi ya zuba mata ido baya ko kiftawa sai tayi murmushi ta sake maimaita wane kake so yace yanzu ni ina na san me zance dake ?. Tace wanan zaka iya saya kakaiwa iyali mata ko mama da yan uwa zasuji dadin tsaraban shi ansan ka shigo kasan cameron . Ko data dago kai still yana kallonta sosai sai taji ta tsargu da hakan ta dan dukar da kanta kasa tana wasa da zara zaran yatsunta. Bakayi magana ba ta kara fada kallon yadda ake durawa mutane a jarka yayi yace nawa duka kayan nan da kika sauke ? Ido ta zaro waje tace dukka fa kace zasu iya kaiwa dubu hamsin da kudinku na Nageria ga mamakinta sai taga yana kokarin zaro kudin daga jikinsa. Kuyi min parking dinshi yadda ba zai samu matsala ba kudin abinda zakiyi amfani dashi ayi parking yana ciki saidai don Allah ? Saita dago ta kalloshi yayi mamakin ganin idonta da hawaye jikinshine yai sanyi ya dan matsa kusa yana fadin. Lafiya dai tayi kasa da kai tana fadin bansan irin godiya da zan maka ba a yau da an watse taron nan bamu saida kayan nan ba ba karamin fitina zamu shiga ciki ba don zamuyi hasara sosai zamu kuma shiga cikin ukuba. Saboda me ya tambaya yana kasheta da ido donson jin karin bayani shidai yanayin yarinyar yayi mashi sosai tana da natsuwa sosai dayake hangowa a gareta. Murmushi tayi tana fadin dogon labarine mundai gode da wanan taimakon da kayi muna Allah ne kadai zai sakama da alherinsa. Amma meya dawo daku kasan nan kuda kuka saba da rayuwan Nageria kuka zabi dawowa nan ku zauna ? Ya zamuyi bamu da kowa a can yanzu wanda yayi sanadin zuwanmu can Allah ya karbi abinshi dole muka dawo kasan nan tunda ba yadda zamuyi. Kina da waya in naje mu dinga gaisawa daku tace da ina dashi wanda nake amfani dashi a school saidai zuwan mu nan gaskiya mun kadar saboda yanayi saidai ka ban number wata rana zan kira insha Allah. Ai har karatu kinyi ashe kuma kika kare a nan kina tallan nono tace wanda baida gata ai duk yadda rayuwa tazo mashi haka zai rungumeta mun rasa gatanmu tunda mahaifinmu ya rasu Allah ya jikansa yace ta amsa da amin. Sai wata rana kenan zaki kira ba zaki kira kiji ko mun sauka lafiya ba ko kuma ina da bukatan wanan abin ki turo muna dashi. Dariya abin ya bata cikin dan kunya take fadin kayi hakkuri banda wayace kona karba ba zan kira ba din kaga ai gara dai kar nayima karya. Kinsan wajen motar mu ko ta amsa da ehh yace a shirya komai kusamemu can ya juya ya tafi ta bishi da kallo tana yaba irin kirkinsa da halarci.