← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 251 OF 306

Sashe 251

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin zancensu da mama a wayan na fahinvci baida niyar komawa gidansu a ranan yana nufin a nan wajena zai kwana ke nan. Banyi magana ba a lolacin saida yayi sallah duk a nan falo na bashi abinci yaci an dan jima nake fadin Yazid din bai dawo ba har yanzu ga dare nayi kuma baka sha maganin ka ba kuma !? Kin ce ya dawone ya kawo mj magani ya tambayeni cikin tsureni da idanuwanshi da sukayi mugun fadawa a yanzu saboda raman daya karayi kuma yana son jin amsan tambayansa a gareni. Saida na sada kaina kasa nake fadin ni bamuyi hakan dashi ba naga dai kana shan maganine bai kamata a kyatare ba kuma ? Rahama ko kema gudana kika farayi yanzune kamar wa yan can dama da wanan maganan yakanci galabata idan irin haka ya taso a tsakanin mu. Gudunka kuma ban guje ka ba a baya sai yanzu na fada ina daure fuskata to ba inda zan tafi yau nazo ke nan dama ai kece mai jinyata din suka koreki ko ? Ka daiyi kwanakinka ka koma ni kada ka jawo min wata magana kuma a sakani a faufai ana tallah na bayan wannan da nake cikinsa. Suyi tayi mana waya damu da zancen mutu ni yanzu ban kara jin nauyi ko idon mutane a irin haka abinda zai fitar dani zanyi idan sun damu dani su biyoni nan su dubani ai. Wani kallon mamaki na sake mashi amma ban furta komai ba saboda gudun rashin fahinta amma nasan hakan ba abu bane da zai yuyu a garemu a yanzu. Bayan hakan nima ai ina bukatan hutu don haka ba zan sake wahal da kaina ba irin danayi a baya koma yace din zai zauna a nan nasan mama ba zata taba barinshi ya zauna din ba. Mikewa nayi na shiga bedroom dinsa har lokacin banyi magana ba ya bini da kallo na jima a ciki na gyaro mai ko ina na sauya zanin gadon nasa mai duhu saboda maganin da ake bursune masa jiki dashi . Ruwan wanka na hada mai na fito na samu yana waya na wuce zuwa kitchen na dan kawar da kaya na fito na samu ya gama wayan nake fadin ga ruwan wanka can na hada ma saidai ban sani ba ko saida magani kakeyi har yanzu. Yanzu da ba maganin a kusafa ba sai in watsa hakana ba yaushema rabona da wankan dare tun tafiyanki ai sai inkai kwana uku ma yanzu ko wankan maganin banyi ba. Da sauri nace saboda kaji sauki ko ka daina magani bayan ciwon bai gama fita a jikinka ba har yanzu ? Saida ya langabe kai yake fadin bari kawai Rahama shiyasa manya ke fadin Allah ya kawar da ranan yabo ga mutum aini naga abu dan tafiyan nan naki saidai kawai a kyale kawai ba a cewa komai. Amma ai yanzu na fahinci kowa a duniyan nan ki bari kawai Rahama sosai zakiga halai yana ya canza a yanzu don darasin dana samu a kwanciyar nan da nayi. Zance da bansan dawa yakeyi ba don haka ban yarda na zake sosai ba illama cewa da nayi ka tashi ka watsa ruwan kada dare yayi. Yai shiru kamar yana tunane kafin naga yana kokarin mikewa tsayen daga inda nake nake fadin kona taimaka makane ka mike ? Yace bari na dafa kujeran ai yanzu dole na koyi hakan tunda ba mai zama dani sai iya, iya kuma aiba zan bata karfina ba tunda itama ta kanta takeyi yanzu. Haka dai ya samu ya mike ina bashin a baya a dakin daya kai saida ya zauna yana ajiyan zuciya nice na taimaka mashi ya mike tsaye zuwa ban dakin nayi set up din komai don har kujara da zai zauna saida na cudashi na fito na barshi ya kara din. Daki na koma na jawo goran ruwan zam zam din da anty Nuratu ta bani na diba na fito zuwa dakin shi na samu har lokacin bai fito ba nayi magana ina fadin har yanzu baka fito ba ashe ? Sai naji ya amsa da fadin ina kara zubawa jikina ruwan zafinne don sunyi min dadi sosai a jikin zama nayi na fara jero adduan data koya min . Wanda kowa ya sani ga sauki ga falala ga musulmi shine suratul fatiha da ikilas sai la,ilaha illah anta subba hannaka innin kummtu minal zallimin kafa 41 da daya data kira shi da raina kama kaga gyaya . Koda ya fito ya samu ina sauke falaki da nas da kulluhullahu kafa uku uku ina tofawa yana zuwa ya zauna na mika mashi ya sha . Saukin abin sam baida gardama shi kam ya karba daga hannuna yana bissimillah ya kafa kai ya fara zuka nace ka dan rage in shafama ya amsa da kai ba tare da yayi magana ba. Saida ya shaye ya miko min na karba na fara shafa mai a jikinsa ko ina sai faman ajiyan zuciya da yake saukewa ana son ya bushe a jikin mutu don haka na barshi nace kada ya rufa sai ya sha iska. Na leka dakin Biba na samu tayi barci nayi mataa addua na fito a yanzu in shha Allah ban sakaci da addu,a abakina tunda aka tunatar dani hakan.. Na kashe mata wuuta na fito daga dakin nawa dakin na koma na kimtsa kaina tsab na rufo kofan zuwa dakonshi na saami ya kwanta shima a bakon gadon na zauna ina karanto addu,oin dake bakina na neman tsari daga Allah. Shina fara tofawa kafin ni nabi bayanshi na kwanta a hankali ina jin yadda yake sauke ajiyan zuciya jefi jefi zakice yayi zuciya akan wani abune ? Shigowan mijin nata ta gaidashi ya amsa yana tambayan yaranshi ta bashi amsa da sunyi barci abinci ta mike ta kawo mashi saida ta hada mai komai ta samu waje ta zauna tana fadin. Dazun su anty Nuratu sunzo daga kadun wai sun dawo da Rahamane yau har ya dauki kofin ruwa zai kai a baki ya dakata yana kallonta kafin yace. Dama yau zata dawo ashe ta bashi amsa da ban sani ba nima saida suka biyo nan ni suna min fada wai ina nuna ban damu da Rahama ba yanzu? Ni yaya suke son nayi don Allah kowa yana ta ganin laifina akan Rahama yanzu shiyasa wallahi ban so auren nam nata da yaya ba tun fatko don gudun irin haka. Kai baka gama daukan naka laluran ba ace sai ka dauki laluran wani ita Rahama ai tunkan ta auri yaya tasan abinda dake cikin gidansa. Kuma ta yarda ta zauna dashi shiya tare ta da fadin kanki daya kuwa kalau kike kike fadan wanan maganan ko so kike ta bijirewa iyayyen ku da suka bada goyon bayan hakan ? In ma laifine su hardo suvkeda laifin ai da suda basu binckeki ba suka daura mata auren dashi amma ita Rahama umurni tabi ta zauna dashi. To ni dai wanan auren a yanzu yasani tsakiya gaskiya nan yan uwanku naganin laifina cewa dani na hada komai nayi sheri data auri yaya . Can kuma gida sun koma ganin laifina a yanzu kan naki tsayawa yar uwata in mara mata baya murmushin da mijin yayi yaci gaba da zuba abincinshi shiya katse mata magana. Sai binshi da kallo da tayi a cikin tuhuma saboda me yayi murmushi bai tsaya kulata ba ya soma cin abinsa falon yayi shiru na dan lokaci kafin taji muryanshi yana fadin. Yanzu dai na fahince ki so kike ta kashe auren ko ? Ko kuma bakiyi na,am yanzu da dawowan datayi gidansa bane da sauri ta tare da fadin ka rufa min asiri don Allah ni ba haka nake nufi ba kawai dai gani nayi a yanzu kowa ya dora laifin hakan a kaina. Ko anyi hakan daidaine Maria ja rasa irin halinki nako in kula har yar uwarki da kika san kece sanadin zuwanta gidan nan kina nuna halin ko in kula irin naki a kamta. Dolene Rahama tayi fushi dake ta nuna bacin ranta duk abubuwan nan dake faruwa kin taba tsayawa kika nuna damuwanki a kai ? Rahama ce fa ku kenan ku biyu ga mahaifiyar ku sai yam uwanku maza amma zurin ciki ya hanaki fitowa ki kare yar uwarki don kada a zargeki ? Nima nazo daga baya nayi tunanen rashin kyautawa yarinyar nan mu ya kamata ace mun tsaya mata ba sai tabar dakinta zuwa wajen ummah ba. Nasan Saratu yar banzan yarinyace sosai idan ta saka abu a gaba daki sai taga bayan abin wanan yasa nayi mata iyaka daku tun farko . Wanan kuma yanzu ni ba mai zama bane balle insan abindake gudana ke kuma baki kirana ki fada min to yanzu gashi ta gane hakan ta dauki zafi dake kuma abin ya dawo ya dameki. Tana da gaskiya idan tayi hakan don mu muka fara nuna mata rashin kullawan mu su kuma aiba fushi sukayi dake ba tunda har sun biyo nan sun duba lafiyan ku. To amma baban ,,,,,, dakata haka maria don Allah wanan zance ya isheni ki barni inji da wanda ke gabana a yanzu don Allah yaci gaba da cin abincin kafin ya daga ya barta tana kuka a wajen. Nima haka na kwana ina tunane akanta don tun bayan zuwan da sukayi gida bamuyi waya nida ita ba saboda ta hau fushi dani wai naki girmama mijinta indawo a lokacin. Kiran sallah asuba na farko na tashi zuwa bandaki na dauro alwala na dawo na fara nafila saidai saidana dubashi yana barci har lokacin cikin kwanciyan hankali hakan yasa banyi dogon motsi ba kada yaji ya tashi a lokacin. Don a lokacin barci ake son ya samu issashe a rayuwansa idan ba hakan ba daya tashi shima tunkan na tashi din din na shedeshi gaskiya akan addini sosai. Shi mutum ne da aiyukanshi basu hana mashi tsayawa bautan ubangiji hakan kuma yana raya dare wajen bautan Allah saidai ba kullum ba. Muryan ladabin unguwar na kira na biyu naga ya falka ina zaune ina lazumi a inda nayi sallah nasan idan ma ba yanzun daya dan ji sauki ba bai iya dagawa da kanshi ko alwala a baya saina kawo wani tasa mai fadi
Chapter 251 · 0% Book details