← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 227 OF 306

Sashe 227

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka abin ya kasance duk da ya nuna baison hakan dana yankewa kaina amma saina dake da safe zan shigo inyi mai duk abinda na sabayi idan yamma yayi kafin magariba saimu koma gida da Biba ko anty Nafisa. Tun yana daure fuska idan nazo har yakai ya dan sake ya fara daina hakan da yake min ina daga ciki tare da mama nake jin hiran mutanen gidan dake zaune falon da ake jinyasa din salima ke fadin. Kefa Asmau na kula kwanan nan sai wani sheki kikeyi kina wani budawa meye sirin hakan kuma ? Koda yake duniya taki yanzu an watse an bar maki miji ke kadai kina shanawa ba dole kiyi sheki ba haka ? Wani anbar mata miji a ina saida aka gama abinda za ayi don dai ita bata san zafin kanta bane ai ina zan zauna mace na shigo min gida tana min feleke da yanga ana iskanci da sunan jinya wallahi ba a haifi wanan yar ba tukun . Komai sukayi ai don kansu saratu balle ma me akeyi duk abinsu dai basuyi da ranana balleni kome zasuyi yanzu ai na saba da ganin hakan akan mutumiyarki Nusaiba bai kuma daga min hankali ba balle wanan din. Sai naji salima tace ballema me akeyi maganan kice dai kawai saratu da wani tashin tashin dinki can daza ki kawo za,a hanata zuwa duba mijintane kuma ? Wayace za,ya hanata yanzu don Allah ni dai banson abinda zai hadani da wanan yar kauyen yarinya dake ganin daidai take da kowa yanzu gidan nan. Jin nayi shiru ina saurarensu yasa mama soma fadin zaku fara takale takalenku ko ku jawa kanku zagi a karshe a juya maganan kuma . Ko yaushe ina muku fadan irin wanan maganan dabai shafeku ba amma baku jin kashedin da nake maku ina ruwanku da shanawanta yanzu kuma ? Sallon ku hada wani fadan kuma kenan a yanzu tsakaninsu ana zaune kalau maman tudun wadace take fadin hakan a garesu rai bace. In sun jawo magana ai suji dashi ni ina ruwana tunda ban aikesu ba sun daiji abinda yazid ya fada game dasu ai ya karya yarinya ba wani abu bane wajenshi. Ballema mama waye zai dauki zancen su tunda ba sakarai nake ba kawai dai magana ce mukeyi sai kawai saratu din ta mike tana guna guni ta fice . Ashe fadi take don an mayar da mutum baiyi aure ba za a dinga mashi abinda akaga dama karya ta fada ba cin amanan akeyi ba inba hakaba ya akayi tayi ciki yanzu ? Na jima a zaune nayi shiru kaina kasa gaskiya wanan mace tana son shiga min rayuwa duk dana tattarata na watsar gefe daya iyakata da ita gaisuwane wata rana kuma bamu ko gaisawa din da ita haka zamu share juna. Tace ita danyar kai nace na fita muje zuwa sai hakan da nake mata kuma a yanzu ya koma bata haushi tana jin kamar ta shakeni ta kwantar. Wai ashe bayan tabar part din takoma nasu shine taje ta kira saiba a waya tana labarta mata duk abinda aka fadi abu ga mara hakkuri saiga saiba din ta kira Asmau tana zagin ta. Muna ciki din mukaji Asmaun na fadin ita saratun din tace hakana wai meyasa saratu keda tsegumine wai ? Shiru daga ita har mu wajen yayi can ta soma fadin Nusaiba na fada din ina ruwana da duk abinda zasuyi ke bakiyi min wanda yafi wanan din bane aiba karya na fada ba ko ? Mama tudu ta mike ta isa tana fadin wai meye kuma yanzu ita yarinyar nan dan maganan nan saida ta kira yarinyar nan tun ba a bar wajen ba ta fada mata ? Anya kuwa saratu kanta daya kuwa da wanan halin ke mara kunya an fada din ai idan bakiyi ba ba zata fada ba ai wanda ya mutu akewa karya. Mikewa nayi na fara hada kayana don tafiya kallona yayi yana fadin ina kuma zaki yanzu na amsa da gida rai bace ban yarda na kalleshi ba. Abin yana ban haushi duk da nasan yana cikin halin ciwone a yanzu amma kuma a yadda na fahinceshi shine gaskiya duk cikinsu kamar kannensa sunfi raina shi don me zatayi ta min hakan ko watan mu ya kasa daukan mataki idan kuma ka dauka da kanka abin ya zama laifi a gun mahaifiyarsu. Ganin ban kulashi ba yasa shi fadin ke Rahama kada ki bari raina ya baci dake gurin nan badake nake magana bane wai ko sunyi dakene yanzu ? Jin abinda ya fada yasa na kara dagowa na dubeshi cikin mamaki banga laifinshi ba kila son yana namiji yasa bai fahinci zancen daga farko ba. Ko kuma wata kila baiji farkon maganan tasu bane sai tsakiya yasa yake fadin zancen bai shafeni ba ai ni dai na hada kayan na koma falo na zauna na barshi nan. Tunane nakeyi a raina ya zama dole nasan yadda zan daukarwa saratu mataki ta daina aibantani ga bakinta a yadda na fahinci maganan ta dai shine. Ina fakewa da cewa ina jinyar yaya ga hakan na shammaci abokan zamana ina kwana da miji ni kadai har ciki ya shiga ba yau ta fara fadan hakan ba karo na biyu ke nan da irin hakan ya faru. Wata rana muna zaune a haraba ana hira ake bada labarin wata wai bata da umma asalinta me saratun zata fada daga inda take zaune tana dakilan waya sai cewa tayi ai ance basu bane shegu. Shegu suna gidan aure inda ake daukan kwanan wata a samu ciki a haifi mutum wanan dan da aka haifa ya zama shege sune shegu na asali da akasani ba wai wanda aka haifa a wajen iskanci ba haka ? Wanan abin ya tsaya min a rai tun lokacin duk da maman tudu ta tsawata mata don ta katseta da fadin to malama inji wano nafsin ya baki wanan fatawan kuma ? Kinhanki saratun nan a yanzu kan gaskiya baki iya zama babban gidan mu saidai ki koma rabe rabe a nan tunda har kin san wanan kikaki kawo miji kiyi aure ki huta. Ai mama Allah ne bai kawo mijin bata fada cikin tsigar rashin kunyarta datakewa mutane nan mama ta rufe ido tayi mata tas a lokacin tace sai inci ubanki wajen nan niko uwarki bata fada min maganan banza haka ? A wanan lokacin har mama tayi fushi tana fadin gida zata koma bata zama tana kallon wanan fitsaran haka saida sukai ta bata hakkuri shine yazid ya kusa halakata din a lokacin sai kuma wanan karon da ta sake maimaita abin shigen hakan. Tunda na zauna a wajen baiyi magana da kowa a cikinsu ba ga Asmau sai maimaita abinda Saiba ta fada mata takeyi amma hakan baisa na tanka masu ba don zuciya daya zo min a lokacin. Ba karya nasan ina da wanan zuciyan wanda idan nace zanyi magana a lokacin tabbas hakan zai iya jawo muna gagarumin rigima a ranan. Saidai kashh jin yadda Asmau ta matsa da zancen har take fadin indai don wanan da akeyi yanzune ai ba ai komai ba balle ko a gabana akeyi hakan bai taba damuna ni. Ai yin ma isace idan fitsari banzane kaza tayi mana Allah ne sheda ta koda hakan ya faru nasan kaddaratace a hakan amma a cikin kiyayyewa nake don ni din ba jahila bace kamar wasu nasan abinda nakeyi ban shiga hakkin kowa ba har na samu wanan cikin . Da za a zauna ana fada min magana inma shegen ne nayi tare da yayanta muka aikata hakan don ba zina naje waje nayi ba balle a zauna a fada min magana haka kamar nice farau. Sai a bari tunda yaya yana kwance nayi cikin idan na haihu aje asibiti a auna dan idan ba nasa bane sai a ban in tafi da abina . In kuma nasane zan shayar daku mamaki a gidan nan don sai nayi karan saratu a wajen hukuma na bata min suna da take kokarin yi a gidan nan. Yau dai ko saratu kishiyatace ya tsaya a hakan irin abinda take min kawai ta koma can gidan takama daki daya mu zauna a matsayin kishiya da ita insan zaman miji daya mukeyi da ita a gidan nan. Naji ina cin amanan su saidai zaki bada dalilinki gobe gaban Allah don ba yafe maki zan taba yi ba saratu sai kin fadawa Allah cin amanan da kika sheda nayi masu a gidan nan. Ke kuma Asmau indau zuwa duban yaya da nakeyi gidan nan ne na daina daga yau ba zan sake leko gidan nan da sunan gaidashi ba balle na kwance maki mijin ki duk ranan da Allah ya bashi lafiya in zai iya zuwa gidana yazo idan ba zai iya ba kuma yasha zamanshi nima nagaji da wanan wahala haka . Na juya zuwa ciki na kwaso kaya ban ko kalli inda yake ba balle su mama get din gidan na nufa na fice ban sake juyowa na kallesu ba . Yau nasan yarinyar nan tsatsan bafulatanace ashe haka ai basu iya fada ba ransu bai iya baci ga abu ba to yanzu dai ankai ga yadda ake so ai ina kula yarinyar nan ko zuwa tayi gidan nan an kama sakin magana ke nan ana mata haibaici tana sharewa tun farkon lamarin nan . Shin garekune farau zama da matan yayyu koko kun zama yan idone da ba a kwaba muku ku auren dai ai kowa zaije yayi yaji abinda ke cikinsa. Ba yarinyar nan ba koni yau zan bar gidan nan tunda Jafaru ya fara samun lafiya nake ganin abubuwa daban daban daga gidan nan hadewa kawai nakeyi . To Alhamdullahi tunda Allah ya bashi lafiya a yanzu Allah ya kara mikar muna dashi lafiya amin daga kofa ya dogaro yana fadin ta wuce ko ? Maman tudu tace dole aita wuce tunda sherin har yakai na sheganta mata abin cikin cikinta a gabata kuma ba a dauki wani mataki ba ko nice ai zanwa kaina gata. Saidai ku sani yau abinda baku sani ban kan yarinyar nan tayi abinda duk cikin mu nan kaf babu mai iya yinsa ga yaron nan. Itace zata hana kanta barci ta kwana
Chapter 227 · 0% Book details