← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 249 OF 306

Sashe 249

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

taga kin tsaya kinyi karatunki tasan zaki zama wata abu nan gaba a cikinsu. So ina son ko baki dauki shawarana dukka ba Rahama kiyi amfani da wasu don Allah a karshe takaini wajen gyaran jiki aka lugudeni tas na fito kamar bani ba . Anan take fadin ki kula ki dinga shigowa kina gyara jikinki ko nan ko kano din duk da nasan zarian ma ba za a rasa ba amma ba zaikai nan dinba ai. Kamar yadda ummah ta sheda min wanan sister din daddy da muke kira da gwaggo Laraba itace dasu anty Nuratu suka mai dani gidana na kaduna ranan jumma,a . Nayi mamaki kwarai yadda naga yan sauye sauye a gidan anyi min hakama wajen gidam anyi sabbin abubuwa na zamani a haraban wajen gidan. Saida aka fito daga jumma,a sukai shirin komawa kaduna a lokacin kuma ya bugo min waya yana min barka da jummah yake fadin sun fito daga sallah yanzu ya dora da fadin. Watau har satin nan ya shige Rahama bakiji tausayina kin dawo ba ke nan Allah ina wahala rashinki a kusa dani sosai Rahama goben nan zaki ganni a kaduna ai. Idan kaje ka gaidasu nikan ina zaria yanzu haka tun karfe shadayan rana muka shigo garin nan nidasu anty Nuraru. Kina ina yanzu na sameku nace gidana a takaice sai naji yace wasa kike min dai ki dawo garin nan ace ban sani ba Rahama ? Duk da ina daurewa a yanzu don fada da nasihan danasha a kanshi na dan daina jin haushinsa da nake ji kamar farko amma hakan bai hana na dankara mashi magana ba. Don Allah wai da gaske kin dawone ya sake tambaya nace kazo ka gani mana yanzun nan ma su anty ke shirin komawa kaduna su. Ina jin yana fadin kai mu gani koda gaske takeyi ya kashe wayan tashi da sauri muna falo suna batun fita suka shigo shida Yazid. Har yanzu dai saida dabara tafiyan nasa haka kuma kallon daya zakiyi mai ki fahinci yana sauran jin jikin nasa karfin haline kawai yakeyi irin na dan adam. Fuskamshi kyam a nawa yake fadin wallahi na dauka wasane kike min baki dawo ba suka shiga gaisawa dashi gwaggo tayi mai nasiha sosai kafin ta mike tana fadin Allah ya bamu alheri. Sun tafi Yazid ya rakasu har gidan mai ya kara cika masu tanki da mai ya kuma basu tukwaicin kamar yadda dan uwan nasa ya umurceshi dayi garesu. Muna falo zaune dashi mama ta kira wayansa tana fadin wai ina kuka tsayane baku dawo kunci ahinci ba kasha magani ga wanan mutumin yazo fa ? Ina nan gidana mama gidanka naji ta tambaya da mamaki yace eeh wajen Rahama data dawo yau nazo daga masallacin inyiwa wa yanda suka rakota godiya. Ta dawo fa shine zata wuce can gidan don ta raina mutane muryan Saratu ce karara a wayan take fadan wanan magana ga uwar. Kallon juna mukayi dashi kafin muryan mahaifiyar tasu race dashi ke nan basu kawota nan ba sai can gidan suka ajeta wai ko sun manta kana da uwane wai ? Kit naji ya kashe wayan ya kalleni yi nayi kamar ban fahinci me hakan ke nufi ba yana nan zaune muna dan hira jefi jefi har yazid ya dawo ya daukeshi nake fadin. Ya kira yaya Ai ya sheda masu na dawo a turo min Biba yace nayi tunanen hakan nima anji zan zo da ita insha Allahu suka fice a gidan sai annashuwa yakeyi da kaninsa yazid. Bandai nuna a gabanshi zancen saratu yaci min rai ba da alama kuma har mama ta hau zancen saidai na share kawai na nuna ba komai a fili kamar ma banji ba. Ya zama dole a matsayina na diya mace in kara hakkuri in daure in dinga shanye duk wani bacin rai da iskamcinsu yanzu tunda nasan manufarsu a kaina yanzu matukar ina son zama da mijina lafiya. Wanda su basu ko iya boyon hakan har salima din da muke dan shiri wani lokacin bata iya boye hassadanta a kaina saita fada a cikin wasa. To tunda na fahinci Basu da wani guri saidai suga an samu matsala a tsakanina dashi ke nan tunda na fahinta zanko tura masu haushinsu akai a yanzu zan nuna masu kan mage ya waye ashe ? Duk da bansa a raina zai dawo gidan ba a ranan don yadda naji kalamin mama da nayi sallah la,asar na fito na gyara gidan tsab duk da ba wani datti na feshe ko ina na rufe window da kofa tunda sanyi akeyi tuwo kawai na dora don ummah tasa saudi tayi min miya mai yawa nazo dashi . Ga kuma soyayyen nama da sauran abin bukata don haka aikin ya rage min a lokacin ina kwance falo muna waya naji horn din motarshi gidan yazid ya kawoshi. Bibace ta fara shigowa sai su a baya da gudu tazo gareni tana rugumana nayi murmushi don naji kewam yarinyar sosai dan rabuwan da mukayi din. Nan yazid ya zauna yake muna sheri donshi akwai son barkwanci damu haka don koda su Asmau nakanga yana dan taba hakan saidai ba kamarni ba da sosai yake wasa din dani. To ni zan tafi yau akwai sanyi wallahi ga sahiba na barta ba lafiya na fito yau dai za a barni na huta tunda madam ta dawo yaya . Zaka koma ka samu jidalin mama kuwa don dai nasan yau kokai ba za a barka ba wajen fada haba dai ina jira ai sai kaji na balla yarinyar nan saratu zuwa gobe idan tayi wani rubishi akaina zanci kaniyarta sosai wallahi. Biba je kitchen ki debi abinci kici nace don basar da zancensu nan yazid din ke fadin what dama iya ta fada ai ko jiki ka mayar a yanzu. Don Allah Yazid idan ka koma iya ta shiga cikin gida ta kwanta don kada a barta a nan ita kadai kwanan nan duk bata kwana da dadi wallahi zazzabi yake damunta a cikin dare haka muke kwana da ita. Abinci fa na fada ga yazid din yake fasin naso in zauna naci abincin nan amma kuma ina gudun makara me kika dafa mai nasan yau ai sai didima a gidan nan. Murmushi nayi ina fadin tuwone kawai donshi nake so shi kuma nayi yace a zubo mai yaje dashi hakan yasa na mike na hado mashi tuwon ya tafi. Saida na zauna nake fadin iya ba lafiyane kuma yace wallahi takai kwana biyar a hakan kafin yaci gaba wayanshi ya dauki ringing lokaci guda ya dauka yana dubawa. Mamace take fadin Jafar ina ka fita da sanyin nan kuma nazo baka shiyanka mana ya bata amsa da fasin gani nan yazid ya kawoni gidam Rahama. Sai naji tace dashi gidan Rahama kuma da daren nan wai kanka daya kuwa daka je can din maganin kafa da sanyin nan ka kwashi kafa zuwa gidanta don kawai ta dawo a yau kome ? Mama wanan ba abinda ya shafeki bane fa ni hakan ya shafa Rahama matatace kuma dole inzo gidanta tunda Allah ya ban lafiya a yanzu. Anzo inda ba a son azo din ranan da zai fara ba mama amsa irin haka dama daddy ya fada a karshe zata gusar da wanan biyayyan da yake mata ita da kanta lokacun daya fara hakan kuma ba zataji dadin shi ba kuma.
Chapter 249 · 0% Book details