← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 306

Sashe 124

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

4️⃣5️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

Mummy zulaihat Allah ubangiji ya baki lafiya yasa hakan ya zamo kaffarane a gareki ubangiji Allah yasa anyi aiki cikin nasaran ubangiji Allahuma Amin ya Allah.
Mama Amina kema Allah ubangiji ya baki lafiya yasa kafarane yasa hannu ya warke a cikin kuduran ubangiji Allahuma amin sauran uwayena da bab kira ba da yayyun mu ya Allah ka basu lafiya masu damuwa Allah ka yaye masu kamai dashi alheti a garesu Allahuma amin jumma,at mubarak gareku yan uwa musulman duniya.
Fada yake sosai gaban matarshi hafsatu tana kara zugashi akan Habu wanan karon fushinsa ya sauka don Habu din yake zagi saboda yana ganin shine ya kawo mashi cikas a ranan.
Idan badon shawaran da habu ya kawo ba da duk yadda akayi a ranan saiya mallaki wani abu daga cikin kudin nan ranan.
Amma ga kudi yana gani ido da ido amma dan banzan yaron nan Habu yai masa bakin cikin su shigo hannunsa saboda wata akidarsa ta banza dayace wai sai ankira wasu malamai can .
To kai malam waisu yaran nan dake gagawan fadin yadda za ayi da tasu kason a sakebawa yayan nasu me suke nufi da hakan yanzu matarsa hafsatu ke tambayashi cikin katse mashi tunanen da yakeyi.
Sai daya nisa ya kallota ta sake fadin yanzu kyalesu zakuyi da shawaran ya asake karban kudin kuma a hannunsa ?
Kafa san idan suna hannunsa ba zai yarda agani ba balle a taba yakamata kayi wani abu akai hakana malam koda baka da gadon mai fata ai kaima dai ka wahala dashi gashi
Yaron nan Jafaru fa malam kana sane ko kashi ya rika ya shiga kasuwa dashi sai sun zama kudi a wajensa na rasa wani irin albarka Allah yaiwa yaron nan haka ?
Dan banza gashi da iya boyon kurwa wai ace akwai wa yan nan kudin haka amma yake daukan dan kudi ya mika maka kaine baka iya kashin kudi ba ke nan ?
Abin ne da daure kai kema kin sani hafsstu ba irin karba da bayin da sunan yaran nan amma kamar ina aika dutsene ba abinda suka canza saima gaba gaba suke karawa.
Wai, kinji yaron nan ashe harda gidaje yake kokarin ginawa yan uwansa bai fadawa kowa ba sai yau din nan yake fada a wajen haduwar nan.
Sai nake ganin yanzu kamar ya fara fahintar manufarmu akansu don ya fara yin abubuwa ba tare da sani ba da farko ba haka bane na samu kansu fiye da tsamanina.
Amma sai gashi yanzu da nake hango kudi sun zauna mashi haka yana kokarin ya juya min baya a tafiyan yanzu.
Harshi ya isa malam wallahi bai isa ba komawa zakayi a kara nemo makashi a hannunka sai yadda kayi dashi a rayuwansa .
Shi wanan Habu dai tauraronshi bai haskawa kamar nasa nake gani don har yanzu bai kaiga samun irin na Jafar din ba amma duk da hakan tunda bakinsu gudane shima ba barinsa zakuyi ba ai malam.
Dole ai insan abin yi a yanzu ya zama dole na sake sabon shiri akansu kafin komai ya jagule muna don ina ganin wancan na farkon ya dushe .
Kwance ya sameni da waya a hannuna har barci ya soma daukata lokacin ya shigo cikin dakin da sallama tsaye yayi a waje daya yana kare min kallo kafin ya tako zuwa bakin ya karbi yawan yana dubawa gamen din engela yana ta playin da kansa.
Dan murmushi yayi yana kashewa kafin yakai zaune a gefe daya yana aje ledan daya shigo dashi a hannunsa sai lokacin naji motsin zaman mutum a kusa dani na dan zabura kadan naganshi .
Komawa nayi ina sauke numfashi tare da dago fararen idona na kalleshi ina furta sannu da dawowa a bakina .
Sai naga ya lumshe ido yana amsawa yace har kinyi barci by this time sorry na tsaya da iyane ban fargaba ashe lokaci yaja haka ban sani ba.
Allah sarki Iya suna lafiya a cikin hamma dake nuna kasala ya amsa da lafiya lau suna gaida ke nayi dan murmushin da nasan zan tsokaleshi na yunkura da niyar tashi zaune .
A lokacin naga ya dadirce da kyat ya iya sassauta muryansa yake fadin ina jin yunwa fa Rahama ?
Na juyo da sauri ina fadin kace kada nayi girkin dare kuma yace ehh muje falo ki ban abu yana can na aje hakan yasa na yunkura na mike zaune daga kwancen har jikin mu yana gugan juna dashi na samu na mike tsaye.
Zanin dana daura saman rigar barcina na gyara dauri zan fita ya bini da kallo tare da ajiyan zuciya ya mike ya fito falon shima ledan na hango saman center table din falon na nufi wajen ledan har na duka zan bude kuma na dago zuwa kitchen na dauko plate da su knife da ruwan wanke hannu irin wanan sallon mazan nasanshi a gidan anty sallama ai.
Na samu ya zauna ya baje saman kujera irin zaman a bude kafa din nan ya dafe goshinshi da hannu dayan shi yana murzawa.
Na duka na fara kiciniyar budan ledan naga take away irin wanda kake iya hango abinda ke cikin roban da alama dai kamar ganyece da wasu tarkace haka.
Saidana bude naga rabin kazace da ganye da aka gyara yaji hadin turawa sai dan shinkafa manne a gefe daya ko wani roba haka yake da abin.
Dayan ledan na jawo dake ta maiko da kamshi kayan cikin ragone a cikinsa mai yawa sai kamshi yakeyi anyi mai irin gashin zamani din nan dayan kuma shima dai namance ta rago gassassa a cikinsa yaji su albasa da kabeji da kayan kamshi.
Saidana gama hada komai yadda ya dace na dago kai na kalleshi ina fadin bissimillah yaya sai naga ashe duk hankalinsa yana kaina shima a lokacin.
Sai naji yace ki zauna tare zamuci ai dake nasan bakici komai ba na noke kai cikin kunya ina fadin idan ka gama zanje daki inci ai.
No no wai kunyata kike jine yana magana yasa hannusa daya ya jawoni zuwa jikinshi ya zaunar dani saman cinyarshi.
Noke noke na farayi ina kokarin zullewa don hakan da yayi min din bakon abune tunda ban saba hurda da namiji ba haka ko yan uwanmu maza ba tare muke rayuwa ba a rugga yunda su suna yawon cinrani.
Kokarin kaimin a bakina yake a dole saina karba na dai karbi na farko amma taunawa na kasa hadewa a gabanshi ga idon daya tsura min wanda yasa na fara kwarewa lokaci guda.
Ruwa ya miko min na dan kurba bai duk da haka bai yadda ya sakeni ba a rikon da yayi min dole ba sarki sai Allah na biye mashi ina karba a kunyace ina hadiyewa a cikin kunya.
Saida yaga na koshi ya barni na koma gefe ina kallonshi yadda yake cin abincin ya tabbatar min daba karamin yunwa yake ji ba lokacin.
Ya gama na kwashe kayan zuwa kitchen na dauraye na fito har lokacin yana zaune yana waya a wajen dana barshi daki na nufa harya gama wayan nasa ashe barci ya daukeni.
Har ya gama ya shigo dakin ban sani ba a cikin barci naji ana tabani hakan yasa na dan yi niyar dagawa sai naji ya matseni a jikinsa yana wasu maganganun da na kasa iya tantancesu a lokacin.
Ga kasa daya dora a kafadana ya sakarmin nauyinsa ban gama mamakin hakan ba naji yana sumbatar wuyana hakan jikinane ya fara rawa lokaci guda.
Abinda ya kara dumatani jin wasan yau bambanta dana dareb jiyan da yake min yafi na daren jiyan don ya bambanta da wasan da zan tsaya fada da baki a nan.
Sai karfe shida da rabi ya samu sallah safe balleni da saida nayi da gaske na iya lalabawa zuwa bandaki na tsabtace jikina.
Ga zuciyana da tayi min wani irin nauyi da ba zance ga daliliba don nasan wani abu daga rayuwata ya tafi ke nan sabon rayuwa yazo min a yanzu duba ga yadda bani samun natsuwan barci a dan tsakanin nan.
Har na idar da sallah na samu na mike na gyara gadon na sauya shimfida da kyar na koma na kwanta don zazzabin da nake jin yana son kamani a lokacin.
Hakan yasa ina gamawa na koma na kwanta da niyar gari ya dan kara wayewa in daure in fito kitchen ashe barci ya daukeni mai nauyi irin barcin wahala din nan bana dadi ba dai kam.
Sau biyu yana shigowa dakin yana samu ina barci gashi ko karyawa banyi ba ga abin kari dsyasa yaya Habu yazo muna dashi tun safe.
Har yazo suka dan zauna kan zancensu da mama ban samu ganawa dashi ba a lokacin yaso ya ganni mu gaisa koda yaya ya duba mashini har lokacin ina kwance jikina yai zafi kuma ban falkaba balle insha magani.
Har yaya Habu din ya tafi shima ya mike zuwa dakinshi yayi wanka ya dawo nawa dakin still ina kwance a takure ina barcin .
Ya tsaya ya kura min ido na dan lokaci kafin ya kai hannusa a saman jikina yana taba temperature dina yaji jikin ya gashe sosai a lokacin.
A dimauce ya fara kiran sunana a hankali hakan yasa na bude idanuwana a cikon nauyin barci na sauke a kansa yana zaune gab dani ya dan rankwafo jikinsa zuwa nawa yake fadin.
Rahama baki da lafiyane haka har sosai shine baki fada min ba muje asibiti ?
Idona dake lumshe na kara dan budewa ina fadin idan nasha Panadol zan warke basai naje asibiti ba..
No tashi dai muje kiga doctor zaifi ga jikinki yayi zafi haka kice in barki a gida ?
Bari nasha magani idan bai bari ba sai muje asibitin na fada ina kokarin mikewa cikin karfin hali.
Ina zakijene wai na bashi amsa da magani zan dauko a jakkata ina jakar take ya tambaya yana kallona don duk maganan da mukeyi dashi tun shigowan shi idona a runtse yake na kasa hada ido dashi.
Gaban mirro yaje inda na nuna ya dauko maganin da goran ruwa ya dawo yana mika min dakyat na dago kai zan karba a cikin kunya.
Yake fadin toki bude ido mana ki karba ya zauna gab dani jikin mu yana gugan na juna dashi na sakeyin kasa da kaina.
Murmushi naji yayi yana fadin Ok har yanzu kunyane to bari na sake fitar da kunyan taki donki daina jin nauyina gaba daya don naga kamar da sauran ki har yanzu.
Da sauri na kalloshi wanan karon ina fadin wallahi ba haka bane kawai ba zan iya bane nayi kokarin komawa saman gado don yanayin jikina.
Yayi murmushi yana dafa goshina ya bare maganin ya bani nasha ya mike yana fadin ina zuwa falo ya fita ya hado min tea mai kauri ya kawo min saida ya tsureni nasha ya fita da kofin na koma na kwanta.
Barci na koma ban falkaba sai wajajen sha biyu da rabi har lokacin yana gida ranan bai fita ba shima barci yayi ya rufe gidan don duk wanda yazo ya koma ya umurci maigadin daya rufe gidan kada ya budewa kowa.
Jin motsin falkawana na shiga bandaki yasashi bude idonshi daga kwancen da yake yana barci a gefena kafin na fito na samu ya kunna wayanshi daya kashe.
Don tunda zai kwanta ya kashe wayan don kada a dameshi barin maganan da yakeyi da wanda yake wayan yayi ya dago yana fadin to ya jikin naji zazzabin naki ya sauka tun dazun ?
Da sauki na bashi amsa ina zama bakin mirro na don shafa mai saboda na tsaya nayi wanka a bayin kafin in fito.
Ya mike zaune da wayan saidaya gama ya tako zuwa inda nake ya karbi man ya fara shafa min a hankali na lumshe idona a cikin kunyarsa.
Saida yazo daidai kirjina sallpn da yake murza min man yasa na bude idona na kalleshi ta cikin mirro ido ya kashe min ta cikin mirro yana fadin in daina aikinane fa ?
Dariya ya bani da yasa na danyi murmushi a fili nace nagode yayi hakana ai shafa man ya isa malam.
Aikinane wanan don haka babu godiya abarni nayi da kyau nayi kasa da kaina kawai saida ya gama don kanshi yakai min kiss a goshi yana fadin bari na dan watsa ruwa nima tunda naga kinji sauki ya fita daga dakin zuwa nasa.
Chapter 124 · 0% Book details