Sashe 295
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana kwance aka fara dukan kofan da karfi taki budewa sai maishi ya wuce taja tsuki tana gyara kwanciya. Ba,afi mintuna biyu ba taji bugun kofan dayafi na farko karfin kara a kunnenta hakan yasata magana tana fadin wai waye don Allah zai fasa min kunne ? Ke ki bude da wullakancin banza ke shige daki kin kyale mutane ana buga kofa konki ki bude jin muryan minjinsu yasa ta mike da kyar ta bude kofan dakin. Ya fado ciki kamar an turoshi daga waje yana fadin wane irin iskancina yasa kinka hitowa a dora girkin abin kari dake ? Ke shige daki keyi kwanciyanki kin mike kafa wa kika son ya dafa ya baki kici da kinkaki hitowa a dora girki ko wa at bawanki gidan ga ? Nagajine Habibi nagaji wallahi ke dakata min don Allah ke gaji ba aure kin kazo yi ba ke nan koso kike ki kwanta daki ki mike kafa a girka maki keko ki kwashi gara daga kwance ? Habibi nifa ban saba da irin haka ba a gidan mu wallahi ban girki sai naga dama kuma baifi gwango biyu muke girkawa ba sai taliya da indomei ko macaroni. Kina mace kika rakin girki ashe saratu baki shiryawa aure ba kin kayi an fada maki zuwa dai akai aita harkan gado baci waka baki abinci kina kwance ? Nifa habibi gaskiya ba zan iya ba don wallahi,,,, dakata min don Allah ba habibiba wallah habibu in kina hitowa kitai girki yara suna jin yunwa ki hito ? Wallahi ban iyawa ta kara fada tana juyawa yace haka kinkace baki iya girkin tace gaskiya indai wanan girkin gandune ba zan iya ba ? Wai baku hitowana kaje ka zauna kana rarashinta a daki kunyi bukui cikin daki wa zaku kawowa bulunkoto a nan ka shiga kana rarashinta akan ta hito wa kunka aje bawanku halan ? Duk yadda ya raya saratu taki fitowa dakin jin muryan uwargidansu da tayi a kofan ya kara bata haushi mata yar tsurut da shegen doka ga iya kissa da kisisina irin na mutanen hausa. In an barta sai tace itace uwar yan daudun duniyan nan kaf saboda marmadin ido da iya tafa hannu idan tana magana baki magana hannci magana ido magana. Bayan fitan mijin taji muryan uwargidan tasu da ake kira da nunu tana fadi a cikin fada taki hitowa ko to walle mu zuba da ita a gidan nan wa taka son ya girka mata taci ? Ko wa a bawanta gidan ga ta iya shigewa daki ta kwana da miji a girka mata yanzu aiki yazo kanta tace batayi asheko zakiga iskanci a gidan ga walle ? Ta mede baki tana zama bakin gadonta cikin takaici da dana sanin auren mansur da tayi inba don sulaiman daya taudareta yayi ta amfani da zuciyarta yaki aurenta ba a karshe da ina mansur zai ganta har ya kwasota zuwa nan ? Dama ance rabu da bakauye iskanci da duniyanci yana wurin bakauye tundai in yana ganin ya fara wayewa sai abin ya hade mashi da wawanci yayi ta abu ba fasali. Bata fito ba tana jin hayaniyan yan gidan har barci ya dauketa sai wajajen sha biyun rana da yunwa yacita ta fito don ta samu abinda zataci. Saidai ta kula duk dan data kira donta aikeshi sai yaro yaki zuwa don uwayensu sun gargadesu akan hakan sai wani saurayi ta samu maraji yaje ya kwaso mata indomei tazo ta sullala saman gas a kuryan daki taci. Jin kamshin indomei din da matan sukayi kuma yasa yan gulma samun uwargidansu suka fada mata ita kuma ta samu mijin da sababi duk ya rude irin matan nan ne dake kammala mazajensu sai abinda sukace gata dai bakauyace amma miji idan tana magana har rawa jikinsa keyi wajen bin umurninta. Shi kuma ya taso ya samu saratu din a daki da fada kan don me zata dora girkinta daban suba haka sukeyi a gidansu ba ta fito ayi aiki da ita yadda kowa ya fito a girka a zauna aci a cikin taro. Wanan halin yasa bata ko iya loma ukku da anfara zata mike tace ta koshi ita dan dama ranan da miji ke dakinta inyaci ya rage takan samu taci itama a lokacin. Ga wata rayuwa ta daban da sukeyi keda miji ke wajenki ba zakiyi girkiba a ranan sai wace miji bai dakinta itace zata girka abinci ta ciyar daku. Gashi kuma mata sunkai goma sha tara duk girkinsu a hafe yake mutum ukku ulku ke girki a rana su ciyar da gidan yadda suka tsara kuma komai da za ayi wajen uwargida ake karban komai itama hannun uwar miji zata karboshi. Irin wanan rayuwan na daban yasa zaman gidan ya karawa saratu kunci tayi tayi ta daure ta kasa hakan wata rana da dare bayan isha,i ta hada kayanta a dan karamin bag dinta makwabtansu takai ajiya. Washe gari ana fitowa sallah tayi kamar zata kewaya ban daki ta aje buta ta fice sai wanan gidan ta ari nikaf ta rufe fuska tana zuwa bakin titi ta samu mai acaba ya kaita tasha zuwa garin sokoto tashiga mota ta nufo sokoto inda zata samu motar zaria. Don tayi kiran mama don su kawo mata agaji ba abinda sukayi kullum magana dayace mama tace mata tayi hakkuri tana tafe an amma shiru. Allah ya gani tana son habibi shima haka amma yan uwansa da matansa sun bata masu shiri don a gaskiya idan tace zata daure tasan karshe zata halaka a wanan gidan. Don aiki kawai zai kasheta gashi bata saba hakan a gida mama tudu in tazo ko sukaje family house daniyar kwana biyu tankayi fada da mama tace ba aiwa diya mace wanan sakacin don ba,asan inda aure zaikai mace ba gashi ko bakinta ya kamata don ga inda aure ya kawota yanzu. Salima da tayi mutuwan tsaye don mamakin kalaman da take ji bakin kawu yasa ta koma da baya zuwa part din iya. Ta kwashe ta fadawa iya shine mafarin tasowan iya tazo ta samu kawu tayi mashi tas barci ta kasa kwanan ba haukan Nusaiba ya hanata barci a lokacin. Sai zancen da take ji yana fita bakin kawu din wanda da alama kuma uwarsu bata damu da hakan ba kamar ma bata gane manufarsa ba take gani. Allah Allah take gari ya waye taje ta samu yan uwanta ta labarta masu komai sai da tagama komai ta shirya batacewa kowa komai ba ta fita daga gidan . A waje ta ciro wayanta cikin jakka ta kira lanban yayanta tayi sa,a ya dauka yana fasin Salima yaya akayi ? Kana ina yaya gani nan zuwa wajen ka ya amsa da gani nan zanje gidan Rahama in dubasu lafiya dai ko ya tambaya ta amsa da yaya bari dai inzo akwai magana gaskiya. Ya shigo ke nan mama zata fita suka hadu a get Aminu zai rakata sarakuwarta ta haihu zata ganin jariri yace barin kaiki mama tace a,a malam kaje ku gaisa da iyalinka tun jiya ta damu bata jika ba jeka na yafe maka harga Allah ga Aminu nan zai rakani in samu mota. Hakan yasa basuje tare ba lokacin ya shigo ina falo don ban koma ciki ba yake sallama na amsa tare da gaidashi yake fadin kun jini shiru ko jiya? A kasalance na juyo ina fadin nina dauka baka garine ai don baka hakan ya kai zaune bayan yagamawa yaron dake bayan biba yana barci wasa ya juyo yana fadin. Ina nan ina jigilan wacan gidan jiya dai su Asmau sun tare a sabon gida ita da yara saura wanan idan na samu kudi ko a gyara maki ko kuma a gina wani don nasan ba zakisu zama a cikinsu ba ? Murmushi nayi na mamaki nace gida ka gina masu ashe yace an dade da ginasa ai gyarashine ban gama ba dama yanzu kuma an gyara din. Wanan kudin dana aje wanan gidan kwanaki aikin gidan nayi dashi kada kudin su salwance min ban more masu ba shiyasa ban fadawa kowa ba . Sallaman Aminu da Salima ya hanashi cigaba da magana inda ya juya yana fasin au salima kin karaso kinga na manta munyi waya dake fa yanzun nan kince kina tafe. Suka gaisa ta juyo ta gaisa dani nake mata takoma lafiya jiya tace lafiya kalau kedai na koma na iske rigima yaya ashe zaka kwashe baka fadawa kowa ba. Na koma na samu saiba na fada da mama tana fadawa mama maganganu muna tsaye saiga kawu kuma ya shigo duk basu ganmu ba dani da Hauwan ya yazid a duhu. Nace barin shiga shine fa na samu wani zance da kawu ke fada na ban mamaki amma sam mama bata damu da kalamansa ba balle ta tambayeshi me yake nufi da shiri ya baci wai ? Shirin me ya baci shima dan uwan ya tambayeta tace waya sanar mai yaya akwai dai abinda haka ke nufi ina fadawa iya ta mike ta sameshi cikin fada tadai kwashe duk yadda akayi ta fadawa dan uwan nata. Ina zaune ina sauraren ikon Allah ya nunani yace kin ganta nan itace mafarin lalacewan komai garesu yanzu idan kin kula tun shigowan Rahama rayuwana abubuwa suka canza a gidan nan. Dago kai nayi da dauri ina kallonshi yacigaba da fadin shiyasa kike ganin basu shiri da ita yana zuga mama akan Rahama tana hawa tana zaunawa tare da wanan shashashab Saratu. Ya san komai a yanzu matukar Rahama tana tare dani ba zai taba cinma manufarsa a kaina ba yasa kikaga ya koma kamar mahaukacin zaki yanzu. Nasani Salima nasan komai har abunda shi kansa bai sani ba duk an fada min duk ciwon nan da kikaga inayi Allah ya nufa sai nayi amma da hannun kawu a cikinsa. Ta kwalo ido waje cikin tsoro tace mayene ke nan ko yace ba maye bane amma yana kama dashi don mugun mutumne sosai wanan matar nasa ta halakashi da yawa. Ba zan boye maki mamace basu so da karuwa sun kulle bakinta ba zata iya magana ba akansu koda ta gane abu saidai ta bisu kawai ba zata iya fada akanshi ba. Salima abu tun muna kanana akeyinsa har yanzun kuma basu daina ba ki rabu da wanan