Sashe 212
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sam bata kaunar yarinyar nan da alheri ko kadan wallahi. Daga inda iya take zaune ta karbe da fadin ina zata kaunaceta tunda sheri yana ranta ita saratu watake so Amina ai banda wanan mara kunyar da halinsu yazo daya banga wanda saratu ke kallo da gashi ba gidan nan har yan uwan nata kuwa. Abu kamar asiri zakice yarinyar nan ta asircesune ita da uwarta yadda suke kafa kafa da zancenta yanzu ba taji hakan ba tana fita zakiga takai zancen nan wajen ta su dinga yiwa yarinyar nan kwakwaf inma cikinne ai Allah ya kawo abinsa. Ina lafe ina jin duk abinda suke fada a lokacin gabana ya soma faduwa ina tuna taraiyan mu da yaya a asirce wanda mukeyi a yan kwanakin samuwan saukinsa wanda daga Allah sai mu muka san abinda muka aikata din . Kai ina hakama ba zai yuyu ba har wani abu mukayi da za ace ciki ya shiga ga hakan mutumin da baida lakkan wani abin kwarai karfin haline irin na maza da yan adam kawai na kwakwa a wajensa. Barci nayi abina bansan wainar da ake toyawa ba a gidan saida wani zazzabi ya tayar dani na falka ina makyarkyata babu kowa a part din sai mama da shi dake kwance dakin na koma wajenshi na kwanta agefensa na dunkule. Ya zuba min ido da kyat ya mika hannunsa a kaina jikina ya gashe yayi zafi kamar garwashi ya soma fadin on tashi a kaini asibiti sai naji sam banson zancen wani asibitin nan da suke min kamar yana son a kara tsanatace a hakan gashi na fara jin zancen banza a bakunan su duk da banda yakinin cewa ga matsalata nasan kuma zazzabine kawai na wahala ba komai ba yake damuna. Shigowan mahaifiyarsu part din don ba kasafai take zama ba a nan saboda mama dake mata kara takanas ta baro komai nata ta dawo nan ta tare saboda danta dole ta kawar da ido tayi kawaici akan hakan dama kowa yasan jafar dan maman tudu ne inbada dan hatsaniyar rabon gado ya dan shiga tsakaninsu ba a kwanaki bayan rasuwan mijinsu yanzu ko an daidaita hakan an koma kamar komai bai faruba a baya. Yar nan ku kaita asibiti fa muryan mama dubu naji tana fadan hakan a gefe taci gaba da fadin ciwon nan kada yaci jikinta duba yadda ta fada a cikin kwana biyun nan ? To shi dai da zai kaita gashi a kwance yana fama da kansa tun safe yaiwa Yazid magana tunda ya fita da motan bai dawo ba tun dazun. Dama yazid zai kaita aiko dai ya fita da nasa iyalan tun dazun nan J din ya fara danniyar fadanshi akan dan uwan nasa a cikin karfin hali ya jawo wayarshi ya tura mashi text ba a jima ba sai ga yazid din ya shigo yana fadin afuwan madam mijikin ya hauni da fada na bar mashi mata na ciwo a gida ? Sannu tashi muje asibitin please ba zai barni in huta ba yadda ya hasalan nan dani yasa kai ya shiga dakin wajen shi na mike ina son shiryawa mu fita. Tare da mama muka tafi asibitin itace tayi min rakiya zuwa ganin likita da zanyi ancewa na kawo fitsari aka kuma debi jinina tun lokacin nashiga damuwa . Ni abu biyu najiwa tsoro na farko kar zancen ciwon ya J ya zamo gaskiya abinda kawai ya fado min a rai ke nan yasa sukace zasu dibi jinina . Munyi zaman jugun muna jiran sakamako saigashi anfito dashi ankaiwa likita Yazid ya shiga akai mai bayani cewa ai akwai shigan ciki a tare dani dan wata daya. Abinda yaba likitan mamaki shine da yazid dake fadin likita kun duba da kyau kuwa don mijinta fa yana kwance baida lafiya almost eight month ke nan yanzu. Shine me hakan bai iya ganetane ko bai sheda kowane har yanzu jin hakan yasa yazid din yin shiru na dan lokaci ya mike yana murmushi sukai sallama da likitan bayan ya bashi takardan da za a sai min magani. Tunda ya fito yake min wani irin kallo daya sani tsarguwashi dan irin yadda yake kallona din mota muka koma nida mama muka zauna shi yaje sayen magani. Ya dawo muka bar sibitin saida muka dauki hanya da kyau naji yace mama akwai matsala fa don nasan za ayi tsiya da sauran yayan ki idan suka samu labarin abinda ke damuwar yarki. Subbahanallahi akan me za a samu matsala kuma wai wasu yayan nawa kake magana ban fahince ka ba ? Mama ki barshi kawai har mu isa amma sai anyi da gaske don kada hakan yajawo rikici barin dan faka in sayo mata lemo ko zataso shi nan ya tsaya ya fita naji mama din tana ajiyan zuciya. Kodaya dawo bai kara maganan ba har muka isa gida don waya da yakeyi a cikin harshen larabci mota na tsayawa na sauka na barsu da mama din kodana shigo falon ba kowa hakan yasa na nufi daki kai tsaye. Nayi sallama na shiga yana zaune da matanshi ranan Nusaibace tayi girki tana zaune tana bashi abincin don angamashi late evening sosai . Ina shiga sukayi min ya jiki shike tambaya da hannu yaya nace da sauki na samu waje na zauna saida yazid ya shigo min da magani da kayab marmarin da ya sawo muna mai yawa ya aje a gabana yana fadin. Ki kula da shan magani likita yace asha na kwana ukku a gani idan bai bariba a koma Allah ya sauwaka yace zai leka part dinshi ya dawo. Sai bayan ya tafine anty Asmau take min sannu da jiki na amsa gami da murmushi ina gyara kwanci shigowan mama tayi muna sannu da dawowa take tambayan yaya jikin nawa ? Tunkan in bata amsa ta juya wajen mama tana tambayan me likita yace wahalan jinyane ko ke damuna sai mama tace anya ban tsamanin hakan gaskiya ? Don yazid dai akaiwa bayani an kuma auna fitsarina da jinina akai gwaji shinema ya tsayar damu bamu dawo da wuri ba. Awon fitsari kuma sai kace mai ciki daga zazzabi Nusaiba ta fada maman tudu ta amsa da fadin abinda nake tuhuma ke nan saidai ban san me sukace dashi yazid din ba. In ma cikin ne dai Allah ya raba lafiya ya kawo masu albarka haba dai sai kace wasan yara mama don Allah ku bari dai ina zancen ciki yanzu mijinta na kwance haka ? Anty Asmau ke fadawa mama haka cikin katse mata zancen da takeyi din ita kuma saiba cewa tayi haba dai ciki a yanzu haka kuma drama ke nan ai ? Ta fada tana wani mere baki ta juya zuwa cikin daki ta samu mijinta don itace da girki a ranan ni dai ina kwance ina jinsu bancewa kowa komai ba. Saidai a lokacin banda natsuwa don maganganunsu sun fara tsaya min a raina na fara tunane barkatai a kan hakan ina yanke shawaran nisantan shimfidan yaya a wanan maran kada wani abu yazo ya auku dani inga boni. Yazid bai shigo ba sai bayan sallah isha,i ya shigo ya samemu dasu mama sai anty Asmau yayi min ya jiki ya wuce zuwa wajen dan uwansa dake daki ya shiga ya samu dan uwan nasa yana sallah ya zauna zaman jiransa. Bayan ya idarne suka gaisa dashi nan ya zauna suka dan soma hira kafin ya fito mashi da zancen daya kawoshi wurinshi din da farko cewa yayi dashi. Ya dan uwa baka tambayeni abinda asibiti sukace game da matar kaba dazun da mukaje don dana dawo akwai mutane a lokacin kuma maganan yana son in fara kebewa dakai tukun. Ya dago ya kalli dan uwan nasa alaman meya faru a fuskanshi yace don gaskiya gwajin da akayiwa amarya ya nuna tana da shigan ciki na wata daya a jikinta shine ke bata matsala a yanzu. Cikin muryansa daya koma kamar a karye ya zaro ido yana fadin kana nufin cikine da Rahama yazid din na kallon yanayinsa yace cikin gyada kai haka sukace dani gama takardan daya bada result din nan. Ya fito dashi ya mikawa yayan nasa dan murmushi yayi ya karba yana bin takardan da kallo kafin ya tura karkashin filon da yake kwance. I hope dai kasan da hakan ko kada rayuka su baci daga baya kai kawai ya dagawa kanin nasa ya mayar da idonsa ya lumshe har dan uwan nasa yaso ya fita. Saiga mama ta shigo dakin tana fadin ashe ka dawo yanzu naga mota a waje dazun da kuka dawo ance kuma ka fita yace ehh na shiga garine . Yanzuma sakamakon asibitin na kawo mashi to maleria ne ko yake damun ta yace a,a kamar dai cikine sukace ga dai takardan nan hannunshi nabashi. Ciki ciki name cikinta ke ciwo kome donni ban fahince ka ba ai kayi min magana haka a dunkule yace mama me kike son in fada maki yanzu tunda nace ance shigar cikine da ita yake sata zazzabi haka ? Cabdi jam ciki ciki fa ita kuma yar nan a ina ta dauko ciki kuma a wanan lokacin badai cikin Jafaru bane ko da sauri Yazid din yace wa,iyazu billahi mama ke kike wanan maganan kuma kanar wace bata da aure mama ? Hakan ya jawo hankalin mu a falo harsu mama suka taso da sauri zuwa dakin suna shiga yazid na fitowa mama na biye dashi a baya. Tana fadin kuji min wanan zance don Allah wai yarinyar nan cikine da ita ashe take wanan laulayin haka ina Rahama din takene wai ? Kiyi mata me zuwa zakiyi ki tambayeta dubu ta yaya ta kwanta da danki kome kike nemanta kiyi mata yanzu ? Asmau dake zaune a kusa dani dakin mama ta mike tsaye da danta a hannu tayo waje ta saurara abinda ake fada lokacin mama dubu tana fadin. Haba iya wanan ai abin a tsaya a dubane yaron nan kwance fa yake rai a hannun Allah ta yaya zamu ganta da ciki ace hankali ba zai daga ba kuma ? To kina da ja da ikon ubangiji ke nan dubu ko kin isa ki hana Allah ikonsa yadda yaso a kuma lokacin daya ga dama wanan tambayan ba a bakinki ya kamata