Sashe 254
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gaskiya zamuce ba laifi don amarya ba zata gwadawa anty barakha komai ba na rayuwa saidaima anty barakha din ta gwada mata don ta fita komai na zamanin nan. Hakan yasa da farko anty barakha daga kai tana ganin cewa ba wani abinda amaryan zata gane aiga mijin nasu don haka ta shiga aika yan dabarrun data iya na kisa don kawai ta sace zuciyar miji a bangarenta. Saidai kash ta manta da haljn da namiji a lokacin dayayi aure idonsa gaba daya makancewa yakeyi wani lokacin ya koma akan amaryan ke uwargida duk gwanintaki ba a ganar maki hakan. Bature yana fadin don,t mind the body mind the engyne matukar gidan aikin na kalau ba a damu da kyau jiki ba. Don kuwa maigida illiya kan amaryansa datayo masa tsaraban kayan hadin matanmu na hausa na gargajiya sune suka haukatashi har yakai yana fitar da sabon rayuwa da ba a sanshi dasu ba a gidan. Mutumin da aka sani yana fita sallah asuba yanzu duk ranan girkin amarya babu mai ganinsa wajen jam,i sai rana ya fito kiri kiri zasu fito yin wanka da ita dashi a cikin bayi daya duk kuwa da yan matan da yake dasu sakwa sakwa baya kunyar hakan. Haka kuma zasu fito zuwa daki don shakiyanci wani lokacin amaryance ke goyashi a baya tana fadin shi babyntane wai a cikin shakiyanci suna wasa da dariya a tsakaninsu. Dare kuwa karfe takwas da rabi sun kargame kofan daki sai kuma safiya idan sun fito ga yaran makwabta kawayen yayansu dake shigowa gidan kallon tv. Amma bawan Allah nan ba kunya haka zasu shige daki su rufe da magariban fari ido na ganin ido ba tare da yaji nautin diyansa ba ko matarshi. Ire iren wanan halin yasa ko yaushe waya yana manne a kunnen anty din tana kai karan mijin a gurin mahaifiyarta ko kanninta. Gashi duk wani kissa da akace tayi tana kokarin yi amma ga banza randama ya dawo dakinta zai tsiri fushin banza da ita da yaranta dan abu kadan ya hausu da fada da cin mutunci. A ranan kuma sai dare bayan sha biyu zai shigo gida ya kwanta da safe kuma inya fita sallah asuba ba zai shigo gida ba sai wajajen tara da rabi na safe ko goma daya shigo ya karya zai fice idan ya fita kuma sai karfe hudun yamma zai dawo gidan. Allah sarki macen bahaushe don mata da yawa suna fuskanta wanan sauyin a wajen mazajensu yayin da akace miji ya kara masu abokiyar zama . Wanan yasa matan mu na hausawa a yanzu saboda halin maza basu kaunar ace miji zaiyi aure sai su dauka abinda ya samu waccan shine zai samesu suma ? Tun tana magana har yanzu ta jinginashi ga Allah ita da yaranta ga wani sabin doka dayasawa yaranshi zuwa kasan layinsu don su dibowa amaryansu ruwan bohol wai bata shan ruwan rijiya tace. Haka zasu fita da safe suje bun layin ruwan bohol din da take so din shiko suna daki kargame da ita sai lokacin da sukaga dama su bude su fito. Zuwanta duban jikin jafar data dan jima acan zaria din ta danyi dabarun ta irin na mata ta dawo dashi amma halin bai canza ba saima wasu sabbin sallon data dawo ta sama a gidan lokacin. Wanan yasa ta rame ta lalace ta fita hayacinta don yanzu ta gaji da kiran gida tana fada masu halinda take ciki saida a yanzu ta daina wahalan kashe kudin da takeyi na gyara girkinta a ranan da yake wajenta haka iya abinda ya bayar kawai take girkawa kowa yaci. Wanan kuma ya kara haddasa fitina a tsakaninta da maugidan ya sako wani bakin kiyayya da yake mata a gaban kowa saidai abokiyar wayarta saratu tace ta daure ta fita batun dan iska kada ta bashi komai nata har yaran ta barsu ai diyanshine. Yanzu kan fitina sosai sukeyi da mijin akan hakan har yakai ana bugaiya tsakaninshi da anty barakha din zai dirke ta a gaban kowa a taru a gidan suna tonon asiri. Tun mama na boyon wanan abin har yakai ga ta fara sakin magana tana jawa surikin nata Allah ya isa a baina. Na samu ya falka dana shigo yana kwance ya zuba min ido har na karaso gaban gadon Allah kadai yasan tunanen da yakeyi a lokacin. Gaidashi na sakeyi da kwana ina fadin da zaka lalaba ka tashi kai wanka sai kaci abinci zaifi ya dubeni yana murmushi kawai yace bayan karyawan da nayi dazun din ? Awa uku da dan kaifa yanzu naso ka yi wanka sai kasha wancan maganin dakazp dashi jiya haka dai na samu yaje yayi wanka ya fito na dauko mai sabon jallabiyansa dake wardrobe wanda bai taba amfani dashi ba ciwo ya kasheshi don a baya yana sayo kayan shan iska ya aje a gida. Wani baki mai addon zaiba maikyaun desine na dauko mashi ya saka muka fito falo na gabatar mashi da abinci . Yadda yake nuna farin cikinshi a fuska yasa nasan yana cikin nishadi a lokacin har ya gama ina gefe ina taimaka mashi a wajen ci bayan mun idarne na mike na kwashe kayan zuwa kitchen nasa biba ta wanke. Falon na dawo na kamashi muka koma saman dogon kujera mai cin mutum ukku muka zauna wayansa ya shiga kara ya dauka hakan ya ban daman mikewa daga wajen na shiga shawagi a cikin falon zuwa kitchen din mu. Duk wayan da yakeyi idonsa yana kaina har ya gama lokacin ina tsaye a kitchen din Biba tana min hiran wasu makwabtansu da sukai fada ina dariya. Jin shirunsa yasa na fito falon na sameshi na zauna a kusa dashi ina fadin naji kana fada yace bari Rahama bansan me mutane suka dauki hakki ba a yanzu Rahama ? Mutane basu tsoron Allah ko kadan kowa dai kokari yake ya gina kansa koda haramun ne a duniyan nan yanzu wai suna fada min kayan dana tura kafin ciwin nan ya kaini kwamce an sace rabi. Ba dole a sace ba kayan da in nakai abina bai wuce inyi wata biyu zuwa ukku sun samu shiga ba amma tunda vani wajen kowa yayi abinda yaga dama dasu. Shi Habu na rasa irin zuciyarsa ya hau ya zauna yana fushi wai don mama da Nusaiba sun jefa masa zargi a dukiyana yau idan habu ko yazid basu tsaya min ba Rahama wa zai tsaya min a garin nan ? Na dauka koda ace ban raye su masu tsayawand suga sun kare min hakkin iyslina da nasu gaba daya amma sai abubuwa akeyi barkatai wanda hanlali bai tunanensa. Na kansa a raina wanan ciwon wani jerabawan rayuwace Allah ya aiko min dashi da zan fahinci yadda lamarin duniya ya koma a yanzu. Don mutane ko da ranka ashe sai kana da amfani ake rayuwan komai dakai sai kana cikakken mutum duniya har dan uwanka zasu dama dakai Rahama ? Sosai nagodewa Allah da dabaran da Allah ya ban nayiwa kaina haka kema haduwata dake Allah kadai na barwa sanin dalilin hakan a tsakanin mu dake. Don ta dalilin aurenki Rahama har Allah ya ban dabaran boye kudina a gidan nan ba tare da nakai banki ba har ke dake zsune gidan ma bakin san da hakan ba don da suna account dina yau Rahama da kudin nan dana aje anan suma an batar dasu kamar yadda wa yan nan suka salwanta min mun koma banda komai. A lokacin kallon mamaki nake mashi yayi murmushi ya gyara zama yana fadin wallahi haka kawai nasa aka kawo min kudin nan nan gida kamar wani abu da niyar idan na dawo daga tafiyan da nayi basai na tsaya shiga bank ba wajen miliyan ,,,,,, Sallaman Yazid daya shigo lokacin ya katseshi duk muka bishi da kallo lokaci guda don yaja ya tsaya daga kofan shigowa falon yana tafa hannayensa. Kafin ya soma fadin wai don Allah yayane nan nake gani haka ko dai wani yaya J din kika sauya munane yau din ? Tsuki Jafar yaja yana kawar da kai ya karaso yana fadin to ina mamanka dake can tana fada a kanka ko ita taga wanan sauyi yau haka sai tayi mamaki zata daina fadan da takeyi dakai tun jiya. Na fada mata dama kai keda jikinka da iyalinka ta barka kayi abinda ranka yake so amma tace ba haka ba tunda bakaji sauki ba don me zaka dawo nan ka tare kuma ? Bayan kasan har yanzu magani kake sha ni itace ma da fitinan ta ta tayar dani tunda safe yau wai na kawo maka maganin nan kasha ya miko mai wani leda dake hannusa fari. Yace ba Rahama ita mama fadan me takeyi a kaina ko na zama yarone yau kuma da za ace sai yadda akayi danine wai magani ko a nan nake ba zan sha maganin bane ? Na rasa meyasa take haka wai akaina wallahi to dai kan ka shirya don wallahi fada ta kwanayi ba don iya ba jiya data biyoka da daren nan iyace ta hanata zuwa sai abin ya ba jafar din dariya haka yasa ya dan sake murmushi a fuskanshi kadan. Don sheri sai ya juyo gareni yana fasin wai don Allah amarya nima ba zaki samo min wata yar filo ba kuwa in kara don dai wanan abin akwai ban mamaki gaskiya ? Ki duba mutumin ki don Allah yau shine a haka yayi clean wallahi yayi kyau kamar bashi ba jiya jiya nan da daren nan fa yazo gidan nan amma dubashi don Allah ? Idan ka gama ka kira min emanual zanyi magana dashi a gabanka yace abinne Allah da ban mamaki kwarai da gaske ya J baka yadda kayi wani fresh ba ? Kaji mena fada ai yake fadawa kanin nasa shima yazid din ya dubi wayanshi yana fadin shi nake kokarin kira ai yanzu hakan . Mutumin ya dauka suka fara gaisawa da yazid yake fada mai mr Jafar yake son magana dashi yana fadan haka ya mikowa yayan nasa wayan ya soma magana na mike ina fadin ya yazid a kawo breakfast ne ? Wallahi madam dina ta cika min ciki kafin in fito amma zan dan taba kadan saboda kwadayi ya fada