← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 275 OF 306

Sashe 275

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Banda niyar zuwa ko wani event a cikin sha,anin bukin donshi ko gyaran jiki ban tsaya nayi ba amma da nayi tunanen kada ai min girshi naje amin kumshi da kitso da gyaran jiki don haka a wahalce na wuni a ranan. Yana can gidan da ake jiransa bayan yayi min kwana biyuna da zaiyi gidan sannan ya koma can gidan don haka an fara sha,anin bukin yana gidan nasu a karshene zai dawo gidana har a daura aure yana gidan. Duk da iya ta dawo gida daga asibiti amma bamu daina saka mata abinci daga nan ana kai mata ba don surfan tsufa tace abincina kawai take iya ci hakan yasa na dage ina girkawa da ita ko yaushe. Kwance nake ina barcin gajiya lokacin da maman tudu ta bugo min waya da basu ganni gidan wajen taro ba na rasa abinda zance mata karshe dai na fito fili na fada mata gaskiya cewa ina gudun fitina yasa na zauna gida. Kada ki hakan yar uwar mijinkice fa ko meye ki shiga koda ba duka ba ki daije a ganki yafi kice kin zauna gida baki tafi ba ba zaiji dadin hakan da kike nufin yi ba gaskiya. Nayi mata godiya barcin da ban koma ba ke nan a lokacin tunda ranan kamune don haka zanje da yamma ayi kamun dani ke nan sunsa a kofan gidansu na cikin gari za a hadu zuwa dan wani wajen event a unguwar. A makare naje wajen don ban fita ba saida na gama har abincin dare don gudun yamma na fito shiya turo da motarshi aka daukemu na samu a cika wajen sosai amma ana ganin zuwan duk wanda yazo taron a yadda tsarin wajen yake. Aminu ne ya jawoni zuwa wajen don haka ya shiga dani sosai inda za a ga fitowana daga motan ya tsaya kafin na saka kafa na fito a hankali. Tankar ba ciki a jikina irin kwaliyan dana caba duk da nauyin cikin da nake ji yana hanani sukuni wanan ban yarda na biyewa hakan ba na lalace don ban bari an barni baya ba gaskiya. Yar uwar Asmauce ta fara tabata tana nuna matani kafin saiba ta farga da abinda suke kallo a wajen. Nida Biba munsha kwaliyan mu muna fita ya juya ya nemi waje yayi packing a can nisa kadan da wajen nan gulma ya dan fara tashi ga matan dake wajen wasu na magana da nice amaryan jafar ai. Wasu kuma suna zance akan cikin jikina yadda na sameshi a cikin jinya yayin da wasu ke fadin yanzu ya fisheni daban a cikin matansa nice ke yadda naga dama a gidan. Kamar Aminu ya sani yana fitowa ya kawo min key din motan ya mika min don yaron akwaishi da gudun zuciya sosai bai yarda ace yayi laifi ta bangaren kawun nasa yana da taka tsantsan sosai wallahi. Sai a wanan wajen muka hadu da mahaifiyarshi ya fada min tazo kwana ukku ke nan a lokacin don haka ta taso daga inda take zaune muka gaisa a cikin mutunci da ita. Wanda nasan ba komai bane yaron nata ya fada mata yadda muke zaune dasu a gidan ya kawo hakan a yanzu. Salimace ta taso ta kamani tana min sheri wai ciki ya boyeni ya hanani shiga mutane koda yake ita ai kyau taga cikin ya kara min na dan harareta ina murmushi. Wajen zama ta sama min daga inda yan gidan suke ban zauna ba saida nabi matan yayyunshi su yaya Auwal na gaidasu na dawo na zauna. Nida biba muna kallon abinda akeyi a wajen hango yar uwata da nayine yasa na kara mikewa zuwa wajenta muka gaisa take fadin yanzu take cewa idan bata ganni ba saita biya ta gidan mu ta dubani. Share zancen nayi na basar ina fadin ina yaran tace suna gidan makwaciyarta ta barsu duk a cikin filanci muke maganan da ita lokacin. Na hango Saiba a cikin wani dogon riga tana kai kawo a wajen taron kafin can na hango tana magana da Aminu sai naga ya nuna matani tana magana kamar da tsawa dashi. Wai ashe cewa tayi ya bata key din mota zasuje wani waje su dauko abu yace makullin yana hannuna kuma uncle yace kada abawa kowa motanshi bayan ni. Shine take fada kamar ya yace kada a bawa kowa motarshi ita din tafimune data shiga sai gashi yazo yace in bashi key inji saiba yake mayar min dame tace nace ta kira mai motan ta fada mashi sannan na bata key din. A shirye nake dasu nasan hakan plan ne yasa ban bata key din kai tsaye ba da ace akwai girma da arziki a tsakanin mu sai in bata key din ai kayan mijintane itama . Amma dana fahincesu saina hana key din yaron ya juya ya koma yana fada mata abinda nace game da amsan key din a wajena. Fisge fisge ta soma tana nunani ana riketa daga wajen muna tsaye maria na fadin kai Rahama ki mike mata mana kafin ta tara maki mutane a nan. Ba zan bata ba don ba ita ta ban ba wasa wasa sai gashi an taru a kanta tana ta zage zage wayana dake vibration na dauko a jakkata shine akan layi na dauka a fusace sai naji yana fadin. Kina inane ke nace wajen buki mana yace ance saiba na fada dake a wajen don kin hanata key din mota ? Au dani take nidai naga tana fisge fisge na zata iska ta hau ai look kada ki yarda kibawa kowa key din nan idan abin baiyi ku dawo gida kawai don Allah ? Na zata kin biye mata don ba hankaline da itaba bata duba condition dinki saboda hauka na cika masu motan da suke amfani dashi tun shekaran jiya yau kuma na basu kudi su kara mai a cikin motar. Don tana mara mutunci hakan bai mata ba saita karbi key a hannunki don kishin tsiya zata gamu dani wallahi dif na kashe wayan ina fadin banjin ka yaya. Munafuncin maza kawai ai baka fada min kayi masu hakan ba sai yanzu nuna min yayi naje da motarshi kada in hau motar haya zuwa wajen kawai kuma mu kula mai da mota kada in yarda inbayar mashi da motanshi ga kowa. Sai kawai mukaga fada ya koma da salima ga saiba can da nata nan kuma ana fada da salima abin ya bamu mamaki matan yayyunsu suka shiga fadan salima din ana ta cacam baki a wajen. Bamu san meke gudana ba acan din don muna da dan nusa dasu matar yazid da aka fara fitinan tazo ta samemu muna tare harda ita. Saida wata kanwarsu yaya matar aurece ita tazo tana fadin bafulata kin yamutsa wajefa da fitina ga amarya can na fada dake wai zuwanki taron nan bai mata rana ba ya bata mata buki. Kishiyarki na fada a dake a barta tazo ta dukeki ana riketa can, nan kuma suna zaginki da mijinku ashe salima tana wajen ta basu amsa shine shine abinya zama fitina ya barke a tsakaninsu har ana batun bawa hammta iska a tsakaninsu. Muryan maria naji a hasale tana fadin Au haka tace ashe, bamu ko sani ba ai ba zata kara ganin mu ba ai kuwa, koda Rahama tazo wajen nan ba wanda yaji bakinta da wata, Ta daiyi da wace ta tayar mata da fitina don itace ta bata mata bukinta ba Rahama ba watau Rahama itace marainiyar tako ? Mariyace ke fadin haka a hasale taci gaba da fadin tun zuwana naga saratu na harare harare a wajen nan, sai sun san dai wanda ya bata masu sha,anin bukinsu don ba Rahama ba dai kam. Dani da mariya din da matar yazid muka bar wajen bukin a ranan ne kuma rana ta farko dana fara jan mota a garin zaria don ko biba ban tsaya nema ba tunda tana tare da yan gidansu Aminu kuma ya bace a wajen taron. Saida na saukesu gida na nufo nawa gidan kai tsaye yayi kiran wayana ban daga ba saboda hayaniya banko ji kiran ba a lokacin yasa ya nemi Aminu . Aminu din ya kirashi yana sheda mashi na bar wajen bukin da dadewa kodaya dawo gida ni ya sameni gidan abinda ya fara tambaya shine waya jawoki zuwa gida ? Nina jawo kaina mana na bashi amsa ya tsaya yana min kallon mamaki baiyi magana ba ya nufi dakinshi kai tsaye don a gidan yake sai daya gama ya fito ya fita zuwa massalaci sallah magariba da isha,i. Ya dawo ina dakina jin shigowanshi gidan yasa na fito daga dakin ina gaidashi abinci na dauko na kawo mashi falo inda yake zaune yana waya. Ya harde kafafuwansa a waje daya a mike yana dan jujuyasu yake wayan yana fadin shi gaskiya yasan dama za ai haka ai wallahi ya fada mata tabar mashi gidansa tunda bataji meyace da ita kafin ta dawo ba. Ai ya fada mata datayi kuskuren akan yarinyat nan tace zatayi mata rashin mutunci ba zai kyaleta ba saurare naji ya tsayayi kafin yace shin mama ana aure dolene ? Ni dai na kawo yarinyar nan gidan nan yanzu kuma nace ta tafi gidansu tunda basu da mutunci itafa ta rokeni motan nan banyi mussu ba nax bata key harda kudin mai da zasuyi jigila dashi. Don naba Rahama tawa motan Aminu ya kaisu abinda zatajeyi shine kuma zai zama jidali a wajenta yanzu a bainan jama,a har ana kamata tana barin a bari taje ta duketa. Watau bata damu da halin da zara iya shiga ba ko ba ruwanta da cikin jikinta ke nan ita idan an barta da Rahaman badon ciki ba me zata diba a wajenta ? Saurare ya somayi na dan lokaci kafin naji yana fadin dole inyi fada mama cikine jikin yarinyar nan fa mama idan tayi mata illa fa hajan bai shafeni ba ke nan ? Sai in tsaya tayiwa yarinyar mutane illa tunda ta kudurta hakan a ranta Rahama bata taba damuwa dame nake masu ba ita dion banyi mata ba itayi fushi Kuma ta sani tasan ina masu ai ko ita ba mutum bace koba aurenta nakeyi bane itama akwai wanda yakai nusaiba wahal dani a cikinsune mama
Chapter 275 · 0% Book details