Sashe 145
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiya daukoni daga school ranan muna hanyane aka kirashi a waya wai mama tana nemanshi saratu ce ta bugo wayan lokacin ya amsa da Ok ta dawo ke nan ? Tace ehh sai naji yace da ita gani nan zuwa zan sauke Rahama injuyo sai banji dadin hakan daya fada ba a lokacin saboda nasan halinta yanzune zata iya juya zancen ya zama babba. A samu na yamadidi dani a gari ana fadin magana ba dadi a kaina wanda bai dace kamar yadda akewa mutum fatan sheri a yanzu don har jira mutane suke wani sheri ya sameka a fara yawo da sunan ka har garin ku. Muko fulani kowa yasan mu kunya garemu badai tsoro ba dan bamu jin nauyi ko girman abu idan mun tashi yinsa kai Aaye muke abin mu ba boyo . Saida ya kaini din ya sauke ya shiga yaci abinci sanan ya tafi kiran da mama din ke mashi inda ya samu mama ta hau akansa don abinda saratu ta fadi har yaso zama fada a tsakaninsu da salima a lokacin. Saboda lokacin da yace gashi hanya ya daukoni zai kaini gida bayan ta kashe wayan tace ke mama kinji. Wai matarsa ya dauko sai ya kaita gida tukun zai zo wai Rahamace yaya yake kira da matarsa Rahama dai Rahama dai wanan ai abu a fili yake kowa yasan hakan aikin asirine gaskiya. Inba asiri ba me yaya zaiyi da Rahama don Allah wanan bagidajiyar yar kauyen yana da mata kamar Saiba. Aikin banza aiba wayewa akajawa ba hali na gari jarin mutum a hakan yar kauyen yake son abinsa don tafi bashi kwanciyar hankali. Balle ko makiyin Allah a yanzu baicewa Rahama yar kauye don koke tafiki wayewa sanin da dai kikai mamata yasa kika kirata da yar kauye. Tafini fa kikace Salima tace kwarai kuwa abu a zahiri ko kina gardaman hakanne koda yake ba mamaki don kin dade baki ganta bane yasa kike fadan hakan akanta. Ta dai fiki ko keda kika mayar da kanki banza wajenta saratun ta fada sai salima tace kona mayar da kaina banza ba kaina bane farau ai don kafin nayi da Rahama wasu sunyi da Saiba ai duk ko da cin mutuncinta da komai haka naga ana binta sau da kafa gidan nan. Balle Rahama dake ban girmana da mutuntani tasan darajana dana dan uwana da kowa nawa kinga ko kowa na son kyautatawa a rayuwa. Kukan dabi,anku baida kyau wallahi ku zauna kuna cin junan ku kamar kishiyoyi kowa kamar yana jiran dan uwansa ya fincika ? Bama shiba dai su daiyi kokari su kama nasu dakin shi yafi garesu ba shiga tsakanin matan dan uwansu suna saka ido ba iya ta fada. Fada masu dai iya wanan abin takaicin dame yayi kama yara basu san ciwon kansu ba kullun jidali da juna kamar kishiyoyi ? Wanan yasa ran mama ya kara harzuka da zancen dan nata don koda yazo yana mata sannu da zuwa a fusace ta amsa mashi zaice a yanzu hakane tsakaninsu da ita. Mama ance kina nemana ya fada cikin maida hankalinsa a kanta tare da natsuwa yana saurarenta cikin ladabi. A,a ka bari idan ka gama abinda ke gaban ka jafar sai kazo kaji me nake nemanka dashi yanzu ai kana uzuri tunda hankalin ka yana wajen yarinyar nan ayanzu. Kallon bangane ba yaiwa uwar tace ehh ance kace saika sauke Rahama zaka zo kiran da nake magaka shine nace kaje idan baka gama uzurinta ba kagama ka dawo. Mama da Rahama zanzo gidan nan koda aka kirani na daukota daga school zan kaita gidane don da motanta nayi amfani yau na bayar da datawa a wanke min. Allah sarki ita Rahama ashe harda mota ka saya mata su sauran ina tasu take take ? Baga mota a gidan nan na ajiye ba mama haka itama na aje mota ibrahim yana kaita makaranta dashi da sauran laluran gidan. Kadaiji tsoron Allah jafaru kasani dukkansu amana suke agareka baka nuna kana banbanci a tsakaninsu ba haka a fili. Kayi tafiya daga gidanta ka dawo ka kuma sauka gidan ta kayi adalci ke nan jafaru kana son kona kankane da hakan Jafar ? Mama kodana sauka gidanta jiya ai da hujjana na sauka a wajenta don kodana tafi kwanakinta bakwai da Allah yace ayiwa budurwa bai kare ba na tafi wanan yasa na sauka na karasa mata kwana dayan daya rage a can din. Kadai ka sani tunda abin ya zamo bin bashi har kana rankon kwana a tsakaninsu dolene akace kayi mata kwana bakwai dinta tunda uzuri ya kamaka na tafiya ? Wanan shine adalcin Jafar kake ganin su nan zasu fahinci hakan da kayi jahilcine ko tauye hakkinsu akan wata tunda daga gidanta kayi tafiyan? To ita kuma saiba dakace meta dawo yi a gidanka nice nan naje na dawo da ita don banga abinda tayi maka na wanan hukunci ba har da saki ? To shike nan ai mama ta zauna ga gidan nan amma ni abinda ya dace nayi akanta naga yayi don ba zan zauna da mace haka ba tana gurbata min gida. Au ita saiba ce kadai take gurbata maka gida su sauran basu wani mugun hali da baka dauki mataki a kansu ba jafar ? Ikon Allah ke nan kada ya dauki mataki akan iyalinshi dubu wanan wani irin rayuwane wai don Allah gaba daya kina neman hanawa yaron nan walwala a rayuwansa. Shin yar nan daya aurace baki so dashi ko shine yayi maki laifin da har kika tsaneshi hakan dubu don abin yayi yawa gaskiya shima fa yana da hakkin a kanki idan kin tauyeshi da yawa dubu ? Yanzu iya ni zakiwa sheri kina zargin ina zuga mama nice zan zuga mama kuma ? Iyan tace ke ungo nan yar banzan yarinya mara mutunci duk abinda kukeyi ina kallon ku keda uwarki . Ki dubeni da kyau banyi tsufan da ban fahintar komai a yanzu ba nan gabana yanzu kika gama zuga uwarki akan yaron nan har abin yaso zama fada tsakaninki da yar uwarki don haka ki shiga taitayinki dani na fada maki niba dubu bace dake daukan maganan ki. Shiru tayi don tunda taga iya dinbta juye tasan yanzu idan ta matsa ranta zai iya baci don haka tayi shiru, ya mike yana fadin yi hakkuri iya ki barta ai tayi Allah na ganinta. To wanan kalamin da yayine yasa saratu din kuka wai iya taja dan uwanta yana yi mata Allah ya isa kan abinda bata aikata ba. Bayan fitanshima iyan bata kyalesu taci gaba da fada tana fadin ta yaya zaki zauna kina bin maganan yara dubu ? Ko yaushe yarinyar nan ta zugaki kika aikata abinda ba daidai ba aka yaron nan idan aka taliyo sai a iske kune baku da gaskiya. Yaron nan yasan abinda yake yi dubu idan bai isa ba baya tara mata ukku a karkashinsa don haka daga yau ina son ku cire masa ido akan iyalinsa don Allah ? Ku barshi ya zauna lafiya da matansa ku barshi ya tsara irin rayuwan da yake so dasu a gidansa don Allah . Ke kuma duk abinda zakice kice saukin abin dai gidan wani zakije kema don ba a nan zaki tabbata gidin uwarki ba saratu dole dai wata rana kiyi aure ki barta. Kina wanan halin na hade haden fada saratu wa zai yarda da hakan a gidansa in wanan dan uwankine yayi hakkuri ya zauna dake da halinsa can inda zaki fada ba lalai bane suyi hakkuri da hakan. Yarinya tana abu mara kyau kina mara mata baya wanan hali idan tacigaba ba zai haifar mata da mai ido ba nan gaba. Ranan dai bai samu dawowa gidana ba sai kirana yayi yana fadin mu rufe gida ba zai samu dawowa gidan mu ba a ranan. Kishi kumallon mata a take naji wani abu a raina lokaci daya kishi ya rufe min zuciya naji wani irin ba dadi a kasan zuciyata. Zancen anty Salmane ya fado min da take cewa Rahama ki cire ido akan duk abinda mijinki zaiyi akan matarsa matukar kina son ki zauna lafiya ki tsira da aurenki. To sai kin dinga kawar da kanki ga rayuwansa dana matansa kada ki zamo mai bin kwakwafin abinda yake tsakaninsu har ki dinga tada jijiyan wuya akai don Allah. Mace mai wanan halin itake sayawa kanta bakin ciki da kudin ta itake sawa hankalin mijin da kishiya dana zagaye dasu su farga da halinki mara kyau a kan kishi. Duk abinda zakiyi Ramah kada kiyi wanda zaki yarda ki kona kanki ki kona mijin ku don Allah tare da matansa kika sameshi bawai bai sonsu bane ya auroki ? Suma so da kaunace ya hadashi dasu don haka kada ki yarda kuje lahira ana shari,a dake kan namiji don Allah ? Kiyi kokari ki yaki zuciyar ki akan zaman kishi donshi dashi aka halicce mata kishi tun muna kanana muke da abin mu a cikin jinin ko wace mace yake don kishi kamar hassada yake a zuciyar mace sai ka tsira daga sherinsa kake samun haske a rayuwan zaman auren ka. Tayi min irin huduban nan sosai taka min kwantace da kanta tace kingani nan idan D baya gidana kwata kwata nakan cire zancensa a rainane amma da zaran ya dawo gareni kuma ya zama miji sai ranan daya bar gidan nan . Take naji abinda nake ji a lokacin yana ragewa a zuciya inda na fara karanta wallahu Ghalibun har karshe ina jin wani sanyi a zuciyana. Karshe falo na fito nasawa Biba kira ta fito muka zauna nan muna dan hira da ita don mu rage dare karfe tara nace zan kwanta tace to bari ta je daki nace a,a ba zan barki ba ki dawo dakina mu kwana tare tunda ba kowa a gidan. A Gaskiya ina jin dadin zama da yarinyar sosai a rayuwata don gwargado tana da gudun zuciya sosai tun da safe da zaran ta sallame sallah asuba zata fito tayi shara da ta gyaro ko ina har kitchen idan na kammala abinci takaiwa su salima dake daki kwance ta dauko namu zuwa falo muyi wanka muyi shirin fita don tare muke barin gida da ita. Shiyasa nake son shakuwa na tsakani da