← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 305 OF 306

Sashe 305

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tun kafin bukin ta koma gida don tafiyansu daya gabato munji kewanta sosai a lokacin. Ina kitchen girkin rana nakeyi dan aiki nawa yakaini rana naji wayata tana ta ringing bibace ta dauko wayan ta kawo min na fito ina amsawa don ganin wace ke kirana din a lokacin. Yandace na daga da sallama ina gasheta ta amsa a gurguje take fada min wai nasan me su yan uwan mu suna cikin garin nan kwana biyu ke nan suna neman gidan basu gane ba ? Suna ina nace mata cikin zakuwa tace gasu suna cin abinci nace dasu in sunga nikan zan basu kudin mota su koma ko suje wajen mama aji yadda za ayi amma ban yarda yaya habu yazo ya samesu a nan ko mama taji ta soma fadan nan nata. A cikin wani murya mai kama da tsawa nace da ita kada ki soma turo min su nan gidana koda yake bari Aminu yazo ya dauki min su. A,a Rahama kinsan halin mutanen gidan nan yanzu da angansu kuma sai ace munji dadin waje muna kwaso yan uwan mu yaya muka kare dasu balle kuma mun dauko wasu ? Maria su kore mu udan sunce basu zama da yan uwan mu saidai mijinki ba amma ni na jima da aje magana a kansu da yaya Jafar. Allah ya yanke muna wahala ya turo muna su nan likacin daya kamata su din a,a Rahama ki bari na basu kudi su koma gida din Allah ? Gida wajen wa suje suyi ta aikin bauta mu muna nan cikin daula suna can suna bautawa kawu ga Aminu nan zuwa yazo min dasu na fada ina katse wayan. Sam banji dadin wanan zance nata ba ba a dauki lokaci ba Aminu ya dawo min dasu zabar tausayi saida nasha kuka dana gansu lokacin. Aminune ya duko gefena yana fadin anty bari na kaisu dakina suyi wanka in basu kaya su muje suyi aski sai mu dawo ina jan majina a hancina saboda kukan da nayi nace dashi bari na dauki maku kudi kaje dasu ka sayo masu kaya yace to anty don dai kince da kayane dan aski kawai ai ban rasa kudin da zasuyi aski a wajena. A,a tsaya in dauko kudi ku dan sayo kaya su samu na canzawa nashiga na dauko kudin na mika mai suka fita kuka nacigaba dayi ina waya da mama da hankalinta ya tashi. Take fada min mijinta bai yadda da yaya mazan ba ya daifi yadda damu matan ita bata san abinda yasa baison ayi zancen su ba ? Ni da kaina na kira yaya ina kuka na labarta mashi zuwansu din da yadda abin ya faru cikin karaji naji tace yanzu suna ina ? Aminu ya kaisu suyi aski ya dan sayo masu kayan sauyawa yace barin nemi Aminu din ajiyan zuciya na sauke dama nasan yaya ba zai taba kinsu ba. Don sauda yawa yana min hiransu lokaci lokaci yakance dani yakamata a dubu su ko ya kira hardo ya tura masu sako duk da nasan hardo zai basu amma baffa amshewa zaiyi. Tare suka dawo gidan dashi sayayya sosai yayi masu suka shigo yanawa musa sheri da ke ashe kanin naki aure yayiwa gudu yazo nan saida yaga za ayi mashi auren dolene ya tuna damu. Harshe na juya ina tambayanshi yake fada min yadda akayi raina ya baci sosai da kawu abinci na mike na kawo masu sukaci suka dasa wani hiran dashi. Dakunan daba kowa a ciki na boys quarters yasa Aminu ya bude ya saukesu a ciki da yake ba nan gidan mu yake ba saida zai tafine yakecewa dani ina ganin fa nan za a kawo yaran nan idan uwarsu zata saudiya. Su basma yace eeh don ban yarda da cewa da tayi wai akaisu gidansu ba Allah ya kaimu nace ban yarda na nuna komai ba ga hakan. Amma nasan akwai ta don yadda yaran suke basu jin magana kuma ba a tsawata masu amma ba komai zanyi iya kokarina dasu insha Allahu. Aikuwa hakan ya tabbata don kuwa tun ana saura kwana ukku su bar kasan sai gashi da yaran yazo min ban ko san da zuwansu ba ya kwasosu zuwa gidana ba yadda zanyi dole na rugumesu . Irin wasan da sukeyi ya fara daga min hankali wasane na alaman ba kwabo din nan ga yaro nan muka fara kwasa dasu nayi masu serious warning akan hakan. Ban yarda na sake masu ba sam da safe kuma zan tayar dasu suyi sallah akan lokaci idan angama kuma nasa suyi brush biba tayi masu wankan safe. Gaida mutane akan Aminu na fara koya masu hakan ya shigo suka bishi da kallo na daka masu tsawa su gaidashi daga zaune inda suke sukace ina kwana nace ba zaku tashi ku gaidashi ba bakuga yadda biba ta gaisheshi bane hakan yasa suka mike daya bayan daya suna gaida shi. Nace duk wanda yazo baku tashi kun duka kun gaidashi ba saina tsunkewa mutum kunnensa da yuka . Haka sunso su dinga irin barnan nan da sukeyi su halaka abu ana kallonsu ba kwabo su barnatashi ana kallo haka zasu barna abu. Shima cikin nasiha da fada na hana wanan da mamansu tazo gidana muyi ban kwana wai daga gidansu take shi yaya ya kawota yadda suka gaida ita ya bata mamaki. Har take fadin wai basmace nan kuwa a,a yan matan anty kece nan harda su makeup a fuska koba kwali kika shafa a indonki ba. Ina jin mijin tace mata waye anty ita ba zasu iya kiranta da mummy ba ko mama karna kara jin wani anty can daga yau nace dashi ai haka suke kirana tunda sunji biba na fadan hakan. Tana dan murmushin yake a fuskanta yace ki duba don Allah dan kwana biyun da yaran nan sukayi a nan yadda suka koma keda suka gaidake da zuwa bakiji dadin hakan ba yanzu ? Toni yaya me zance kai kome nayi ai banyi daidai bane a wajen ka kasan halinsu baji sukeyi ba nan ma dai don suna shakatane ai to kada ki koya masu din ni ai nasan matakin da zan dauka don ba zan yarda ba gaskiya. Basu jima ba yace su tashi suje nasan don ganin da yayi yaran sun narke a jikintane saida ya mike yake cewa dani ki shiryasu idan na dawo zamuje can gida ku sallami su mama. Hakan ya faru don kafin ya dawo munyi wanka mun shirya tsaba duk da kayan yaran ga kaya na kwarai sabbi amma duk sun nakashe daga wanda ya yage a tsakiya sai wanda zip dinsa ya lalace hakana dai muka samu aka saka aka fita ina yaba sakaci irin na wanan matar a raina wai kuma harta iya hado wanan kayan haka azo dashi. Munje gidan ba laifi don mama har daukan Amir tayi tanawa mashi wasa da wakan yabo na mai sunan, baban nasu yana murmushi ta dubi yaran tace indai ba idona ke gizau ba sai ince yaran nan sun sauya a dan kwana biyun nan da sukayi. Tunba Siyama ba ni dai har kiba naga tayi ai dole yanzu ta rage wanan alaulayin nata Saratu dake neman shiri da dan uwan nata ke fadin hakan . Yawan cuwon nan da kwanciya naga duk ta dainashi yanzu uban ya fada mama tace dashi aiko yunwa ya isheta yaushe suke tsayawa su kula yara? Jiyama nake ji ance anga uwar wai a nan garin na dauka ai duban tar tazo ko tazo ina zata ganta nayiwa maigadi kashedi idan ya bari tazo min gida bakin aikinshi ranan. Ni dai banyi magana ba ina zaune ina jinsu aka gama yace mu tashi muje da zan fito na mikawa mama dubu biyar iyama dubu biyar muka fito. Naso na rakasu har kaduna amma yaya Auwal yace kowa ya zauna gida sun gode sai mazan su suka rakasu zuwa kaduna a ranan kuma akace sun tashi da dare don saida suka daga suka dawo gida. Gaskiya munji kewa sosai gidansu mama Saratu aka bari da matar Yazid duk ita da ita da babu dukka dayane tunda bata fitowa kullum suna ciki rufe. Sai su Aminune isah yaya yace zasu dinga kwana gidanshi shi kuma musa a gidan su mama haka ya rabasu ni dai najawa yaran kunne sosai a lokacin. Nayi ta jira inji wani korafi daga mama game da yan uwana din sai baniji ba yasa na saki zancen a raina suma basu da rugima sai hakan yayi min dadi. Sana,anmu da Nafisa a yanzu ya bunkasa sosai don ba zannuwan gado kawai muke daukowa ba har da kayan kitchen masu kyau sabbin yayi muke daukowa hakan yasa muka fara shawaran bude shago a asirce ba tare da kowa yasani ba. Ni da wata kawata da muke unguwa daya zata bude shagon kayan mata ni kuma nace na kayan kitchen din da sauran abubuwan mata. Na nemi shawaran yaya na fada mai ya yarda da yace zaiyi magana abokinsa ya nema muna shago a bakin tiri inda za afi samun kasuwa. Ni dai nasan baiyi niyar zuwa saudiya ba sai gashi kwatsam yazo min da zancen zaibi jirgin yawo ya cin masu don hankalinshi bai kwanta ba tunda suka tafi. Duka duka cikin kwana ukku ya daga yabi bayansu duk wanda aka fadawa ya tafi makka sai yayi namaki tunda yace sai wani shekara zai tafi. Ashe gara da Allah ya kaishi don kuwa mama tun zuwansu ta fadi ciwo yau ciwo gobe lafiya har suka bar madina zuwa makka ana fama da ita hankalinsu yaya duk ya tashi sai ganinsa sukayi kwatsam yace hankalinshine bai kwanta ba. Zuwan shi ne dan dama dama don dole aka samu keke yana garata ta samu tayi aiki a lokacin ganin ta dan samu sauki ya koma da ita madina sukai ziyara ya rigasu dawowa Nageria tunda shi jirgin yawone. Saida ya dawo muke jin cewa ga abinda ya faru a can din da mama ai taji jiki sosai badon zuwanshi ba zata samu aiki ba sosai amma bai dawo ba saida ta tabbatar da tayi ibadan daya dace tayi. Yaji dadin yadda ya samemu da yaran don gaskiya ba yabo ba yaran sunyi kyau sosai duk da ba komai nake masu ba
Chapter 305 · 0% Book details