Sashe 101
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kayan zuwa kitchen dinta. A part din iya kuma washegari da aka shigo da tasu tsaraban take fadin kasan fulani kukaje ke nan daga zuwa tafiyan wuni sai kuma kwana haka matar dauda ta ishemu da waya bataga mijinta ba. Kamar wani yaro kuma yaran matanku basu damu kamar yadda ita ta damu ba ni Hansatu na rasa wani irin so takewa dauda haka har tsufa. Jafar ne ya shigo cikin wani dinkin shadda mai maiko ga laushi da santsi kallan ruwan konanen kuka sai kamshi dake tashi a jikinsa ya kafa hular data dace da kayan da bakin takalma half cover ta maza Ikon Allah wanan shigafa haka Jafaru sai kace wani ango dakai can kana zuba kamshi ya washe baki kafin ya kai zaune yana fadin ai ango nake Iya tsohuwa. Kema dai shigar tawa ta burgeki kenan iya ina amaryan tawa zataga shigan nan ta yaba haka kafin ke iya ki gani ki yaba din. Kunji ja,iri ni ba amarya bace ke nan kakarai ka fada wanan matar taka Nusaiba taji tayi muna dariya ko ita dai na rigata ganin wanan shigar tunda ita bata yaba ba. Ba zata jimu ba iya koda taji din ma ba zata samu hakoran dariya gareki ba a yau iya don nata ya sameta tunda kin kirani da ango ya fada don ganin irin kallon da iyar tayi mai. Itama iyan murmushi tayi tana fadin jafaru na dai gane kamar kana son kara aurene a yanzu don abinda yaran nan sukai maka ? Da dai kayi hakkuri dasu hakana don koka kara auren wa yan nan masu ido a tsakan kai ba fasa halinsu zasuyi ba yaran da suka bushe fitilansu suka iya dawowa nan idonawansu a bushe haka ? Kayi hakkuri ka shirya da matanka ku zauna lafiya tunda ita wanan mai idanu kwashi kwashin ido a kafe mata na rashin kunya kowa ka auro a gidan nan ba zata taba barin ku zauna lafiya ba. Iya komai kayi a duniyan nan saika samu wanda ya fika iyasa ai nata kuka gani bata san wace zan auro mata ba a yanzu ki saurara zaki sha kallo ne a gidan nan ai kwanan nan. Allah ya zaba maka mafi alheri a rayuwanka jafaru yace amin iya yama zaba har ya ban ki dai tayani da addua kawai iya shi nafi bukata a wajen ku yanzu. Jafaru uwarku ba zata yarda ka kara aure a yanzu ba yadda naga ta daukaka zancen yarinyar nan tun dawowanta gidan nan ni har tsoro abin yake ban. Wai mama ya tambaya yana mikewa yace mama kan ki tayani bata hakkuri don aikin gama ya gama a yanzu saidai adfu,a a tsakanin mu kuma. Ka daiyi niya baka jin kwabo nake gani Allah ya zaba muna abinda yafi zama alheri a rayuwan mu amma daka shirya da matan naka har dai wanan mai tsohon cikin. Aida cikin ta biyewa sherin yar uwarta a kaina iya ni sam ban ni tausaya mata don itama bata tausaya min ba lokacin da nafi bukatansu a kusa dani ai. Yasa kai ya fita iyan ta bishi da kallo ita kadai a falin take magana tana fadin tsiyan kakai namiji a bango ke nan ai shimai hakkuri bai iya bultsewa ba dama yaron nan yayi hakkuri a rayuwansa kusan dai ace a tauye yake. Salima dake jinsu taki fitowa su gaisa don gudunsa da takeyi kan kada su hadu don zancen saurayinta data turo mashi washegari daya dawo garin . Kuma ya tabbatar mata da cewa yaga J din sunyi magana amma kuma baice mata komai ba har yanzu game da zancen. Au damake idon ki biyu kina jin shigowan yayanki kikaki fitowa take cewa salima din saida ta zauna take fadin ina jin ku iya tsoronsa nake ji kada yayi min fada akan Yusuf. Haukar banza shi zai zauna maki dashi da zai maki fada tunda kin dage saishi shi meye nasa naki kece zaki zauna da abinki ai ba wani ba ? Iya nifa zancen yaya kamar aure yake bida har zance yayi nisa don irin amsan da naji yana baki a yanzu har cewa yayi ai Allah ya zaba mashi ko saidai addua. Yo saidai adduan mana tunda nasan uwarku wanan karon ba zata yarda ba ko wanan sakaran daya aure daga baya ai saida aka inmata. To ita mama meye nata a ciki tunda shi zai zauna da abinsa kya fada kema yar nan nidai banga abin sakawa yaro ido ba yana cikin lokacinshi. Kuma ko banza tara mata ai gada yayi tunda ubanku ras mata hudu ya jera a gidansa ya zauna dasu ashe ko aure gadonsa yayi. Habu ya dauka suka fita don suje wajen mama suna daukan hanya daga gefe inda yake zaune yake fadin muje samaru sai habun ya dan kalloshi. Amma baiyi magana ba ya dauki hanyar Samaru din kamar yadda dan uwan nasa ya fada da kwanta ya kawosu kofan wani gida mai dogon gina horn sukayi aka bude gidan daga ciki habu yasa kai da mota ya shiga. Bin gidan yake da kallo kafin ya dubi dan uwansa yana fadin wanan gidan fa J gidan waye haka baiyiwa habun magana don maigadi daya iso yana gaidasu lokacin. Hakan yasa ya bude motan tare da amsawa maigadin yace baba mun sameku lafiya habu din shima ya fito yana kara bin gidan da kallo . Ya juyo ya kurawa dan uwan nasa ido daga inda yake tsaye saida ya gama maganan da zaiyi da maigadi yace to yaya kaga Surprise din ? Kallon ban gane ba habu yayi masa yace ehh nina gina abina da kaina Habu da gurin in mama ta yarda na baro can na dawo nan. Yau shekara kusan biyar kenan ina wanan ginan ba tare da kowa yasan da hakan ba sai yau nake fada maka don na fahinci mama ba zata bari na baro can ba a yanzu. Wancan dayan ginan kuma na gaban wanan din kai da yazid na dorawa saidai rashin lafiyana yasa komai ya tsaya min a lokacin . A yanzu sam ba zan iya dauko saiba ko Asmau na kawosu gidan nan ba don na fahinci basu taba canza halinsu na kazanta din nan. Sai gashi faduwa yazo daidai da zama yanzu Rahama zan aje a nan ta zauna su kuma su zauna can din har abinda hali zaiyi muje mana ka ga cikin gidan sosai habu. Sai lokacin habu ya nisa yana fadin ninaso na riga wanan Surprise din ashe ka rigani saidai ni tawa gaskiya ko rabin wanan baiyi ba J. Tau ashe kaima kana da wanan dabaran ya ciro dan makuli daga aljihunshi yana bude falon suka shiga ido waje Habu ke bin ko ina da kallon mamaki a gidan. Don bai taba tunanen dan uwan nasa yana da irin arzikin da zai gina wanan mamaken gida haka ba a ransa muryan Jafar din ne ke kara fadin. Idan Allah ya nufa ina kuma rokonsa da yaban rayuwa na kammala gidajen nan Habu don na dankawa kowa dukiyansa a hannunsa in huta. Kaga wanan da kace ka fara ginawa sai na saye shi da sunan mama ta fito wancan gidan ta dawo nan gaba daya ta zauna. Wanan wacan kuma din sai mu barwa Saare da anty baraka da Salima a matsayin nasu rabon da suka samu ka tayani addua habu in sauke wanan nauyin dake kaina ba tare da an samu matsala ba . In sha Allahu habu ya fada a sanyaye kafin shima yakai zaune cikin sanyin jiki yake fadin kayi hikima da dabara sosai J . Could you believe not morethan one year saida kawu yayi min zancen kudin mu dake hanku inda na nuna mashi banda matsala da hakan ai. Yace ni yarone ya kamata yanzu nima na fara tawa plan din don haka zaiyi magana da mama a raba kudin nan abawa kowa nasa ya rike. Kawu kawu na dade a raina ina zargin mutumin nan ba tsakani da Allah yake muna wasu abubuwan ba dama ? Habu yace nina dade da fahintar hakan tun rasuwan baba ai na fahinci waye kawu don ba karamin abu yayi a lokacin ba da sunan karfin mu bai kawo ba. Quet sure yayi wanan maganan iyace nasan ta taushesu da zancen amma ina da tabbacin ya zauna da mama akan hakan lokacin. Ohh my god meyasa mutane suke kasancewa hakane a yanzu habu duk wanda ka yarda dashi sai ya ha,ince ka ni kawu zai zarga akan na taushe kudin magada a karkashina. Bayan yafi kowa sanin cewa ban wasa da wanan abin koshi wani lokaci daya bukaci da in bashi aron wasu abu daga ciki na fada mai cewa koni ban taba taba kwandala da dukiyan nan ba Habu. Nawa business dina na gashin kaina nakeyi habu shine kuma na dora ka kaima akai ka samu rabonka ban amfani da wa yan kudin don in kara kaina Habu a harkan business na shigo da kayan masarufi din dai na barsu a juya . Sun dan jima suna magana kan kawu nasu kafin su bar gidan bayan sun leka ko ina na gidan habu sai yaba kyawon gidan yakeyi yana ajiyan zuciya. Suka dauki hanya zuwa babban gidan nasu a can ma basu samu shiga maza ba don rikicin da suka samu anayi tsakanin dan umma da dan wanjen gwaggo kan gina sock away na masai daya dan shiga gefen umma din. Ita da diyanta suke fadin basu yarda ba tunda gidan dama rababene ai don me zasu shiga wajensu suyi gina. Sun dai tsaya an sulhuta inda shi Jafar ya roka da cewa suyi shawara sai a sayi wajen a gina ma gwaggo din tunda bayi za a yi mata zama ba bayi kuma baiyi a gareta. Daga gefe Habu ke fadin wai tsaya Isah yaushe aka raba gidan nan bamu da labari sai wanda aka kira da isah din yace ba dole sai kayi labari ba ai tunda ita mama dubu tasan kowa akan bangaresa yake ai gidan nan tun baba na da rai kuwa. To ban yarda ba yasa kai ya shiga yabarsu ana wani hayaniyan a wajen kuma iya gaskiyarsa ke nan akan bai yarda ba din a lokacin.