Sashe 158
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nan nawa ba amma mama ta kasa gane hakan karfin hali kawai nakeyi Rahama kike ganina a tsayen nan amma nina san abinda nakeji. Naje asibiti har nagaji amma likitoci sai suce dani banda matsalan komai a jikina donshi na fawalawa Allah lamarin a yanzu amma idan ka ganni haka sai ki dauka mai lafiyaneni a tsaye. Har lokacin na kasa magana sai wayan da nake latsawa ina neman lamban Dage daya fado min a rai lokaci guda nayi sa,a ya daga na fara magana a cikin yaren mu dashi. Da farko fada muka soma yana fadin naje birnin zaria na mamta dashi cikin wahala bai dauka rashin mutuncina yakai haka ba ai ? Ace har aure hardo ya daura min amma ban nemesa ba ga baffa yanzu ba lafiya ke gareshi ba shima dai a tsaye yake dai. Nan dai na bashi hakkuri na nuna mashi nima bansan da zancen auren ba yadda yaji haka najishi ban sani ba shine ma yanzu na kirashi akan mijin nawa ai don baida lafiya a jikinshi. Yace Jam jam Anini kada ki auri gawan fari fa nace ba akai can ba yayana Dage tunda ina da Allah dasu ai hakan ba zai faru ba in sha Allahu. Sai ya dirka min zagi yana fadin ohho yar damcen uwa taga kudi taga wajen ci ku kadai kecin kudin ku sai mahaifiyar ku da yan uwanku duk da nasan ba karya ya fada ba amma nace wani kudi dage in akwaisu ai kasan tare dakai zamuci. Ni dai yanzu kiranka nayi daka taimaka min ko da wani abu da zaka bamu ko nawane zamu turo maka dashi yanzun nan yace koda Fam dari nace Anini ? Wucema hakan ai Dage kai din ai dan uwanane banda wanda ya wuceka dage donshinema na nemaka yanzu ai ? To ki kwantar da hankalinki ina kuna da dawakai a garin ku nace kwarai kuwa ba za a rasasu ba in sha Allahu tunda akwai sarakai a garin . Dadina dake akwai kiran Allah to ku nemo ruwan da doki yasha ya rage sai ki kirani zan fada maki yadda zakuyi dashi godiya sosai nayi mai nace ga fam darin ka da kace din zan turo mashi hardana goro dubu goma na tura mai a layinshi take a wajen . Don nasan komai zaiyi zaiji karfin gwiwan bani har abinda baiyi niya ba saboda kudin donshi ne banji komai ba na tura mashi kudin haka. Na dago kai ni ya J ya zubawa ido kafin naji yace dawa kike wayane haka na lumshe ido nace Dage ne dan wajen baffan mu wanda ya taba ban maganin dana baka kwanaki. Sai naga yayi murmushi ya gyara kwanciya kanshi na saman cinyana har lokacin yace ai matsalan nawane Rahama yana da daure kai. Idan mutum baiyi hankali ba sai yayi shirka gara ka dogara da Allah duk abinda ubangiji yayi ga bawa daidaine dashi Rahama. Amma kinki duk inda naje sai ace matsalata na gidane kuma mamace kadai mafitan matsalan nawa amma ta kasa kwantar da hankali ta gane hakan. Wanan yasa kikaga zuwan ilimi a yanzu ba karamin amfanan al,umma yayi ba sosai a yanzu don malumanmu suna kokari wajen wayar da kan mutane sosai a yanzu na su daina irin shirkan da akeyi a da can baya a cikin duhun kai. Don gashi abin baibi kowa a cikin muba saini yake bibiya haka kuma mun kasa tsayawa mu fahintar da mama inda matsalan namu yake . Hardo ya fada min komai lokacin danaje zancen auren ki mutum dayane zai iya shawo kan mama a yanzu itace iya. Don da zan zauna in fadawa iya abinda ke nan daga kawu har mama din zata zaunan dasu ta bincika maganan . Katseshi nayi da fadin wanan mai saukine ai yaya idan har baka iya zama da iya kafada mata a can gida sai mu daukota nan ta kwana biyu daga hakan sai ka samu daman fahintar da ita komai dake damun ka din. Shiru naga yayi na dan lokaci kafin yace hakane gaskiya don zance ne dake son natsuwa da fahinta nakanyi tunanen zancen hardo da yake fadin duk matsalan yana ga kawun mu dauda. Kawu dauda kuma na fada cikin mamaki ina kallonsa yace hakane kawu yasan komai amma yake boye hakan don wani nufinsa akan mu da bamu san na meye ba ? Munyi magana sosai a lokacin inda na fahinci yana cikin damuwa akan matsalan lafiyanshi dana iyali dana sauran yan uwa dake cinsa a zuciyarshi. Nake fada mai dage yace ya nemo ruwan da ake ba doki wanda yasha ya rage idan an samu mukirashi zai fada muna yadda zakayi dashi. Naji yace sai yanzu na yarda ba banza fulani suke zaune a dokan daji ba ashe da shirinsu suka zabi zaman dajin da sukeyi ana masu kallon basu san me sukeyi ba ? Waya fadama basu san komai ba su suna ganin ku dake cikin gari a zaune kune suka kwara ai yace naga alama ai. Wani abokin mahaifin mu bafulatanin nan dajin zaria ne kwanaki da nazo har wajensa muke da yan uwana yake fadin nayi dace tunda na auro bafulatana a gidana. Murmushi nayi nace baka sanin hakan ai shi daya san irin wahalan da bafulatani yakeyi kafin ya mallaki mace ai dole ya fadi hakan. Kiran sallah da aka fara a wayanshi yasa ya mike ya shiga yin alwala yayin da nake zaune a wajen ina charting da anty salma. Har ya fito ya sameni a zaunea inda ya barni yake fadin amma kinji lokacin sallah yayi nace yanzu zan tashi ban fada mai ina fashin sallah ba kai tsaye. Kodaya fita munci gaba da hiran mune da ita har ya dawo ya kara samuna wajen zai dauka na dawone na zaune a wajen kuma. Tun bai zauna ba dana gaidashi nake fadin a binci na saman dinning na hada yace ok barin gama waya da Meabei tana kirana ina masjid dazun ban daga kiran nata ba lokacin. Na saba jin wayarsu don haka na mike na shiga kitchen na dauraye yan kayan da mukayi amfani dasu da rana koda na fito wanan karon yana waya da matarsa Saiba. Naji yana fadin ok sai gobe idan nashigo zamu gaisa a raina nace miji da mata ke nan sai Allah dama idan kace zaka shiga tsakani kai za a bari a cikin zancen. Da mama ta sani tasa masu ido ba zata san lokacin da suka shirya ba a tsakaninsu dazun nan yagama min korafi kanta yanzu gashi suna waya kamar ba komai a tsakaninsu. Tsawan daya daka mata yana fadin nace maki ba zan shigo ba sai safe ko bakiji mena fada bane ban dai tsaya jin abinda ta fada a bangarenta ba na nufi wajen abinci na zauna ina jiransa don ko abincin kwana biyun nan ya rage zama yaci soai don haka nayi hikimar yin wanan dabaran don nasan dole ya taso yadan tsankwara koda kadan ne. Naji yana waya da yan gusau suna fada mai washegari zasu taso yayi masu ban gajiya lokacin ya mike ya sameni mukaci abincin a tare. Bayan ya gama na mike na hada kwanonin zuwa kitchen don ya shiga dakilan wayarshinema lokacin hakan ya ban daman tsayawa in wanke kayan na kife ina gyara wajen najishi a baya. Ya rike min kwankwaso yana fadin sarkin aiki ke baki gajiya da aikine wai ko yaushe kina sa kanki busy na kula ko yaran nan ke ke faman dawainiya dasu a gidan nan idan ban nan ko ? Nace a,a nida su duka munayi bani kadai suke bari da aiki ba ai ga kuma habiba tana taimaka min sosai itama. Tsoman hannuna ya karba yana fadin gashi bata dawo ba nace ta kira da wayar yayanta dazun wai kumshine basu fara da wuri ba nace tabari sai gobe ta dawo ba matsala. Jana yayi muka koma falo bayan na rufo kitchen din muna zama kuma ya shiga waya hakan ya ban daman samu na sulale zuwa daki don lokacin a tsawale nake jin kaina wanka nayi na shirya sosai na lakace jikina ko ina da humran mama na maiduguri a jikina. Yana falo kishigide yana waya a cikin natsuwa idonsa yana kaina harna karaso ina fadi a hankali na kawoma ruwan shayine yanzu ? Kai ya gurgizamin yace ki bar shayin nan a koshe nake yau Rahamce ashe da yaya Habu yake waya na dai ga yayi murmushi yana miko min wayan na karba. Naji muryanshi yana fadin Rahama kina son J yafini kiba ke nan kike faman dura mai abinci haka ? Murmushi nayi don ban iya wasa haka dashi ba da yake jana dashi a yanzu tunda na zamo matar dan uwanshi din. Munkai wani dan lokaci a falo kafin mu koma daki da sai lokacin ya gane fashin sallah da nakeyi tunda ya fahinci hakan naga mood dinsa ya canza . Ya lafe yai shiru sai can naji yana ajiyan zuciya yace na dauka cikine dake ai Rahama da sauri na jiyo ina fadin ciki kuma yaya ? Kamar ba zai ban amsa ba sai kuma can yace baki son haihuwa yanzu ke nan nayi kasa da kaina ina fadin ba wai banso bane yaya in Allah ya ban ina so mana . To Allah ya bamu ni ina son haihuwa sosai wallahi ina son ganin kema kin samu rabonki dani tun ina raye da raina. Yaya kana kashe min jiki idan kana wanan maganan dazun ka fada yanzu kuma kana fadan hakan sai naji yace ana son bawa ya dinga tuna duniya ba matabbata bace a gurinsa ai. A raina nace lalai akwai abindake damun mutumin nan abin kuma babbane daga Allah saishi saiko kila yaya habu suka san komeye matsalan don bai fada min ba. Haka na kwana da damu akanshi washegari zuwan su Salima yasa na dan sake shi kuma ya fita ya barmu a gidan bai dawo ba ashe yana can gidan da yan uwan saiba suna fafatawa dashi kanta. Da yamma kuma yan gusau suka dawo zuwan Ibrahim daya dawo da mota yasa muka fahinci hakan sai gashi shima ya dawo suka zauna tare sukaci abuncin rana dana aje mashi. Aiki mukayi sosai har dare ba hutawa duk