← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 306

Sashe 118

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gaji da yawa. A raina nace ka daizo hanawa rayuwata shakat malam banki ba din na mike na yafo gyale a kafadata muka fito falon a tare dashi. Salimace a falon tana jera kayan breakfast din data shigo dana karshe jin motsin nu ta juyo tare ta ganmu munfito daga dakin ta fara gaida yayab nata kafin ta juyo kai muka gaisa a yar kunya da ita. Ina Nafiss ya tambaya take fadin tana kitchen ku zo ku karya zamuje gida dani dake mu dubo su mama ba zamu jima ba so Nafiss ta jiramu mu dawo. A gurguje naga ya karya da ruwan shayi sai dsnkali da kwai ds suka soya shi naga ya tutura ya juyo yana fadin ina salima din ta fito mu tafi kada mu kara, Barin lekasu indawo don Allah ya juyo yana fadan haka gareni a cikin kullawa nayi masa Allah ya tsare ya kare ya amsa da amin ya fita. A waje ta sameshi har ya shiga mota saboda kawu da yaya Habu yayo masa da text yazo ya gashi a falonsu mama suna magana daya shiga gaisheta. Koda suka kama hanya da salima ya kalleta yace salima kunsha fama ban nan ashe abinda kawu ke kulla min ke nan jiya ban fito da maganan bane don Nafisa dake zaune. Ai kawu gaskiya mugun mutum ne yaya makin ya taushe mama ya bata hakkuri wai amma shi da matarshi sune suke zuga mama a kanka ni shine ya bani haushi wallahi. Yadda kake kokari dasu din nan amma suka iya haka basu nuna mata gaskiya ba wai ace mama ta zauna tana shirin ci maka mutumci akan inda zaka aje matarka ? Me Rahama tayiwa mama don Allah tunda ba itace ta tillasta maka dole ka aureta ba kai kayi ra,ayin haka kuma iyayyenka suka bata duk fa yaya Habu ya fada mata komai amma mama ta yarda ta dauki zugi a kanta game dakai. Bakomai salima dukiyane yau zan mayar ma kowa da abinsa inyaso suyi abinda suke gurin yi dashi nadai godewa Allah da ban taba dukiyan nan ba. Yanzu yaya mayar masu zakayi wallahi yadda naga su kawu sun damu kamar suna da wani manufane akan kudin nan in bashi ba meue nasa a ciki don Allah ? Maigadi na bude masu get kawu din suka fara hangowa tsaye kofan part din Iya yana waya ya zubawa motansu ido har suka karaso. Da farko bai sheda waye ba saida J din ya bude motar ya fito tare da salima ya gane shine lokacin kuma waya yakeyi game da J din yana tambayan lamban a wajen abokin J din daya sani. A,a Jafar dama kana kusa ashe to sannu da zuwa ashe kana hanya dama ? Eh kawu ya fada yana hawo step din da zai sadashi da kofan iya bai tsaya ya gaidashi yadda ya saba bakawai yasa kai ya shiga wajen iya da sallaman shi. A,a a lale marhabin dan halas kaki ambato ashe ana nan ana faman cigiyan ka kamar wanda ya bata sai gaka kwatsam ka fado ? Ashe dama kana kusa ba nisa kaje ba to sannu da zuwa yaya hanya iyace ke wanan magana tana taba hannayenta daga inda take zaune. Iya wake cigiyata haka kedai ko don kada amarya ta daukeni ya fada yana zama gefenta sai wani annuri yakeyi da ganinsa kasan abubuwa sun zauna ana cikin lokaci. Iya tace ba dole ba Jafaru tunda ance ka gudu ba a san inda kashiga ba anyi kiran wayanka baya shiga kowa ya kira baya samun ka ka dauki dukiyan mutane ka salwantar ka kama gabanka ka bace wa mutane. Iya wani dukiya na salwantar tace to danga dukiyan magada dake hannunka mana masushi suna bukatan abinsu yanzu tunda ance sune kake,,,,,,, Haba iya wacce ya gudu da dukiya nai cikin mu waga dabi,a batayi ba iya mi da zaki hwada mai haka don Allah ? Anty barka dake fitowa daga dakice ta tare iya dake fadin zancen da dan fada fada iya tace yanzu kuma zakuce baku fadi hakan bane a gabansa ? Nan fa kuke keda yar nan saratu kuna fadin magana tundai saratun nan bakinta baya fadan alheri game da kowa saidai sheri. Anty Baraka ashe kinzone ya fada yana kallon anty baraka din da ta bata rai don abinda iya ta fada a gabanshi yaiwa kowansu zafi. Nazo tun karshen satin can jafaru an dawo lafiya ya hanya wai tace ance ka gudu to wayace banda abin iya da shirme baki san me ake fada ba kije gulma ? Murmushi yayi yana fadin da hankalinta ba shirme bane iya bata son wani ya sokeni kila inke baki fada ba taji wani ya fadi hakan ta rike a ranta. Inke baki fada ba ai uwarku sun fada ko zaki toge yanzu don kun gasa ya dawo a yadda baku zata ba ,,,,,,,, Iya koma me aka fada aishi yaja a fada mai hakan don babu yadda za ayi dukiyan mutane yana hannunka ka zauna baka kara maishi sai kanka kana ta faman auren daba riba don me ba za ayi magana ba ? Mama dake fitowa daki take fadin hakan ta murde fuska ga dan nata a karo na farko haka ya tabbatar mashi cewa kome akace mama din ta fada akanshi lokacin zata iya fada. Mama na gudu kuma ban kara kowa ba kamar yaya nabar kowa ban kula dashi ba mama wallahi banjin cewa a duk garin nan kaf akwai wanda ya fini kula da yan uwana da iyayyena ko banzo na daya ba ba zan wuce na biyu zuwa ukku ba in sha Allahu. Aure kuma da nayi ra,ayinane mama bana wani ba ban dauki kudin kowa na auro Rahama ko saiba ko Asmau ba ni na nemi kudina na auro matana dashi mama. Haka kuma lalurar da nake masu da kowa da abinda Allah ya hore min nakewa kowa tasa laluran dashi bada dukiyan wani ba. Fada masu dai Jafaru don kona fada ba yarda da hakan zasuyi ba tunda shedan ya rufe masu idanu akan dukiya suna son su tozartaka a yanzu don kawai abinda bai shafesu ba kanka. Haba dai Iya zancen nan dai nace na ari bakin kowa nace nina fadi hakan ko to abarshi mana a haka idan zaiga laifin wani yaga nawa ni kadai ? A lokacin hankalinsa yana ga waya da yake neman lamba a ciki ya danna kira aka dauka yake fadin kai Nura fadawa Salis kuzo min da sakon nan ganinan gida part din iya zaune. Meshi ya tsaya fadin kadawone ashe yace na dawo tun jiya ya kashe wayan yana dagowa yace mama ita anty baraka tace ban kulata ko habu ko yazid ko yaran nan su saratu ? Ya akeso mama anty baraka gaki dai har account naje nasaki gaba don in zan maki sako ina shan wahala naje garinku na dukeki muka bude maki account da nake tura maki kudi duk wata. Koda banda lafiyan nan ina kwance haka nake tura maki kudi ko yaushe daidai abinda Allah ya hore min shi kuma yazid dake sudan a kirashi a tambayeshi nawa nake tura mai ko wani wata. Balle yanzu da yake shirin dawowa gida din nan gaba daya yaran nan kuma a cikin su waye ban tare masa lalurashi mama ? Har wajensu kawu su fada idan akwai wano wanda ban dauke wa wani matsalan gabanshi ba don Allah shi habu wanan tsakanina dashine ba sai na fada ba nayiwa banza balle habu nawa ? Kai Jafaru anji kayi hakan wanan ai ina zumunci kayiwa ko yanzu zancen hakinsu akeyi ka,,,,,,,, Sallaman su Nura da suka zo da jakkar bako niki niki suke shigowane ya katse mata zancen data soma tana binsu da kallo suka shiga gaidasu suka zauna yace ku girka a gaban kowa a gani nawane a ciki. Habu ya shigo fuska daure yace Habu ka zauna a kirga kudin nan bari na leka su Asmau indawo acigaba in dauko wasu takardu a can ya mike ya fita a cikon kamshin turarebshi daya gauraye part din dashi. Jin fitan shi daya bayan daya suke fitowa daga dakin kowa ya samu waje ya zauna su Nura din suka shiga kirgan kudin hannunsu din tare da Habu dake lissafa masu suna hadawa a waje daya. Part din nasa shiru kamar ba kowa a cikinsa har ya shiga dakinsa ya dauko wani file ya fito dakin Asmau ya shiga tana kwance kasa saman tieles tana barci ya dan bugeta ta farka ta bude ido tana fadin ka dawo ashe ? Yace eeh ya gida lafiya kalau ta fada tana mikewa zaune yace ina zuwa yasa kai ya fita zuwa na Saiba daya sama kwance tana waya. Ta jiyo ta kalleshi taci gaba da wayanta ya dan tsaya cike da takaici ya kuma juya zuwa waje ba tare da yayi mata maganan komai ba a lokacin. Yasan idan yace zai tsaya mata magana a yadda yaga tayi din nan ransane zaifi haka baci haka yasa kai ya fice ya gama da wanan issue din dake gabanshi kafin ya dawo nata a yanzu. Kodaya koma an gama lissafa kudin kawu yana zaune sai faman gyaran zama da yakeyi yana harde kafa a waje daya ya shigo yana fadin ya kun kammala ko ? Habune ya bashi amsa da fadin an kammala J miliyan ashirin da takwasne da dubu dari biyar da hamsin da tara gasu. Yace good Nura wanan milliyan bakwai kenan dana baka ko yace ehh maigida Nura jirashi a waje salis kai ina wanda na baka milliyan biyar ka juya din ya nuna mai yace gasu yanzu sun kai miliyan ashirin da daya da da dubu dari biyu ga yadda muka lissafa su. Good Nura ina son ku zamo cikin sheduna tun a nan duniya don don Allah tunda na baku kudin nan a juya na taba karban kwandala a hannun ku ? Haba maigida wallahi banda lissafi da in kazo mukeyi dakai na riban da aka samu a shekara ka debewa shago da namu hakkin ka bamu nikan kam kwandala baka taba karba a hannuna ba. Shima salis ya fadi to na gode idan na fito zan nemeku a san yadda za a dawo da harkan ba
Chapter 118 · 0% Book details