Sashe 233
Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya kasance mun shigo falon a tare da daddy muka gaisa nan mama ta soma fadin haba diyata don me zakiyi min haka duk hakkurin da nake baki ? Dukar da kai nayi kasa a cikin jin nauyinta ina wasa da yatsuna ta cigaba da fadin kin kamo hanya kibar min dana a cikin tashin hankali jiya ? Gaba daya jiya sam bamu gane kansa a gidan nan don ya rikice muna ciwo yana kokarin ya dawo saba a jiyan Allah dai ya gyara. Alh ayi hakkuri a bamu yar mu mu yafi da ita don Allah ko zamu samu ya kara kwantar da hankalinsa don in ba komawa tayi ya ganta ba gaskiya yana iya samun matsala. Murmushi daddy yayi ya gyara zama yana fadin ai hjy banki ta takiba don babu iyayyen dake son yarsu ta taso daga gidan aurenta ai gata nan zaune idan tace zata biku din wa,lillahi hamdu udan kuma tace a,a to ba dole don ni banwa yaro dole akan rayuwansa. A,a Alh kada kace haka adaiyi hakkuri shima ya tareta da fadin yes iya gaskiyata na fada don yarana kaf banwa kowansu dole akan matsalan aurensu. Don bani ke zama dasu ba a can amma ba inda za ace asa ido yarinyat dako auren farko batayi ba tana kokarin sheganta jinin dan uwanta amma ba a dauki wani kwakwaran mataki a kanta ba. Inaga idan dan yazo duniya sai abinda taso zatayi mai na wullakanci ke nan don tun jiya datazo da zancen nan da ace nine na haifeta da wanan yar ta kwana a cell . Taje can ta koyi ladabi da kama baki na kwana biyu kafin a sakota saidai za ace don banina haifi Rahama ba a yanzu idan nayi hakan. Alh dan yaune kanayi kamar bakayi in bashi ina wanan zancen zai fito haka a bakin yaro adaiyi hakkuri don Allah an tsawata mata ai. Nan Habu ya tsoma baki yana fadin daddy yarinyar kamar wata mai motsi a kai don tsaban iskancin da takeyiwa matan mu saida na taka mata burki a gidana. To kagani kai kayi mata iyaka da naka gidan gidan dan uwanka ke nan ta koma ashe gaskiya zancen yayi muni ace a bakin yara ya fito bako manya ba ban taba gani ko jin yadda dan uwa zai batawa dan uwansa jininsa haka tun baizo duniya ba ? Yarinyar banzace daddy ayi hakkuri don Allah hakan ba zai sake faruwa ba da yardan Allah kwanan nan duk aure za ai masu su kama gabansu. Kaiya ko kun masu aure ai suna tare daku kun taba ganin inda wuya yabar kai sai gangan jiki kawai ? Yanzu ga yarinyar nan ai a kusa muji ta bakinta na fada maku tun farko ba zan mata dole bani don bani shiga hakkin mutum a rayuwata. Kafin ya rufe baki na amsa da daddy ni gaskiya ba zan koma ba su aiko min da takardana kawai in huta ina fada a cikin kuka sai salati mama da iya sukeyi . Mama na fadin yar nan da bakinki kike fadan haka a gaban mu me mijinki yai maki da zaki yanke danyen hukunci haka tsakanin ku ? Iya take fadan hakan kuka sosai nasa ina fadin iya niba zan koma ba inda ba a kaunata ba kuma ba mai daukan min mataki ga hakan saidai aga laifina idan na dauka ni gaskiya ban komawa gidan nan kuka sosai nakeyi a lokacin. Haba yar nan kiyi hakkuri zancen nan ya mutu a nan ki shirya mu koma gida amma zancen ba zaki koma ba ai bai taso ba mama ta fada. Mama nagajine nagaji nina san abinda ake min kan ya jafar ina hadewa gara kawai in bar gidan zaifi ni dai bani bace na dafewa yaya saina aureshi shi yaje yasa iyayyena suka aura min shi bada sanina ba kuma nayi hakkuri na zauna dashi duk da irin barazanan da nake gani a gidan wallahi ba zan koma ba. Cikin bacin rai don ya nuna min shi wanine a gareni lokacin ya mike tsaye yana fadin Iya ku tashi muje tunda hakane don taji ance ba zata koma ba udan bata so zata tsaya tana muna wanan shakiyancin haka ? Habu ke fadan hakan cikin bacin rai ya mike yana fadin su tashi suje nan dan uwan yace a,a bros ba za ai hakaba dole mu lalashe ta tunda laifi akai mata. Me kake son muyi yanzu tunda an fada mata matakin da za a dauka kan abin tace ba haka ba ba saita zauna gidan ba ban taba mashi rashin kunya ba sai a ranan . Nima a hasale nace dashi a barini mana sai me idan na zauna gidan ai yafi min sauki da zama inda ba asan darajata ba sai wajen amfani . Ko an barni aiba mutuwa zanyi ba hakan ma tafi min dadi da zama inda a kullum laifina ake nema a gorantawa iyayyena don ana daukan mu marasa gata. Rahama ni kike fadaqa wanan maganan yau haka ya fada yana kallona da sauri mama tace kai habu gyara mukazo yi ba barnawa ba don haka kabi abin nan sannu don Allah. Nima shina gani tunda har yarinyar nan tayi haka an dade ana cusguna mata tana hakkuri yanzune take ganin tagaji koma waye gaskiya haka zaiyi. Baiyi magana ba har matanshi shiru tayi shiko ya juya ya fice falon yana fadin ummah nina tafi ke nan sai anjiman ku ya fita. Daddy yayi murmushi yana fadin ga alama nan ya nuna kanshi ko a yanzu yarinyar nan an tabata a rarasheta amma yana son ai mata dole ta koma ? Ba dole yayi min hakana ba tunda kansu hade yake da dan uwanshi amma aishi da aka tasa matarshi gaba ya dauketa yabar gidan a lokacin duk da ban gidan ban huta ba tunda har inda nake ake biyoni aci min mutunci akan gaskiyana. Dashi da jafar din waya taba daukan mataki udan ba iya ke kusa ta tare min ba bagaji wallahi ni ba zan iya ba gaskiya na fada na mike zuwa ciki ina kuka . Ajiyan zuciya ya daddy ya sauke yana fadin wanan abin dole a tsaya a natsu abawa yarinyar nan lokaci don Allah harta sauko don na fahinci ranta abace yake yanzu. Idan munce zamu mayar da ita da karfi da yaji abin ba zaiyi dadi ba gara dai a bari ta dan huce zaifi sauki saita koma din. Abinda nakewa gudu ke nan nasha fadawa dubu hakan tana ganin bai zama komai ko kuma ta dauka ai basu da gatan irin haka yau gashi dai din ya faru ai. Amma na dauka akan Saaratune da abokan zamanta matsalan ai yazid ya fada yana kallon iya iya din tace ai kaji metace ko yanzu kokai matanka ai don suna ciki kullene ko yaushe basu kwasa da ita. Bar dubu inda ka ganta akan yaran nan da kawun ku hardai ace maka sun hade da shedanin nan guda dauda to ka barsu kawai na gayama . Ni yanzu aiba mu koma babu yarinyar nan bace yaron nan Jafar ya rikece muna yadda yayi jiya ni shine tashin hankalina a yanzu. A to mama tunda ance a barta ai dole mu barta din har ta huce yaya zaiyi kuwa banda hakkuri tunda ba tare aka haifesu ba dama ? Yasan yana sonta haka yarinya tana kokari dakai baka iya kareta ga kowa anatayi mata cin fuska yana kallo bai dauki mataki ba da nine gobe wata ba zata kara ba ai idan anga irin matakin dana dauka. Yaren fulancin da mariya tayi tana mikewa tsaye shine yasa suka bita da kallo itama ummah yaren tayi mata tana bata amsa don fadi take wai akan me zanyi haka tunda an biyoni bari ta ganni. Shine ummah din tace gaskiya itama bata son a barni in koma kawai kowa ai hakkuri yakeyi a gidansa shine ta nufi dakin wajena. A kwance ta sameni na kifa cikina ina hawaye tashigo ta tsaya a kaina tana fadin yanzu ke kinga haka yafi maki kizo ki zauna nan ? A fusace na dago na tareta da fadin ai dole kice haka tunda bake bace akewa abinda akemin a gidan koda yake ke naga hakan bai dameki ba ai dama toni ban daukan hakan . Kiri,kiri mama ta nuna bata son zaman mu da diyanta abinda take muna idan ayiwa diyanta zata dauki hakan ta kyalene ? Ko gaida matar nan nayi duk zuwan da nakeyi gidan nan bata amsa min sai taga dama duk abinda sararu tayi min da sanin mama . Tunda sunce ni ba alheri bane ga yaya Jafar sanadina abubuwa da dama suka sameshi na barshi don abubuwan su wuce din garesu tuda nice matsalansu. Ashe in kina bin zancensu ba zaki zauna da mijinki lafiya ba kuwa don su ko ajikinsu kuma kina gani tun baki aureshi ba ai yadda sukeyi damu a gidan . Ku kikace Yanda ni baku nane ai don ban iya daukan hakan nagaji wallahi amma baki mashi adalci ba Rahama udan kinyiwa yaya haka ? Naji ke kije kiyi mashi adalcin bashike nan ba ta tare da fadin akankifa ya saki Nusaiba jin hakan data fada yasa na dago na tsareta da idanu ina fadin. Aikanafa kikace Maria kaina ya rabu da matarshi tace akankine mana nace akanshi dai idan baki san abinda yasa yakai ga sakinta ba nina sani kuma ban fadawa kowa ba duk da fadin da akeyi kainane ya saketa din dama yana da niyar hakan. Ki dai tashi muje kawai kinga har habu yayi fushi dake yau na sake jefa mata kallo a cikin mamaki tare da mikewa zaune nace habu ubanane ko yayana maria ? Shigowan ummah dakin ya hanani cigaba da maganan tashigo tana fadin habu ba ubanki bane amma kamar uba yake gareki ai don shine gatanku acan din. Kememe na kafe duk abinda suka fada ban yarda na bisu ba mama tashigo muyi sallama da ita a cikin dabara nan take fada min kin mun daidai Rahama dabaki yarda kin koma ba a yanzu sai dubu ta kawo kanta gidan nan da kafanta. Lokacin zata gane kina da ma,ana a wajensu idan ba haka ba bata da