← Book details Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 231 OF 306

Sashe 231

Murfin Jallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

hannuna ta koma fadin kai gaskiya mijinku dai yaji jiki wallahi wasa wasa fa yakai shekara da rabi yanzu ai nace za a kai gaskiya ciwon ya dade a jikinsane . Tace balle abu ya kasance na jifa ai sai yawancin rai irin hakan son ma dai suna tsayene suma ba a samu yadda ake so ba dashi. Hamma na soma yi hakan yasa take fadin tashi kije ki kwanta ki samu hutu yar nan nima bari na kwashe kayan nan zuwa kitchen hakan ya rabamu da ita ranan na fahinci tana da son surutu gaskiya. Washegari kodana tashi nayi sallah na koma na kwanta abinda ban sababa nayi barcin safe mafarkin da nayine ma ya tayat dani misalin tara da rabi na safe sai nake ganin ai rana yayi sosai lokacin. Mikewa nayi zuwa bandaki ban fito ba saida nayi wanka na tsabatace jikina nafito na shirya zuwa falo ina neman abin karyawa. A falon na samu ummah zaune tana karyawa itama tana waya tun kan na karaso na fahinci wayar dai a kainane har lokacin gaida ita nayi da kwana ta amsa tana fadin. Yanzu nake zancen na tayar dake ashe ki dade da falkawa ga abin karyawa nan ki zauna kici ta fada tana nuna min abincin a bakin table nakai zaune kamar zan bude sai kuma nace daddy fa ya fitane ? A,a manjo ai bai fita ko ina shi indai baya kama ba ko ina bai zuwa shi ko yaushe yana gidan nan dan dama da yamma yana zama ta wajen gidan nan da mutanen unguwa. Balle yau da yasan yana da baki koda fitan ya kamashi ai bai zuwa ko ina sai sunzo sun wuce ban tambaya suwaye bakin ba tunda ba abinda ya shafeni bane. Sai misalin karfe sha biyun rana saiga sallaman mama da iya tare da yazid maria da habu suna bayansu suka shigo gabana ya fadi daki na tashi na koma da sauri don a falo nake kwance ina kallo abinda na dade banyi ba ke nan a rayuwata. Ummah ta kunna min wai in rage rana a nan din tunda ni kadaine bata san hakan baya damuna ba don na saba ko a gidana wani lokacin ni kadai ke zama ai. Sun shigo naji ana gaisawa dasu suna tambayan ina inane tace ina ciki maria ta mike zuwa uwar dakin ta sameni ko kallonta banyi ba a wajen . Take fadin yanzu ke haka yayi maki ai gashi saratu taji dadin hakan can yazid ya kamata tana waya tana fadawa Nusaiba yai mata dan kareb duka jiya ya hade mata haushi biyun ta da yake ji. Dama nayine taji dadin ai abinda bakina ya fada ke nan nace kinga saita dawo da nusaiba din tazo tayi ta haifa masu yayan halas a gidan. Ki bar wanan zancen don Allah jiya aita kwammace da bata fada ba din don yadda akai mata dukka yan uwa kuma sunce wata daya suka bata ta fito da mijin ko suyi sadaka sa ita. Ke jiyafa da yaya J ya mutu wallahi don faduwa yayi harda jin ciwo wai abarshi ya biyo ki ko yanzu ma dakyat aka samu ya zauna don mama tayi mai alkawarin dawowa dake yau din. Cab aiko tayi kaffara don wallahi ba inda zani barin fada maki wanan gidan har shi sun fita raina wallahi suyi da wata kuma badai Rahama ba kuma ? Wasa dai kikeyi kina son bawan Allah nan ya shudene Rahama baki ganshi bafa mama tayi fada duk da bata so laifin Saratu amma tun jiya take kan zaginta gidan nan akace. Su wanan ya shafa ko ince ku amma ni na fada maki ba zan koma ba gaskiya nagaji wallahi neman sanadin abinda zai zubar da cikin nan nasa nakeyi yanzu a jikina na daina tuna komai nasa ga baki daya. Wai kanki daya kuwa Rahama kodai kema din Nusaiban ta hada da kene wajen mallaka ta yamutsa maki hankali baki komawa kamar yaya ? Nusaiba fa kikace Yanda in an fada maki nusaiba zata iya min wani abu ya kamani a duniyan nan baki mussawa ko kin manta dani yar baffa ne ? Saidai ta Allah bata mutum ba kin sani amma mutum ya gwada idan yana ganin haka sai kace ba diyar fulanin asali nake ba muryan ummah ne dake kirana tana fada akan banji zuwansu bane naki fitowa mu gaisa dasu. A daidai lokacin kuma mijinta ya shigo falon suke gaisawa dashi na fito na gaidasu duk sun kura min ido suna bina da kallo ?
Chapter 231 · 0% Book details